• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gudun zuwa kotu, Adam A. Zango ya ba matar sa Safiyya Chalawa takardar saki

by DAGA ALI KANO
April 12, 2023
in Labarai
2
Adam A. Zango da Safiyya Umar Chalawa

Adam A. Zango da Safiyya Umar Chalawa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A ƘARSHEN ƙarshe, shahararren jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Adam A. Zango, ya saki matar sa, Safiyya Umar Chalawa, watanni biyar bayan ta yi yaji sakamakon rikicin da ya addabi auren nasu.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta kusa da Zango ɗin ta shaida wa mujallar Fim cewa jarumin ya yi sakin ne a shekaranjiya Litinin inda ya aika mata da takardar a gidan iyayen ta da ke Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

Da ma ya taɓa sakin ta tun ta na amarya, amma ba ta kai ga komawa gida ba ya mayar da auren nasu.

Saboda haka a yanzu saki biyu ya tabbata, wanda ake ganin daga wannan dai magana ta ƙare.

Wannan shi ne sakin mace ta shida da Zango ya aura a rayuwar sa.

Wata majiya ta shaida wa wakilin mu cewa da farko Zango ya finjire ya ce ba zai saki Safiyya ba duk da yake ta sha alwashin ba za ta taɓa komawa gidan sa ba.

Amma sai iyayen ta su ka yanke shawarar kai maganar kotu domin a kashe auren. “Da ya ji haka ne ya ba ta takarda don gudun a yi fallasa,” inji majiyar.

Meera Shu’aibu

Idan kun tuna, a watan Fabrairu mujallar Fim ta ba ku labarin yadda rikicin da ya turnuƙe tsakanin ma’auratan biyu ya fito fili sakamakon wani bidiyo da Zango ya wallafa a TikTok kan yanayin zaman auren sa.

A bidiyon mai tsawon minti uku, ya bayyana saɓanin da ke tsakanin sa da Safiyya wanda ya yi sanadin barin ta gidan sa.

Bidiyon na kare kai ne daga zargin da matar tasa ta yi masa na kasa kulawa da gida a wani saƙon murya da ta tura wa wata mata mai suna Anti Fati wadda ke zaman Saudiyya.

Duk da yake Zango ya tabbatar wa da duniya cewa bai kai ga sakin Safiyya ba a lokacin, amma ya ce akwai yiwuwar zai sake ta ɗin idan har ba a sasanta ba.

A lokacin da ya yi bidiyon, ɗimbin masu sharhi a soshiyal midiya sun nuna masa bai kyauta ba da har ya fallasa sirrin gidan sa a kafar sada zumunta. Hakan ya sa ya yi wuf ya goge bidiyon daga shafin sa, to amma a lokacin har wasu sun kwafa.

Bidiyon ya bazu a soshiyal midiya kamar wutar bazara, kuma ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sharhi.

Zango ya yi ƙaurin suna wajen auri-saki, domin kuwa Safiyya ita ce mace ta shida da ya aura ya saki.

Da farko ya auri Amina ‘yar garin Kaduna a cikin 2006, ta haifa masa ɗan sa na farko, Haidar, wanda a bana ya cika shekara 16 da haihuwa. 

Da ya sake ta, sai ya auri A’isha, wadda ‘yar’uwar sa ce ta jini, daga garin Shika da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Ta haifa masa ‘ya’ya maza uku. 

Jarumin ya auri matar sa ta uku mai suna Maryam daga Jihar Nasarawa. Ita ma ya sake ta.

Sai ya auro jarumar Kannywood mai suna Maryam A.B. Yola daga unguwar Lugbe a Abuja a cikin 2013. Kafin nan sun fito tare a cikin fim ɗin ‘Nas’. 

A cikin 2015, Zango ya tsallaka ƙasa zuwa garin Ngaoundere a Jamhuriyar Kamaru ya auro Ummul Kulsum. Ita ce ta fara haifa masa ‘ya mace, wadda ya raɗa wa suna Murjanatu.

Da ya sake ta ne ya auro Safiyya, wadda aka ɗaura auren sa da ita a ranar Juma’a, 26 ga Afrilu, a 2019 a masallacin fadar Sarkin Gwandu da ke garin Gwandu a Jihar Kebbi.  

Sun haifi ‘ya mai suna Furaira (sunan mahaifiyar sa), wadda ake wa laƙabi da Diana, a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

Diana ce ta bakwai a jerin ‘ya’yan Adamu (maza huɗu da mata uku), kuma abin lura shi ne kowane ɗa uwar sa daban.

A lokacin da aka yi auren Zango da Safiyya, mutane sun taya su murna, yayin da wasu ke tababar ɗorewar auren saboda yadda ake kallon jarumin a matsayin mai auri-saki.

Mujallar Fim ba ta san takamaiman dalilan mutuwar aurarrakin Zango guda biyar ba, amma ya faɗi dalilin saɓanin sa da Safiyya.

A cewar sa, ta na kasuwanci irin na intanet ne a asirce ba tare da sanin sa ba, kuma da ya hana ta sai ta ƙi bari, tare da ɗaurin gindin ‘yan’uwan ta.

