FITACCIYAR jaruma mai ritaya, Mansurah Isah, wadda ake wa laƙabi da Maman Iman, ta na ɗaya daga cikin matan Nijeriya masu shirya finafinai. Tun kafin ta yi aure ta fara ɗaukar nauyin shirya fim, wato ta zama furodusa a Kannywood.
Kamar yadda mu ka sha faɗa wa masu karatun mu, baya ga harkar fim, har ila yau Hajiya Mansurah ce jagorar wata ƙungiyar agajin jama’a mai suna ‘Today’s Life Foundation’, wadda ke taimaka wa mabuƙata a cikin al’umma.
Jefi-jefi, ta kan shirya babban fim ta sake shi don mutane su kalla su nishaɗantu kuma su ilimantu. Na baya-bayan nan su ne ‘Majalisa’ da ‘Akeelah’.
A yanzu haka jarumar ta ƙara yin wani hoɓɓasa ta shirya wani gawurtaccen shiri wanda waƙoƙin sa su ka mamaye soshiyal midiya da wasu kafafen yaɗa labarai. Fim ɗin, mai suna ‘Fanan’, ana sa ran zai fita nan bada jimawa ba.
Furodusar ta tattauna da mujallar Fim inda ta bayyana cewa labarin ‘Fanan’ ƙayatacce ne kuma mai ɗauke da faɗakarwa a cikin sa. Haka kuma ta bayyana wasu abubuwan da dama. Ga yadda hirar ta kasance:
FIM: Menene dalilin shirya wannan fim na ‘Fanan’?
MANSURAH: To, da farko assalamu alaikum! Alhamdu lillahi, fim ɗin ‘Fanan’ na shirya shi ne duba da wani abu da ya faru a kusa da ni; ba wai ni abin ya sama ba, amma kusa da ni abin ya faru, inda wata baiwar Allah ta na ladabi da biyayya ga aure amma shi kuma mijin ba ya ganin kyautatawa da ta ke yi na aure, wanda don tsabar kyautatawar da ta ke masa ya ce shi ba ya so, ya gaji, ya sake ta To amma duk da sakin da ya yi mata ta ƙi tafiya, ta ci gaba da zama domin ta na tunanin mahaifin ta shi ya umarce ta da ta yi auren kuma ba ta so a ce wai yau ta ƙi bin umarnin mahaifin ta. To amma kuma da ya ke ba ya ganin shi wannan abin da ta ke masa shi ya sa ya ke mata wulaƙanci da cin zarafi da ita da ‘yar da ta haifa masa.

Wannan abin kuma ya faru ne da gaske, kuma wacce abin ya faru da ita ta ba ni dama da izini in nuna in yi fim a kai. To ka ji dalilin yin wannan fim na ‘Fanan’ kenan.
FIM: Shin ko mecece ma’anar kalmar ‘fanan’?
MANSURAH: ‘Fanan’ ya na nufin ‘kamila’ ko a ce natsattsiya.
FIM: Mai karatu zai so jin shin wannan fim ɗin na haɗin gwiwa ne ko ke ce ki ka shirya shi ke kaɗai?
MANSURAH: To, kamar dai yadda mutane su ka sani, na daɗe ina shirya fim; ina jin tun lokacin da na ke fim industiri na ke shirya finafinai, tun lokacin da na yi fim ɗin ‘Majalisa’, na yi fim ɗin ‘Sakna’ – (mai waƙar) “Uwargida Ran Gida Shaba Ya Na Miki Rawa”… Kai, finafinan ma ba zan iya tunawa ba! NZa zo na yi su ‘Akeelah’ na kwanan nan, na zo kuma yanzu na yi ‘Fanan’. Don haka ni na shirya abu na ni kaɗai.
FIM: Waɗanne jarumai ‘Fanan’ ya ƙunsa?
MANSURAH: Jaruman dai sun haɗa da Sani Musa Danja, Yakubu Muhammad, Ali Nuhu, Sabira Mukhtar wacce sabuwa ce yanzu a masana’antar fim, su Rahma M.K., akwai ‘ya’ya na irin su Khalifa Sani Danja da Khadija Sani Danja.
FIM: Yaushe aka ɗauke shi, ganin cewa ga Sani Danja a ciki?
