• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Adam A. Zango: Matasa mu riƙa kai zuciya nesa

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
September 25, 2021
in Labarai
0
Adam A. Zango tare da 'yan jarida a lokacin firimiyar 'Ribar Duniya'

Adam A. Zango tare da 'yan jarida a lokacin firimiyar 'Ribar Duniya'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHAHARARREN jarumi kuma mawaƙi a masana’antar Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa rashin kai zuciya nesa da kau da ido har ma da rashin tawakkali ne ke sanya matasa faɗawa harkokin da ba su kamata ba a wannan zamani.

A cewar sa, matasan wannan zamani za su iya komai musamman idan su ka taso a cikin halin matsi wanda zai iya kai su ga samun ribar abokai wajen sanya su cikin wani hali na Allah-wadai.

Jarumin ya bayyana haka ne a daren jiya Alhamis, 24 ga Satumba, 2021 bayan wani taron nuna wani sabon fim mai suna ‘Ribar Duniya’ wanda aka shirya wa ‘yan jarida a gidan sinima na Platinum da ke Kano, kafin a fara haska fim ɗin a sinima.

Kamfanin shirya finafinai na ‘Shehu Media Entertaiment’ ne ya shirya fim ɗin.

Da ya ke jawabi ga manema labarai, Zango, wanda shi ne jarumin fim ɗin da ya fito a matsayin Sardauna, ya yi tsokaci musamman ga rayuwar matasa a yanzu.

A lokacin da ake haska fim ɗin a zauren sinimar

Ya ce, “Matashi a wannan lokaci zai taso ba shi da kuɗi kuma ba zai gode wa Allah ba, sai ya yi ta tunanin ta wace hanya zai bi domin ya ga ya samu kuɗi. 

“Matasan yanzu za su iya bin kowace hanya ta samun kuɗi kuma wannan dalilin ya sa ake samun mutane a cikin sana’o’i irin su damfara, kidinafin, sace-sace, kashe mutane, shiga ƙungiyar asiri da sauran su idan har mutum ba shi da tawakkali ko kuma bai yarda da Allah ne ya ke arziki ko ya ke hanawa ba. To idan mutum bai yarda da wannan ba, mutum zai iya faɗawa kowanne hali.”

Zango ya ba matasa shawara da cewa, “Duk wani matashi ya kamata ya nemi na kan sa, kar ya tsaya hangen wani wanda ya ke wucewa da motoci ko ya dinga hangen wani da ya ke riƙe manyan wayoyi ko hangen wani da kayan alfarma ya yi tunanin cewa shi ma gobe sai ya samu. Bai san yadda wannan mutumin ya yi ya mallaki waɗannan abubuwan ba. Ta yiwu ta hanyar da ya dace ne ko kuma ta akasin haka.

“Don haka matasa mu daina kallon wani mu ce za mu zama irin shi ba tare da mun dogara da Allah ba.”

Shugaban kamfanin da ya ɗauki nauyin wannan fim, Alhaji Shehu Mika’ilu Abdullahi, ya bayyana dalilin da sa ya shirya fim ɗin. Ya ce, “Ko da yake wannan  fim ɗin shi ne farkon aiki na, da man na daɗe ina ta tunanin ya za a yi na zo industiri. 

Wasu daga cikin jaruman shirin

“Kuma da man ina da sha’awar wannan aiki a Kannywood, to kuma Allah ya kawo wannan lokacin, don mun daɗe mun a shirya yadda za a yi mu shirya wannan fim ɗin, sai Allah ya kawo wannan lokacin.

“Kuma wannan shi ne aiki na na farko kuma ina da burin ci gaba da shirya wasu finafinan.

“Mun shirya wannan fim ne saboda yanayin abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummar mu. Mu na neman labari wanda zai wa’azantar da mutane yanzu, kuma abu ne yanzu da mutane ya kamata su guda kamar yadda rayuwa ta ke kasancewa a yanzu saboda in kun duba samari a yanzu irin manyan wayoyin da su ke riƙewa abin kai za su iya komai don su samu dukiya.

“To wannan fim ya na daga cikin abubuwan da ya kamata mutane su ga ne.”

Alhaji Shehu ya ce duk da yake shi sabon shiga ne a wannan masana’anta, ya samu wani ilimi a yayin ɗaukar fim ɗin, musamman ma yadda ake haƙuri da jama’a.

Ya ce, “Darasin da na samu yayin ɗaukar wannan fim shi ne haƙuri; kar mutum ya yi gaggawar yin wani abu. A dinga haƙuri saboda ba mu san yadda rayuwa za ta kasance ba.”

Ya kuma yi kira ga jama’a da su je su kalli wannan fim don irin darasin da ya zo da shi.

A taron, an ba ‘yan jarida da jaruman fim ɗin dama su fara kallon fim ɗin kafin a sake shi ga jama’ar gari don su bayyana gyara da shawarwari ga waɗanda su ka shirya shi.

‘Ribar Duniya’ fim ne da aka shirya don a tura wa masu kallo saƙo kan yadda duniya ta koma a yau inda mai dukiya ke samun abu cikin kwanciyar hankali in ya yi amfani da kuɗin sa, yayin da wanda bai da shi ba a ma kulawa da shi.

Fim ɗin ya kuma nuna irin illar yadda aka yi watsi da al’adar bincike kafin aure, musamman idan auren ya zo da abin duniya, da kuma nuna illar rabuwa da wanda ya kamata mace ta aura, wato wanda ya ke da dangi da aka san su, da sauran illolin da ya kamata Hausawa su duba don su gyara.

Ya ƙunshi jarumai irin su Adam A. Zango, Abdul M. Shareef, Fatima Hamisu, Rabi’u Rikadawa, Fati S.U., da sauran su.

Fostar ‘Ribar Duniya’ da aka kafe a jikin gidan sinimar

Malam Alhassan Toron Giwa ne ya rubuta labarin wannan fim kuma Alfazazee Muhammad ya bada umarni.

Tuni dai aka fara haska fim ɗin a gidan sinima na Platinum da ke birnin Kano.

Loading

Tags: Abdul M. ShareefAdam A. ZangoFati S.U. GarbaFatima Hamisuhausa filmsKannywoodmatasaPlatinum Cinema KanoRabi'u RikadawaRibar Duniya movieShehu Mika'ilu Abdullahi
Previous Post

Haramcin fim kan kidinafin da daba: Ba zan iya faɗa da gwamnati ba – Asase

Next Post

Gwamnati ta ƙara wa’adin aikin tantance masu cin moriyar shirin N-Power kashi na uku

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Gwamnati ta ƙara wa'adin aikin tantance masu cin moriyar shirin N-Power kashi na uku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!