A bidiyon da ya wallafa a cikin Fabrairu, ya ce: “Tunda sun zaɓi kasuwancin da ta ke yi fiye da zaman auren ta, ba ni da zaɓi. A kowanne lokaci daga yanzu, za a ji labari mara daɗi. A gafarce ni, wannan shi ne. 

“Saboda ina sananne ba zan kashe kai na saboda mabiya na ko masoya na in birge su ba in ci gaba da zama da baƙin ciki saboda babu yadda na iya.”

Sai dai kuma binciken da mujallar Fim ta yi ya gano cewa babban abin da ya farraƙa ma’auratan shi ne soyayyar da Adamun ya yi da jarumar shirin sa mai dogon zango da ya ke shiryawa mai suna ‘Asin Da Asin’, wato Meera Shu’aibu, wadda aka fi sani da Junaidiyya ta cikin diramar ‘Gidan Badamasi’.

Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunan ta ta faɗa wa mujallar Fim cewa Meera ta zama silar mutuwar wannan auren ne saboda soyayyar da Zango ya yi da ita ce ta jawo saɓani tsakanin sa da Safiyya wanda har ya kai matar tasa ga barin gidan auren ta a Kaduna, ta koma Kebbi.

“Meera ta so auren Adamu, kuma shi ma haka, amma sai ya kasance mahaifiyar sa ba ta so, sannan shi ma ya yi wani bincike, saboda haka dai ya haƙura da auren ta,” inji majiyar.

Majiyar ta ce Safiyya ta bayyana cewa “ita ba ta damu da soyayyar sa da Meera ba in da auren ta zai yi, amma ba yadda su ke yi ba.

Majiyar ta ƙara da cewa, “A lokacin da Soffy ta koma Birnin Kebbi, Meera ta riƙa faɗa ma mutane cewa saboda ita ne Soffy da Adamu su ka samu saɓani. 

Safiyya tare da Furaira (Diana)

“To amma ba su tare yanzu, soyayyar tasu ta tarwatse. Kuma Meera ta lashi takobin cewa Adamu da Soffy ba za su taɓa sasantawa ba tunda har ya ci amanar ta.”

A bidiyon da ya saki a farkon wannan shekarar, Zango ya nuna ya san irin kallon da mutane su ke masa na aure-aure, har ya sha alwashin in dai har auren sa da Safiyya ya mutu to bai ƙara yin aure ba har abada.

Ya ce: “Ina ganin na gama aure. Da izinin Allah na gama aure, kuma ina roƙon Allah ya kare ni daga dukkanin abubuwan da na ke gujewa ya sa na ke ta yin wannan auren.”

To, yanzu da auren ya mutu za a zuba ido a ga idan zai ƙara yin auren ko a’a, da kuma irin rayuwar da zai yi ba tare da aure ba a matsayin sa na matashi mai jini a jika.

Loading

Tags: Adam A. ZangoaureKebbiMeera Shu'aibuSafiyya Umar ChalawasakiTikTok
Previous Post

An kama ‘yan sandan da ke bai wa Rarara kariya

Next Post

Shari’a kan zargin zamba cikin aminci ta N10.3m: Lauyoyin Rarara sun gurfana a kotu

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Dauda Kahutu (Rarara)

Shari'a kan zargin zamba cikin aminci ta N10.3m: Lauyoyin Rarara sun gurfana a kotu

Comments 2

  1. Fatima lamaj says:
    2 years ago

    Allah ya kyauta. Allah ya kaeo karshen aure suren nan. Babu dadi. Amma tun ran gini tun ran Zane. Allah ya rubuta akan hakan zai kasance da zango amma ya dage da adua Allah ya jaeo karshen haka, . Amma baton cewa bazai kara aure ba, wannan wasa ne. Domin da sauran shi kuma yana bukatan mace arayuwan sa. Allah ya kyauta.

  2. NURA MC KHAN says:
    2 years ago

    YA SUBUHANALLAH, ABUN DA AKE GUDU SAIDA YA AUKU, ALLAH YA KYAUTA, ALLAH YABAKA IKON CIN JARABAWAR DA TAKE TUNKARARKA A RAYUWA, KOWANI DAN ADAM DANASHI KADDARAN, MUNAFATA JADDARANMU TAZO DAIDAI DA YANDA HANKALI ZAI IYA DAUKA, MUNAKUMA ROKON ALLAH KADA YAJARABEMU JARABAWAR DA ZATAFI KARFINMU,
    ADAMU TAKE HEART, BAKA DA OPTION,. SAIDAI YAZAMA WAJIBI KA TOSHE KUNUWANKA, DOMIN BAZAKAJI MAGANGANU MASU DADIBA A KUNNENKA,
    MUNAFATAN ALLAH YABAKA DAMAN DA ZAKA KULA DA YARANKA CIKIN AMINCI, YAKUMA BAKA IKON ZAMA CIKAKEN JARUMI, INANUFIN JARUMI SHINE WANDA ZAI IYA HAKURI DA YANAYIN DA YA TSINCI KANSA, BAWAI JARUMI NA CIKIN FILM BA,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!