MANSURAH: Mun fara ɗaukar fim ɗin tun shekara ta 2020 a watan Desamba, zuwa watan Fabrairu, mu ka gama ɗaukar duk abin da za mu ɗauka. Amma ba mu yi waƙoƙi ba, sai mu ka tafi hutu domin a lokacin ina ta ƙoƙarin in samu lokaci amma a lokacin ban samu ba saboda ana so a farfaɗo daga annobar korona, wato COVID-19. Rashin samun lokacin shi ne bai ba ni ƙwarin gwiwa in samu na ƙarasa waƙoƙin ba.
FIM: Muryoyin su waye ake ji su na rera waƙar ‘Fanan’?
MANSURAH: To, muryar namijin dai Umar M. Shareef ne, sai kuma Zubaida ‘yar Kaduna da ta yi muryar mace a cikin waƙar.
FIM: Waƙoƙi nawa ne a fim ɗin?
MANSURAH: A ƙa’idar fim ɗin waƙoki guda uku ne, wanda Sadiq Mafiya wanda shi ne ya bada umarnin waƙoƙin fim ɗin gaba ɗaya. To a ƙa’ida waƙa guda uku ne, sai waƙoƙi guda biyu mu ka iya samu mu ka yi saboda ka san a duk lokacin da na zo zan yi aiki ina yin sa mai inganci; idan na ga cewar ba zan samu mai inganci ba, to na kan haƙura da wani abin.
Don haka waƙa uku ce a cikin fim ɗin, amma kuma ba mu samu mun ƙarasa na ukun ba, kuma waƙa na ukun wani abin mamaki ya kamata ya zamar wa mutane, to kuma Allah bai yi mun samu mun yi ba. Amma har yanzu fa ba mu fidda rai ba a ko da yaushe zan iya wannan waƙa ta cikon ukun, sannan in saka ta a ciki.
FIM: Me ‘yan kallo za su zata dangane da ingancin labarin, da tsarin fim ɗin da kuma kyan hoto da sauti?
MANSURAH: Kamar dai yadda mutane su ka sani, alhamdu lillahi, yawancin finafinai na akwai harkar ‘yan gayu, ‘yan gayu haka a ciki. Mun yi amfani da babbar abar ɗaukar hoto ta zamani kuma mun samo wanda ya san kyamarar ta zamani yadda ya kamata, kuma shi kan sa wanda ya bada umarni ɗan gayu je, wato Isah Alolo. To ni ma da na ke a matsayin wacce ta ɗauki nauyin wannan fim ɗin ni ma ‘yar zamani ce! Mu kan duba me duniya ta ke so, meye duniya ta ke tsammani a harkar fim, meye za mu iya yi da zai kawo wa harkar fim inganci har ma manyan masu kuɗi, har shuwagabanni za su ce za su kalla. To na kan duba wannan kafin mu yi fim.
Don haka mutane su tsammaci abubuwa masu kyau, ingantaccen labari da zai bada ma’ana kamar yadda aka yi fim ɗin ‘Akeelah’ wanda ya zama darasi ga iyaye da yawa har ma wasu su na kira na, wasu kuma har kuka su ke yi a kan cewa wallahi wannan labari da mu ka bayar kamar mun shigo cikin gidan su mun ga me ke faruwa. To in-sha Allahu wannan ma ba mu fidda rai ba. Amma duk da cewa ka san shi ɗan kallo ba a fiye ba shi abin da ya ke so ɗari bisa ɗari ba.

FIM: Me za ki ce game da tsarin tallata fim ɗin da ki ka yi ta hanyar yaɗa waƙar ‘Fanan’ wacce mutane har a ƙasar waje su ka dinga yin ta a soshiyal midiya, sannan ga gasar da ki ka saka a kan waƙar?
MANSURAH: Kowa ya na da nasa salon na tallata fim ɗin shi, kuma kowa ya na da irin ɗaukakar da Allah ya ba shi. Ni ta ɓangare na, mutane su na so na, su na ƙauna ta duba da yadda ni ma na ke kyautata wa wasu mutane. Dalilin kyautata wa wasu in faranta musu rai, to wasu ma su na ƙauna ta, ba wai don ni ɗin ba, a’a, kyautatawar da na ke yi ya sa wasu su na ƙauna ta. Kuma na san duk abin da na fito na ce ina so su taimaka min su ma su so wannan abin, to iyakaci gwargwado mutane su na so.
