A daren jiya ne Allah ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, rasuwa. Shekarun sa 92.
Za a yi jana’izar sa a yau a Birnin Kano.
An haifi Alhaji Abbas ne a Bichi a cikin 1933. Ya yi makarantar elementare ta Ƙofar Kudu a Kano a cikin 1944. Da ya gama, ya tafi Kwalejin Rumfa a cikin 1948. Ajin su ɗaya da mariganyi Galadiman Kano da ya gabace shi, wato Alhaji Tijjani Hashim, kuma a shekara ɗaya aka haife su.
Memba ne a majalisar Sarkin Kano tun a shekarun 1950.
Sarkin Kano na yanzu, Malam Muhammadu Sanusi II, shi ne ya naɗa shi Galadiman Kano. A lokacin, Sarki Bai, Hakimin Ɗambatta, Alhaji Mukhtar Adnan, kaɗai ne ya girme shi a majalisar Sarki.
Rabon da a naɗa Galadima tun 1992 lokacin da Sarkin Kano Ado Bayero ya naɗa Alhaji Tijjani Hashim wannan sarautar. Da Tijjani Hashim ya rasu yana da shekaru 81 aka naɗa Abbas.
Tun a zamanin mulkin Haɓe ne aka samar da sarautar Galadiman Kano, wato kafin Jihadin Fulani da aka yi a 1804, kuma shi ne muƙamin sarauta mafi girma bayan Sarki, har zuwa 1890 lokacin da aka aro sarautar Waziri daga Sakkwato. Daga nan Galadima ya zama na biyu a jerin manyan masu sarauta a Kano.
Abbas Sanusi kawu ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II domin kuwa ɗa ne ga kakan Sarkin, wato Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi I.
Mahaifin sa ne ya fara ba shi sarauta, da ya naɗa shi Sarkin Dawakin Tsakar Gida kuma Hakimin Ungogo a cikin 1959. Sarkin Kano na gaba, wato Muhammadu Inuwa, ya ɗaga darajar sa da ya naɗa shi Ɗan’iyan Kano a cikin 1962. Da ya rasu, Ado Bayero ya naɗa shi Wamban Kano, muƙamin da ya riƙe har zuwa lokacin naɗin sa matsayin Galadima.
Lokacin da Ado Bayero ya tafi asibiti a yayin ciwon ajalin sa, shi ne ya riƙe masarautar. Kuma da Ado ya rasu, yana daga cikin waɗanda suka yi takarar sarautar, amma sai Allah bai ba shi ba.
Allah ya rahamshe su baki ɗaya.