• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, November 3, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ciroma: Yadda wani amini na ya so kashe mani aure da Wasila

by DAGA ABBA MUHAMMAD
October 7, 2020
in Ranar Murna
0
Wasila Isma'il tare da Al-Amin Ciroma

Wasila Isma'il tare da Al-Amin Ciroma

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MALAM Al-Amin Ciroma sanannen ɗan jarida ne wanda ya taɓa zama Editan jaridar ‘Leadership Hausa’. Yanzu kuma shi ne Manajan gidan talbijin na Farin Wata. 
 
Bayan haka, fitaccen darakta ne kuma jarumi a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood. Za a iya cewa kusan tare da shi aka yanke wa masana’antar cibiya. To kuma sai kaya ya tsinke a gindin kaba, ya auri fitacciyar jaruma Wasila Isma’il, wadda ta shahara a matsayin jarumar fim ɗin ‘Wasila’ na furodusa Yakubu Lere.
 
Auren ya yi albarka, domin kuwa an samu yabanyar ‘ya’ya, sannan an yi haƙurin zama da juna a tsawon lokaci. A ranar 6 ga Oktoba, 2020 auren nasu ya cika shekara 18 cur. Hakan babbar nasara ce ba kawai ga Al-Amin da Wasila ba, har ma ga Kannywood baki ɗaya, domin sun fatattaki iƙirarin da wasu ke yi na cewar wai auren ‘yan fim ba ya yin ƙarko. Wasila da Al-Amin na daga cikin ‘yan Kannywood da za a ce auren ‘yar fim da ɗan fim ya daɗe, wato irin su Shu’aibu Lilisco da Zulai Ɗalhat da kuma Sani Musa Danja da Mansurah Isah.
 
Shin menene sirrin wannan daɗewa tasu? Waɗanne irin ƙalubale aka fuskanta daga 2002 zuwa yau? Kuma shin da gaske ne Ciroma ya so ya auri jaruma Halima Atete? A wannan hirar ta musamman da ya yi da mujallar Fim, daraktan kuma jarumin ya feɗe mana biri har bindin sa, kuma ya karantar da mu wasu muhimman darussa game da aure da zamantakewa. Ku karanta ku ji.
 
 
FIM: Da farko, me za ka ce game da wannan rana ta cikar ku shekaru 18 da aure da maiɗakin ka Wasila Isma’il?
 
AL-AMIN CIROMA: Abu ne mai wahala, mai kuma sauƙi. Ni shekaranjiya ne ma ta ke tuna mani, ta ce ‘anniversary’ ɗin mu. Na ce mata shekara nawa? Ta ce sha takwas. Na ɗauka wasa ta ke yi, saboda ni a tunani na kamar jiya-jiya aka yi wannan abu, sai ga shi ana lissafin shekaru sha takwas! 
 
Ban yi mamaki ba, amma kuma haka da ma rayuwar ta ke. Don haka zaman aure ya fi ƙarfin ka misalta shi. Kamar yadda na rubuta a shafi na na Facebook, aure ya fi ƙarfin soyayya kawai ko kuma a yi ta bayyana soyayya. Aure ya kai ƙololuwar da za ka iya cewa rayuwar ce baki ɗayan ta. Akwai soyayyar, akwai haƙuri, akwai kuma juriya. 
 
A cikin shekaru sha takwas ɗin nan da na zauna da ita, Allah kaɗai ya san aurarraki nawa kan soyayya ɗin da ake magana, amma sai ka ga an watse. Wasu ma har an manta, wasu kuma an yi auren an sake yi; an yi ɗaya, biyu, uku, huɗu, har an gaji an ce an haƙura da auren. 
 
‘Point’ ɗin shi ne shekaru sha takwas ba ƙaramin tafiya ba ne; ya kamata a ce an ba mutum digirin digirgir a kan wannan zaman da ka yi da mace ɗaya, ta yi ‘tolerating’ ɗin ka, ka yi ‘tolerating’ ɗin ta. 
 
Kuma zama da irin mutanen mu, akwai abin da za ka ɗora wa kan ka. ‘Yar fim ce, a zamanin ta ta yi fice, duk da ba fim ta ke yi ba a yanzu, ta na da ƙawaye, ta na da aminai. Ka na ji ka na gani za ka sallama irin hulɗar da za a yi. Wasila ta na hulɗa da mutane, kuma ni na ƙara mata ƙarfin gwiwa, kuma kai a matsayin ka na namiji dole ka tsaya ka kalli yadda ake hulɗa ɗin da ake yi; addinin ka ya ba ka wannan dama, don Allah zai tambaye ka. 
 