Wasu ma su kan ba ni waƙar su su ce na yi musu don Allah kan mutane su ji shi, balle kuma nawa na kai na; in wani zai biya ya ce na yi masa tallar waƙoƙin fim ɗin sai in ce ba zan yi ba wanda duk abin da aka samu dai ni zai dawowa?
Sannan kuma tallar da na yi wa wannan fim ɗin ban ji a cikin masana’anatar shirya finafinai ta Kannywood an yi irin wannan talla ba, allon da ake tallar shi a kan tituna guda goma mu ka yi a Kano. Kuma na tabbata yau in za ka zagaya Kano, yanzu akwai wurare da dama da za ka tarar da waɗannan allunan da mu ka yi. Sannan ban da gidajen rediyo da mu ka ba wa talla da kuma gidan talbijin. Akwai kuma irin su yanar gizo da sauran ma wasu wuraren zamani.
FIM: Yaushe fim ɗin zai fito, kuma ta wace hanya?
MANSURAH: Wato mu na da hanya uku da mu ke sa rai za a samu damar kallon fim ɗin ‘Fanan’. Hanyoyin sun haɗa da:
1. za mu sake shi ta hanyar sinima, wato akwai wani sabuwar sinima mai suna ‘Platinum Cinema, Kano, kuma sun sayi damar sa ta cewa su kaɗai su ke so su nuna. Bayan lokacin da su ka gama ne kuma za mu iya ɗaukar sa mu kai shi wata sinima ɗin su ƙara nuna shi.
2. Sannan kuma hanya ta biyu shi ne ta ‘Africa Magic’ (talbijin). Mu na sa rai za mu daidaita da ‘yan ‘Africa Magic’, bayan Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta gama ba mu takarda ta shaida.
3. Bayan mun gama da su, za mu sake shi a YouTube domin waɗanda su ke ƙasashen ƙetare ba za su iya kallon ‘Africa Magic’ ba.
Sannan a ranar 26 ga Oktoba, 2021 za mu fara nuna shi a matsayin firimiya.
Su ma na DSTV mu na magana, amma mun san nan da kwana uku zuwa biyu za mu samu matsaya da su.
FIM: Me za ki ce game da lalacewar kasuwar fim, hatta a sinima? Shin gaban ki ba ya faɗuwa?
MANSURAH: E to, da farko dai in zan yi fim ba na tunanin zan taɓa maida rabin kuɗin da na kashe a fim, haka kuma ya na nufin ni Mansurah Isah ba na yin fim don na ci riba; ina yin fim ne don in ƙara martaba da darajar industiri ɗin in dai zan iya zuba jari na a fim in yi shi da ƙololuwar inganci wanda har wani babban mai muƙami a Nijeriya zai ce, “Ina so na kalli fim ɗin nan,” to buri na ya cika a rayuwa.
Buri na shi ne waɗanda su ke ganin ƙasƙancin mu, ba ma sa son su yi alaƙa da fim ɗin Hausa ko ‘yan fim ɗin Hausa, to ina so na canza tunanin su na cewa ba kowane fim ne ya ke ba daidai ba ko kuma ba kowane fim ne ba shi da kyau ba. In ka duba, da man mu a al’adance ba ma taɓe-taɓe, ba ma rungume-rungume. Ba wani fim ne da za a ce yaro ba zai iya kallo ko wani abu ba, ba abin da ake a fim ɗin mu; daga “Baba ina son shi” sai “Inna ina son ta”. To amma ni ina son na canza tunanin mutane cewa labari da irin abubuwan da mu ke da shi a arewacin Nijeriya, ya wuce fim ɗin soyayya.
Mu na da wasu ayyuka da za mu fara nan da watanni uku zuwa biyu in-sha Allahu, wallahi labari ne da duk wanda ya ji shi sai ya yi kuka, amma kuma alhamdu lillah ni na kan so na nuna wa mutane cewa irin abubuwa da ake gani da abubuwan da ke faruwa a arewacin Nijeriya ya fi a ce wai kullum fim ɗin soyayya ake yi.
