• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 24, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnati ta ƙara wa’adin aikin tantance masu cin moriyar shirin N-Power kashi na uku

by DAGA WAKILIN MU
September 25, 2021
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta ƙara wa’adin aikin tantancewar ido-da-ido ta masu cin gajiyar shirin nan na tallafa wa matasa, wato N-Power kashi na uku, wato ‘Batch C’.

An ƙara wa’adin ne daga ranar 24 ga Satumba zuwa ranar 30 ga Satumba, 2021.

Shugabannin shirin na N-Power sun bayyana haka ne a wani saƙo da su ka wallafa a shafin su na Facebook a ranar Juma’a.

An bayyana cewa tilas ne duk mai cin moriyar shirin ya je da kan sa a tantance shi kafin a tura shi wurin da zai gudanar da aikin, wato ‘Place of Primary Assignment’ (PPA).

Sanarwar ta ce, “An ƙara wa’adin aikin tantancewar ido-da-ido da ake gudanarwa yanzu ta shirin N-Power ‘Batch C, Stream 1’ zuwa mako ɗaya. Ana sa ran masu cin moriyar shirin za su kammalatantancewar su ta ido-da-ido daga yanzu zuwa ranar Alhamis, 30 ga Satumba, 2021,” inji sanarwar.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa shirin N-Power ne a cikin watan Yuni, 2016 don magance matsalolin da rashin aiki na matasa ke haifarwa.

Shirin wani ɓangare ne na Shirye-shiryen Inganta Rayuwa na Ƙasa (NSIPs) na gwamnati mai ci yanzu.

Ana gudanar da shirin a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya a ƙarƙashin Minista Sadiya Umar Farouq.

Loading

Tags: Disaster Management and Social Developmentinganta rayuwamatasaMinistry of Humanitarian AffairsN-Power Batch CNational Social Investment ProgrammeSadiya Umar Farouqsamar da aikin yi
Previous Post

Cewar Adam A. Zango: Matasa mu riƙa kai zuciya nesa

Next Post

Dokar hana fim kan ta’asa: El-Hajeej, Alhaji Sheshe da TY Shaban sun bambanta a mahanga

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Daga hagu: Maje El-Hajeej, Alhaji Sheshe da TY Shaban

Dokar hana fim kan ta'asa: El-Hajeej, Alhaji Sheshe da TY Shaban sun bambanta a mahanga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!