A wannan zaman da ake yi na soshiyal midiya, za ta shiga guruf da sauran su, babban abu (shi ne) babu wani abu da ya taɓa zuwa mani na zargi. Ban taɓa tunanin akwai wani abu da za ta yi na daban ba a kan wannan, saboda irin fahimtar juna da aka yi. Wannan, a taƙaice, tafiyar da aka yi na shekara sha takwas kenan.
 
FIM: ‘Ya’yan ku nawa?
 
CIROMA: ‘Ya’yan mu da ita guda huɗu ne. Na farkon ya rasu, Muhammad Albaƙir, sai A’isha wadda na sa wa sunan mahaifiya ta, sai Fatima, sai Jaafar da kuma Ruƙayya.
 
FIM: Waɗanne nasarori da ƙalubale ku ka samu a tsawon shekarun nan da ku ka yi?
 
CIROMA: Gaskiya nasarorin su na da dama, musamman zuri’a da Allah ya ba ka. Wani za ka ga ya na ta ƙoƙari amma Allah bai ba shi ba, wani kuma zai ta bin hanyoyi da dama masu kyau da marasa kyau don neman zuri’a, sai ka ga kuma ba a samu ba. Amma kai sai ka ga ba rawa ka yi wa Allah ba, ga shi ka na da ‘ya’ya kuma Allah ne ya ba ka. Babban abu shi ne ka tashi da yaran ka tare da kai, ka na gadin rayuwar su shi ne babban nasara, ba sai ƙarfin ka ya ƙare ba. 
 
Nasara ta farko, za ka ga ina tare da ‘ya’ya na ana raka rayuwar da ƙarfin ka, ka na nuna masu ga fa abin da ya dace a yi. Allah kaɗai ya san wa zai riga wani a duniya. 
 
Nasara ta biyu kuma, ana cewa ‘yan fim ba su zaman aure, da zarar an yi aure, sai a ce aure ya mutu, kaza-kaza da sauran su. Ga shi dai dukkan mu mu na cikin industiri ɗin, sai ga shi ana ƙirga shekaru. Ni da an ƙyale ni, sai in ce ba a wuce shekara biyar ko shida aka yi ba! Amma ita ba ta manta ranar ba. Har ga Allah, ban iya tuna ranar sai in ta tuna min. Abu ɗaya na ke tunawa, ranar ‘birthday’ ɗi na; nata ma sai da ta yi min ƙorafi sosai sannan na sa shi a kai na. 
 
Don haka masu cewa ‘yan fim ba su zaman aure, ya kamata su canza tunani a kai. Ta yi aure a lokacin da za ta ci gaba da harkar fim. 
 
Sannan kuma ba wai ba a samu matsaloli ba, an samu matsalolin da za ta iya cewa ita ma bari ta fita ta koma fim, amma an tsaya an daure an ci gaba da tafiya har zuwa yanzu.
 
Waɗannan su ne  nasarorin da mu ka samu.
 
FIM: Shi kuma ƙalubale fa?
 
CIROMA: Ƙalubale, kamar yadda na fara faɗa maka a ɗazu, akwai ƙalubale na zamani da mu ke ciki. Za ka ga in ba ka kai zuciya nesa kai kan ka sai ka yi tunanin a’a to na ga wacce da ta ke yin fim ai ta na hulɗa da mata ta, anya ba za ta zuga ta ta yi wani abu ba? To irin wannan za ka yi ta tunani na ƙalubale, amma in ka san da wadda ka ke tare sai ka ji abin ba wani ƙalubale ba ne. 
 
Na biyu, a matayin ka na namiji za ka ga ana jawo hankalin ka a kan an yi kaza, gutsiri-tsoma da sauran su. 
 
Waɗannan abubuwa su na cikin al’ummar mu sosai: a kakkawo maganganu don a ɓata wani, a kawo abin da za a kawo matsala a cikin gidan ka, da sauran su. Irin wannan an ɗan fuskanta ɗaya biyu. Misali, ni da ba zama na ke yi a gari ba, babu abin da ke tada min da hankali (kamar) a ce akwai matsala a gida na, domin in akwai matsala a gida na babu abin da zan iya yi, gaba ɗaya ranar zan zama gani nan dai kawai. Duk da haka mun samar da wani fahimtar kan mu. 
 
Na farko dai yadda ta ke ba ta da wayo sosai, amma da aka tafi sai ta gane. Wani lokacin mu na zaune za ta ce min, “Ka ji wane ya ce min kaza,” har ma a cikin abokai na na jiki sosai, wanda na amince masa ya je ya na ta haddasa min matsala ban sani ba. In kuma ya zo wuri na sai ya ce, “Ai wance ba ta da haƙuri. Menene Wasila ta ke buƙata? Babu abin da ba ka yi mata.” Sai kuma ya koma wurin ta ya ce, “Ai wannan ya na ba ni mamaki, ga abin da ya ke yi, ga abin ya ke yi.” 
 
