ƊIYAR tsohon Shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Malam Murtala Muhammad Aniya, ta rasu.
Fatieha Murtala Aniya, ‘yar kimanin shekara 9 zuwa 10, kuma ita ce ta uku a cikin ‘ya’yan sa, ta rasu ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Lahadi, 26 ga Yuni, 2022 a Asibitin Mu’awiyya da ke Tudun Nufawa, Kaduna.
Aniya, wanda darakta ne kuma jarumi, ya shaida wa mujallar Fim cewa Fatieha ta ɗan yi zazzaɓin maleriya na kwana biyu, amma ta samu sauƙi har ta je Islamiyya a ranar Asabar, an saka ta a cikin waɗanda za su yi hadda nan da shekara ɗaya, kuma da ma ta yi haddar izu talatin.
Ya ce: “Ka ga kenan ana gobe za ta rasu ta je makaranta.
“To, mu mun ɗauka ciwon ba mai damuwa ba ne, tunda an sha magunguna, an yi allurai, ta samu sauƙi ta tafi makaranta, ashe ciwon na ajali ne. Allah ya jiƙan ta da rahama.”
An yi addu’ar kwana uku a safiyar jiya Laraba, 29 ga Yuni, a Layin Asibitin Azhar, kusa da Primary Health Care, bayan Layin Iman Academy da ke Hayin Ɗanmani, Kaduna.
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka je ta’aziyya sun haɗa da Malam Ibrahim Tahir, Sabi’u M. Gidaje, Hamisu Ba Wasa, Nura M.C., Baba Ali Kabala, Sanusi Ɗansunu, Hajiya Fatima Lamaj, da Ibrahim Zariya.
Allah ya jiƙan Fatieha, ya sa mai ceton iyaye ce, amin.