DARAKTA-JANAR na Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta Nijeriya (NCC), Mista John Asein, ya bayyana cewa Gwammatin Tarayya ta fara aikin sake fasalin Dokar Haƙƙin Mallaka ta 1988.
Ya ce, “Gwamnatin Tarayya ta fara aiki babba na farko na sauya fasalin tsarin kare haƙƙin mallaka na ƙasar nan a cikin sama da shekara talatin.
“Hakan ya biyo bayan miƙa Ƙudirin Soke Dokar Haƙƙin Mallaka da Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC) ta yi ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da nufin sake ƙirƙiro ta a bisa doka.”
Asein ya faɗi hakan ne a cikin wata sanarwa da mujallar Fim ta gani a Abuja ran Talata.
A sanarwar, wadda Daraktan Hulɗa da Jama’a na hukumar, Mista Vincent Oyefeso, ya rattaba wa hannu, an ruwaito Asein ya na faɗin cewa manufar sabuwar dokar da za a yi ita ce a yi wa tsarin kare haƙƙin mallaka a Nijeriya garambawul.
Haka kuma a cikin abubuwan da dokar ta ke so ta cimmawa har da ƙarfafa aiki kan masu karya dokar ta hanyar tsaurara hukunci a kan su da kuma ƙarin nagartattun hanyoyi da su ka dace da zamanin yau na intanet, inji sanarwar.
Darakta-Janar ɗin ya tuno da cewa da ma can Majalistar Zartaswa ta Tarayya ta yi nazari tare da amincewa da kundin Ƙudirin (wato Bill) na dokar tun a taron ta na ranar 13 ga Yuni, 2018 (Ref. EC 2018), bayan da mai girma Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Malam Abubakar Malami SAN, ya gabatar mata da shi.
Ya ce: “Wasu daga cikin sababbin al’amuran da kundin Ƙudirin ya ƙunsa su ne: haƙƙin biya na wasu daga cikin gungun masu haƙƙin mallaka, bada tsamewa ta musamnan ga makafi da waɗanda ke da matsalar gani da kuma waɗanda ba su iya karanta rubutu.
“Sauran su ne: samar da dokar hana kauce wa kariyar sabbin hanyoyin fasaha, haƙƙoƙin gudanar da bayanai, cikakken tsarin aiwatar da doka kan masu karya doka a intanet da hukunci mai tsanani kan aikata laifin saɓa wa haƙƙin mallaka.”

Asein ya bayyana cewa Babban Ƙudirin kan Haƙƙin Mallaka ya ƙunshi tanade-tanade na tunkarar yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa dangane da haƙƙin mallaka waɗanda Nijeriya ba ta aiwatar ba.
Ya yi la’akari da cewa manyan burukan Ƙudirin su ne: “kare haƙƙoƙin maƙirƙira don a tabbatar sun amfana sosai kuma an san su ne ke da kayan su.
“Kuma za su samar da isassun iyakoki da damarmaki don tabbatar da ana yin amfani da ayyukan fasaha tare da bai wa Nijeriya damar bin yarjejeniyoyi, waɗanda ka taso a wasu muhimman tarurrukan haƙƙin mallaka.
“Sannan za a inganta ƙarfin Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka don ta zama mai tasirin yin doka, gudanarwa da aiwatar da doka.”
Bayan an ƙaddamar da cikakken tsarin garambawul ɗin tsarin haƙƙin mallaka na Nijeriya a cikin 2012, kuma a bisa kyawawan buƙatun jama’ar ƙasa, ya lura da cewar, kamar yadda aka saba a ko’ina a duniya, sai aka miƙa daftarin farko na Ƙudirin Haƙƙin Mallaka ga jama’a a cikin Fabrairu 2015.
Ya ce, “Bisa ga bayanan da masu ruwa da tsaki da kuma jama’a su ka yi, wani gungun masana ya yi wa daftarin gyare-gyare masu yawa kafin a miƙa shi ga Majalisar Zartaswa ta Tarayya domin ta duba ta kuma bada amincewa.
“Sabon Ƙudirin shi ne sakamakon aikin da aka shafe shekaru ana tuntuɓa, tare da masu ruwa da tsaki na cikin ƙasa da na ƙasashen waje, da ‘yan industiri, da ƙungiyoyin masu haƙƙi, da masana a harkar haƙƙin mallaka.
“Wannan Hukuma ta na kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da kuma abokan hulɗa da su bada goyon baya ga wannan aiki, kuma ta na fatan Ƙudirin zai samu kyakkyawar karɓa.”
Ita dai wannan hukuma ta NCC, an ƙirƙire ta ne a ƙarƙashin Sashe na 34 na Dokar Haƙƙin Mallaka (Cap C28, Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004). An fara ƙaddamar da ita da sunan Cibiyar Kare Haƙƙin Mallaka a ranar 19 ga Agusta, 1989, sannan a cikin Afrilu 1996 aka ɗaga darajar ta zuwa Hukuma sannan aka tabbatar mata da hakan a cikin Dokar Haƙƙin Mallaka (Gyararriya) ta 1999.
Hukumar ce ke da alhakin duk wasu al’amura da su ka danganci kare haƙƙin mallaka a Nijeriya, wanda ya haɗa da gudanarwa, yin doka, aiwatar da doka da kai ƙara a ƙarƙashin Dokar Haƙƙin Mallaka.