Mun samu wannan babban ƙalubalen. Da maganar ta fito sai da na ji kunya. Ni fa ba ni na aikata ba, amma na ji kunya. Bayan na ji, na je na same shi na faɗa masa wannan abin da ya yi bai dace ba, amma in ya yi ne don ya haddasa min matsala, ba damuwa. Daga nan sai na ja layi tsakani na da shi. Irin waɗannan abubuwan su ne, Malam Abba. (Dariya).
 
FIM: A baya, ka taɓa yi mata kishiya wadda ku ka rabu. Ko ka na da niyyar ƙara yin wata?
 
CIROMA: Ai kafin ita ma ina da wata. In ka tuna, ba ita ce ta farko a wuri na ba. Ita waccan a ranar da ta fahimci zan ƙara aure matsaloli su ka zo, abu dai ba daɗi, ta ce ba za ta zauna ba, in rasa wadda zan aura sai ‘yar fim ma da ake yi masu kallon ‘yan iska? Sai kuma ta matsa wa kan ta, ta fita a gida na, ba ni na sake ba. Wanda a tsarin rayuwa ta, har ga Allah tun ban san me duniya ta ke ciki ba na ke faɗa wa mahaifiya ta ni mata biyu zan yi. 
Yabanya ta yi kyau: Iyalin Ciroma
Bayan rabuwar mu da waccan, na ci gaba da ita kaɗai. Daga baya na yi yunƙurin  yin auren, amma sai tafiyar ba ta yi ƙarko ba, domin kusan ‘yan kwanaki ne kaɗan da yin auren al’amarin ya lalace, har aka zo aka yi yadda aka yi, aka sauwaƙe wa juna.
 
Shi aure haɓo ne; a matsayi na na namiji lafiyayye, kuma Musulmi, in ya zo alhamdu lillahi! Ina da wannan muradin, amma ya danganta da yanayin da zai iya zuwa. 
 
Kuma a zato na guda biyun nan da na yi, na farko ita ta fita da kan ta, ta ƙarshen kuma na samu matsala. Shi ne abin ya ke ba ni wani irin tunani, wanda idan zan yi yanzu duk tunanin nawa ya sake. Za ka yi tunanin wacce za ka aura a yanzu a zamanin da soshiyal midiya ya yi yawa, a zamanin da in za ka auri mace za ta fara tunanin ta ina za ta kassara ka. Mu na kallon abubuwan da ke faruwa. 
 
Duk waɗannan abubuwa su na yawo a kan mutane, ba ni kaɗai ba. In ka yi hira da mazaje da dama za ka ji; wani ya na so ya yi ɗin, amma in ya tashi wacce zai aura? Kowane lungu ka je akwai Islamiyya, akwai masallatai, akwai malamai na wa’azi, duk wayoyin mu cike su ke da wa’azi, a rediyo ka na jin wa’azi, a mujallu da jaridu ana wa’azi, amma a cikin wannan al’umma ne za ka ga idan zan aure ki za ki fara tunanin mata ta da ke gida za ki raba ni da ita ko kuma ki yi asirin da in na tafi gidan ta ta rinƙa kallo na kamar dodo ko kuma in rinƙa kallon ta kamar dodanniya saboda zafin kishi da sauran su. Wannan yanayi shi ya ke ɗan taka wa mutum birki.
 
Idan kuma ka ce bari ka je ƙauye ka samo wadda ba ta waye ba, in ta zo ai ba da aljanu za ta zauna ba, da mutane za ta zauna. In ta falle kuma ya za ka yi? Ka sake ta? Don haka al’amarin akwai wannan tunanin. 
 
In abin ya zo, kamar mutuwa ne. In kuma ka shirya zuwa ka yi mata albishir, Alhaji Abba, sai ka je ka yi mata wannan albishir ɗin! (Dariya)
 
FIM: A baya an ce ka so ka auri jaruma Halima Atete, wanda abin bai yiwu ba. Wasu na cewa ka yaudare ta ne. Me za ka ce?
 
CIROMA (Dariya): Wallahi wannan dai daga wurin ka na ke ji, Alhaji Abba. Amma dai Halima mun yi mutunci, kuma ana yi har gobe. Ban taɓa sanin wani abu mara daɗi game da ita ba, gaskiya. Kuma har gobe ta na girmama ni sosai. Don ko kiran ta na yi yanzu ma, za ka ji oga ta ke ce min. 
 
