HUKUMAR ‘yan sanda ta Nijeriya ta tabbatar da kama wasu ‘yan sanda da su ke baiwa shahararren mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) kariya.
A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta jiya an ga ‘yan sandan su na bin mawaƙin a baya har ya shiga mota, daga nan su ka soma harba bindiga a sama.
Sai dai a wani saƙo da mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya, Muyiwa Adejobi, ya wallafa a Facebook, ya ce rundunar ‘yan sandan ƙasar nan ta yi tir da “rashin ƙwarewa da kuma halaye na rashin ɗa’a da ‘yan sandan su ka nuna inda su ke harba bindiga domin ɗaukaka darajar mawaƙin wanda hakan ya saɓa wa ƙa’ida.”
Mista Adejobi, wanda Babban Suferitendan ‘Yan Sanda ne, wato CSP, ya ce: “An gano ‘yan sandan kuma an kama su. Za a kai su hedikwatar ‘yan sanda domin yi masu tambayoyi tare da ɗaukar matakan da su ka dace.”
Ya ƙara da cewa: “Irin wannan ɗabi’a ba ta ‘yan sanda ba ce kuma ba za su lamunci hakan ba.”
Sai dai a wani bidiyo da mujallar ta ga ana hira da mawaƙin, Rarara ya musanta cewa ‘yan sandan sun yi harbi domin nishaɗi, ya ce wasu ne su ka yi niyyar tayar da tarzoma a garin su na Kahutu cikin Jihar Katsina lokacin da ya je raba kayan tallafin azumi, wanda ya sa su ka yi harbin.
Rarara ya ce: “Mun je mu na rabon abinci a Kahutu, sai wasu ɓata-gari su ka shigo su na neman su tayar da tarzoma, a nan wurin ne mu ka samu matsala, ‘yan sandan mu su ka yi harbi sama.”
Ya bayyana cewa dalilin da ya sa ‘yan sandan ba su harba barkonon tsohuwa ba shi ne ana azumi.
Ko a kwanan baya ma dai wasu matasa sun far wa ofishin mawaƙin a Kano tare da wasu da su ke kusa da shi, inda su ka ƙona tare da kwashe wasu kayayyaki.
Sai dai daga baya ‘yan sanda sun samu nasarar gano wasu matasan da kuma ƙwato kayan da su ka sata.