Tun da na ke yin fim ban taɓa yin fim ɗin soyayya a rayuwa ta ba. Idan ka duba, duk finafinai na ba inda aka taɓa yin soyayya a ciki domin mu na da labarai da yawa waɗanda za mu iya isarwa.
Mu fim industiri na sha faɗa mu ba masallaci ba ne ba, kuma ba Islamiyya ba ne ba; duk mutumin da ya ce ai wai fim ya na koyon nasiha da darasi a fim zai koya wa ‘ya’yan sa yanda ake tarbiyya ko yanda ake sallah ko yanda ake gaskiya ko yanda ake amana, to ya raina wa kan sa hankali.
Industiri neman kuɗi ne, masan’anta ce ta nishaɗantarwa, ba industiri ɗin koyar da addi ba ne. Ba a fim za a koya maka yadda ake alwala ake sallah ba. Shi ya sa masallaci ya ke sunan shi masallaci, Islamiyya ya ke sunan shi Islamiyya, malamai su ke sunan su malamai, mu kuma masu nishaɗantarwa ne, wanda a cikin nishaɗantarwa ɗin za mu iya kawo abin da zai iya amfane ku, wani lokacin kuma za mu iya kawo muku shiriritar da ban da dariya ba abin da za ku yi ta yi don da yawa abin da ke faruwa a fim ƙarya ne a ce zai faru a zahirin gaske.
Don haka in mutane su na cewa wai a haka wai su na koya tarbiyya ne, mu ba mu ce Islamiyya ba ne. Ni dai Mansurah Isah za ka kalli fim ɗi na za ka koyi hankali, za ka koyi abu, amma fa ka sani ni ba masallaci ba ne, kuma ni ba Islamiyya ba ne.
Don haka ku kalli fim ɗin mu domin ku yi nishaɗi domin ku ji daɗi, domin in ku na da wani damuwa in ka kalli fim ɗin su Bosho da sauran su za ka yi dariya, in ka na cikin damuwa damuwar ka za ta ɗauke.
Saboda haka mu in ka kalli fim ɗin mu ko dai ya sa ka yi hankali ko kuma ya kwantar maka da hankali, ya ba ka nishaɗi. To shi ne kawai.
FIM: Wane shiri ki ka yi na tabbatar da cewa jama’a sun je kallon fim ɗin?
MANSURAH: E to, kamar yadda na gaya maka daga baya, cewa mun yi allon tallika guda goma a garin Kano, wanda ba a taɓa Hausa fim da aka yi masa wannan allo ba, sai dai a ɗan yi wata kalanda a ajiye shi wani wuri. Amma mu mun yi wajen guda goma a Kano. Sannan kuma kamfaninnika da dama su ma sun ba mu haɗin kai, sun ji daɗi cewa mun neme su, sun goya mana baya.
Sai kuma tallatawa da mu ke yi a yanar gizo ba dare ba rana. To mu na fatan Allah ya sa mana albarka.
FIM: Masu so su kalli fim ɗin a wasu garuruwa, ya za su yi?
MANSURAH: Da man na faɗa akwai ‘Africa Magic’ da kuma DSTV da mu ke sa ran za mu kammala magana da su. Sannan kuma daga ƙarshe bayan mun gama haska shi a wuraren sai mu ɗora shi a YouTube.

FIM: A matsayin ki na furodusa, me ya sa Mansurah ba ta shiga yayin shirya fim mai dogon zango ba don sakawa a YouTube kamar yadda wasu ‘yan Kannywood ke yi?
MANSURAH: To, ina ganin yadda mutane ke yi, amma ba abu ne da kawai lokaci guda zan jefa kai na a ciki ba. Ka gan ni nan, ni mayyar kallon finafinai masu dogon zango ce. Ina da son kallon sa na fitar hankali, kuma na kan samo wasu abubuwan daga kallon wannan fim mai dogon zango. Amma ni ba mace ba ce da a lokaci ɗaya na ke tsalle na ga na je inda ake so ba.