Ba zan manta ba a  ɗan baya-bayan nan akwai abin da na gani a midiya a game da ita, wasu sun yi shaguɓe kuma da gangan aka yi da sunan ta, don sunan ɗan fim ya fi yawo. Yanzu da an yi wani abu aka ce Abba Mujallar Fim ne sai a ɗauka a yayata, duk irin wannan. Da na gani, na kira ta na ce, “Kin ga wannan abin?” Ta ce, “Wallahi oga ban gani ba”, amma za ta je kotu. Na ce mata, “A’a, ai abin da su ke so kenan, a ce wacce ta na faɗa da su wane.” Na ce mata, “Tunda abin haka ya ke, kada ki yayata, a ƙarshe zai ji kunya.” 
 
Kuma abin mamaki, ita da maiɗaki na su na shiri matuƙa. Don har cewa ta ke yi  za ta zo ta kwashi ‘ya’ya na su je su yi hutu a wurin ta. 
 
To ka ga ana irin wannan mutuncin ya za a yi yaudara ta shigo ciki? Akwai mutunci mai ƙarfi da girmamawa a tsakanin mu.
 
FIM: A ƙarshe, me za ka ce wa mutanen da ke kallon ‘yan fim mata a matsayin waɗanda ba su zaman aure?  
 
CIROMA: Shawara ta farko, mutum ya ɗauki abin da ya ke yi ibada ne. Ina yawan faɗa wa mutane aure fa ibada ne. Ka ga sallar asuba raka’a biyu mu ke yi, don Alhaji Abba na jin ƙarfi ba zai ce yau raka’a huɗu zai yi ba; ka na yin huɗu menene sunan ka? Ai ka ga ka fita daga tsarin yin sallar, ko? Azahar ba za ka ce za ka yi raka’a ɗaya ka tashi ka yi tafiyar ka ba, bai yiwuwa; hatta a tafiya aka ce ka yi ƙasaru saboda sauƙi, da sauran su. Ibada ba ka yin ta yadda ka ke so da son ran ka, sai yadda Allah ya tsara maka. 
 
In ka bi wannan tsarin, sai ka ce aure ma ai ibada ne, ba za mu zama kaso ɗari ba gaba ɗaya, don mu ba ma’asumai ba ne. 
 
Shawara ita ce, duk wanda ya ke tunanin zai auri mace, Hadisi ya sauƙaƙa mana komai. Wanda duk ya zo yin abu da niyyar da ya zo yi da ita zai raka rayuwar sa. 
 
Abin da ke kawo matsala ga ‘yan fim: na ga yarinya ta na shiga fulawa, ta na karya ɗankwali, sai kawai in taho da ‘yan kuɗaɗe na in zo in nuna mata ƙarya. Duk masu wannan abin ba laifin ‘yan fim ɗin ba ne, laifin su mazajen ne. Na faɗi wannan ne sosai saboda ni a ‘practically’ na ke faɗi saboda ina da ‘experience’, kuma in za a lissafa a ‘yan fim ba na jin mun kai mu biyar. Kuma a cikin mu biyar ɗin nan babu wasu ‘yan fim da su ka zauna sama da shekarun da mu ka zauna tare da Wasila. Sai dai ka ga ɗan fim ya auri wadda ba ‘yar fim ba sun daɗe. Sani Danja da Mansurah Isah ‘yan fim ne, su na zaman lafiya, amma shekarun su bai kai sha takwas ba, su ne dai za su zo na biyu. Amma dai sha takwas sai ko a bincika, amma ni ban sani ba. 
 
Abin da ya sa na ce laifin mazan ne, su ke lalata komai, sai su ce ai da ma ba su zaman aure, wata biyu ko uku ne sun fito. Mazan su ke zuwa masu da ƙarya. Ka zo mata da gaskiya ka ga in ba ku zauna lafiya ba. Don haka mutum ya tsarkake niyyar sa, shi ne abu na farko, kuma shi ne abu na ƙarshe. Shi ya sa Manzon Allah ya ke cewa duk aiki ya na tafiya ne bisa niyyar ka. Ayyukan su za su fitar da abin da ke ran mu. Wannan shi ne.
A cewar Al-Amin Ciroma, wani abokin sa ya kusa kashe masa aure da Wasila

Loading

Previous Post

Duk da gobara, mun shirya wa zaɓen gwamnan Ondo, inji shugaban INEC

Next Post

Gasar Aminiya- Trust: An fidda gwarzaye 20 na matakin kusa da ƙarshe

Related Posts

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara
Ranar Murna

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara

October 10, 2026
Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa
Ranar Murna

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa

September 28, 2026
An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff
Ranar Murna

An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff

September 7, 2026
Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya
Ranar Murna

Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya

September 5, 2026
Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Next Post
Gasar rubutu ta Aminiya-Trust ta haɗaka ce tsakanin kamfanoni

Gasar Aminiya- Trust: An fidda gwarzaye 20 na matakin kusa da ƙarshe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!