MAWAƘI, jarumi kuma furodusa a Kannywood, Lilin Baba, ya gwangwaje ɗaya daga cikin yaran sa, Murtala Abdulhameed (Bloko), da mota.
Lilin Baba, wanda sunan sa na ainihi Shu’aibu Ahmad Abbas, ya ba Bloko kyautar motar ƙirar Toyota LE a yau Asabar, 8 ga Afrilu, 2023.
Bloko ya ɗora hotunan motar tare da saƙon godiya ga Lilin Baba a Instagram, inda ya ce, “Ya Allah ina miƙa godiya a gare ka, kuma ina miƙa godiya ga maigidan mu Lilin Baba. Allah ya saka maka alfarmar wannan watan azumi mai albarka.”
Ba wannan ba ne karo na farko da mawaƙin ya ba wani yaron sa kyautar mota, domin kuwa a baya ya ba darakta Alfazazi Muhammad da kuma Sulaiman Sir Zeesu.
A halin yanzu a Jihar Kaduna babu wani ɗan fim da ke da halin da Lilin Baba ya ke da shi, kuma hannun sa a buɗe ya ke, sai dai idan rabo bai biyo ta kan ka ba.
Wannan dalilin ya sa yawancin yaran Adam A. Zango da na aminin sa Umar M. Shareef su ka koma ƙarƙashin sa.
A baya kowa ya san cewa Bloko ɗan gaban goshin Zango ne, masu kare muradin sa tare da cin mutuncin duk wanda ya taɓa maigidan nasu. Hasali ma dai shi ne direban Adamun, duk inda ka hange shi dole za ka ga Zango a wurin.
Sai dai kuma a yanzu Bloko da Zango ba su tare, hasali ma ko ga maciji ba a yi. Sannan kuma Bloko ya koma gidan Lilin Baba, wanda ba su shiri a tsakanin su tun bayan matsalar da su ka samu a kan matar Lilin Baba, Ummi Rahab, kafin su yi aure.
![]()