Mu na sa rai cewa fim ɗin mu na gaba da za mu yi, za mu yi shi ne mu ɗan yanke shi a matsayin fim mu nuna shi a sinima, mu nuna shi a DSTV ko Arewa24, duk wanda Allah Allah ya ƙaddara mun shirya da su; mu nuna shi a YouTube na cewa fim ne. Amma ka sani, inda za mu tsaya za ka san cewa fa akwai ƙarashe, wannan fim ɗin bai tsaya a nan ba, don haka yanzu aikin mu na gaba abinda mu ke sa rai kenan. To amma kuma duk da haka mu na duba ta yaya za mu iya, ta yaya za mu bi mu yi fim mai dogon zango ɗin da mutane za su ji daɗi, za su dinga samun nishaɗantarwa da faɗakarwa a ciki, shi ne kawai.
FIM: Ko akwai yiwuwar nan gaba a ga Mansurah ta fito a wani fim musamman ganin cewa kin rera waƙar ‘Fanan’ a wajen tallata shi?
MANSURAH: E to, akwai wasu ayyuka da na ke da su wanda ba a Nijeriya ba gaskiya. Fim ne wanda ya ke ‘documentary’, amma ba a Nijeriya ba gaskiya. Har ma mun ƙulla yarjejeniya da masu fim ɗin, amma ba a nan ƙasa Nijeriya ba.
To, amma kuma zuwa yanzu ba ni da tunanin ko kuma sha’awar shiga fim ɗin Hausa. Ko wancan ma da na ke so na yi abu ne wanda ya ke na tarihi kuma su na neman mutanen da za su ba su abin da su ke so. Kuma in aka ce abu akwai biya, ka gane, akwai isasshen kuɗi, to yawwa!
FIM: Yaya ake ki ke samun kuzari da sukunin haɗa furodusin fim, gudanar da iyalin ki, da tafiyar da harkar gidauniyar ki, ga kuma sauran al’amura irin su bukukuwa da sauran su?
MANSURAH: Wallahi wallahi a gaskiya ina shan wahala, kuma abu ne wanda ba shi da sauƙi gaskiya. Rayuwa ta gabaki ɗaya babu hutawa. Ayyukan da na ke yi ba su da sauƙi. To amma dai Ubangiji ya na ba ni ƙarfi da ƙwarin gwiwa, ya na taimaka min a wasu abubuwan, domin wani lokacin in na ga abin ya yi mani yawa kawai sai na tashi da tsakar dare in yi sallah nafila raka’a biyu in ce, “Allah ka na gani.”
Kuma ni a yanzu ina ganin cewa duk waɗannan abubuwan da su ke zo min a yanzu ba wai matsala ne ba, Allah ya ba ni wata dama ne karo na biyu. Lokacin da na samu dama ta farko ina ƙaramar yarinya, ba ni da hankali, ba ni da wayo, ban san ciwon kai na ba, ban san me ya kamata na yi a rayuwa ba a lokacin da mu ke samun maƙudan kuɗi. Amma duk wani sa hanun jari, ajiye kadara in ba wai wasu ‘yan ƙalilan da addu’ar iyayen mu ma wasu mu ka iya ajiye su ba, ba abin da nu ka yi da ɗaukakar da mu ka samu a baya. Amma sai yanzu kuma Allah ya sake dawo mana da ɗaukakar nan kuma ya ba mu dama ta biyu, domin ba kowa ne Allah ya ke ba wa irin wannan damar ba. To shi ya sa ka ga duk abin da ya zo mani ko ka gaji zan ta shi na yi shi domin dama ce da Allah ya ba ni wanda ba kowa ya ba wa ba. To kuma ba na so na zama butulu; ni na ke neman, amma kuma sai in ce ni a’a wallahi ya yi min yawa! Bai min yawa ba. Allah, in da ƙari ma a ƙara min!
FIM: Mansurah na hutawa kuwa?
MANSURAH: In na fara aiki in ba wai na ga na kammala ba, gaskiya ba na hutawa. Amma kuma in na tashi hutawa kamar yanzu ka gani da ka zo ka same ni na ce maka zan yi tafiya jibi, to in na yi tafiyar nan to da ƙyar za a samu kai na don saboda sai na ware kamar kwana uku ko huɗu kawai sai dai na yi bacci na yi sallah na kuma ci abinci. Zan yi kwana uku ina wannan abin.
Inda za ni ma ran da na isa washegari ina da aiki. In na gama aiki – kwana ɗaya ne – zan ware kamar kwana uku zan huta. Daga kwana na uku na huɗu zuwa na biyar kuma zan fara aikin uwarɗaki na, wato Dakta Zainab Bagudu; za ta yi wani tattaki na fatattakar ciwon daji, wato kansa, kuma mu na da irin su tattaunawa da ‘yan jaridu, ziyartar asibitoci inda mu ke biya wa masu cutar daji a yi musu kemo (chemotheraphy) na shekara ɗaya kyauta. Duk wata riga da hula da mu ke sayarwa, to kuɗin mu ke haɗawa sai ita ɗin matar Gwamnan Kebbi, wato Dakta Zainab Bagudu, sai ta kira mu mu raka ta. Sai mu je asibutoci kamar Babban Asibitin Abuja, mu bibbiya musu kuɗin aiki na shekara ɗaya.
Don haka ka ga ina da wannan aiki da zan shiga yi a Abuja, wanda kuma zai kusan ɗauka na wajen sati ɗaya ma ina yi. To ka ga shi ma idan na gama aikin shi ma zan huta kamar kwana biyu, sai in dawo gida kuma in ci gaba da tallar fim ɗin ‘Fanan’ kamar yadda na ajiye.
FIM: Wane saƙo ki ke da shi ga masoyan ki duba da irin soyayyar da su ke nuna miki?
MANSURAH: Abin da zan iya cewa shi ne: Ku ci gaba da ƙaunar mu, ku ci gaba da kallon finafinan mu domin mu ci gaba da nishaɗantar da ku, domin mu ci gaba da faranta muku rai, domin mu ci gaba da jin daɗi in ku na kallon finafinan mu. Don Allah don Annabi kar ku juya mana baya. Mu na ƙoƙari mu ga mun sa ku farin ciki ta hanyar yin finafinai masu kyau duk kuwa da cewa in mu ka yi kuɗin mu ba dawowa ya ke ba domin satar basira da kuɗin da ba kallon fim ɗin mu ku ke ba ya na sa mana koma-baya, kun fi son kallon fim ɗin ‘yan Legas, wanda su ke rungume-rungume, su ke sumbata. Mu fim ɗin mu da mu ke sa addini ma a ciki da ba ma rungume-rungume ba kwa son kallon mu. Kullum mu ka fito sai ku ce mana ‘yan camama ne!

Ban da haka ma, wani lokacin idan an ga ɗan fim a gidan mutum kamar wani sheɗan ne ya shigo mishi gida, wanda kuma idan aka ce a bibiye shi a kan abin da ya ke yi a gidan ma ƙazantar ya fi na wani waje. Amma to ba mu da abin da za mu ce sai mutanen nan sun ja mu a jiki sun ƙaunace mu sannan za mu samu cigaba, sannan yaren Hausa ma ya samu cigaba a ƙasa da duniya ma baki ɗaya.
Mu na gani yanzu wani fim aka saka kwanan nan, ‘Squed Game’, na ‘yan Koriya ne kuma yaren Koriya aka yi, amma yanzu a dalilin ƙauna da kuma karɓar fim ɗin da mutanen duniya su ka yi ya zama ɗaya daga cikin finafinan da aka fi kallo a Netflix a tarihin duniya baki ɗaya. Duk inda ka je yanzu sai maganar ‘Squed Game’; kuma ba Amerikan fim ba ne. To ashe kenan in mu ka samu goyan bayan manyabɗn mu da shuwagabannin mu mu ma za mu iya yin kwatankwacin wannan domin mu Kannywood mun fi kowa a Afrika samun labarin da za mu iya yin fim a kai. Mu na da usuli, mu na da labarai da yawa da za mu iya yin fim da su wanda kuma duniya za ta karɓa. Amma kuma ina! To ba mu da jarin, ba mu da kuma wanda zai tsaya mana.
Matuƙar za mu samu taimakon su, sai ka ga da taimakon Allah da su sai a samu abin da ake so gabaki ɗaya.
![]()







