• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Kano ta haramta shirya fim kan kidinafin, shaye-shaye da ƙwacen waya

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
September 21, 2021
in Labarai
0
Alhaji Isma'il Na'abba (Afakallah)

Alhaji Isma'il Na'abba (Afakallah)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Jihar Kano ta haramta shiryawa ko nuna duk wani fim da aka yi shi a kan yadda ake garkuwa da mutane ko sayarwa da shan kayan maye ko ƙwacen waya. 

Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana wa mujallar Fim cewa an yi wannan dokar ne domin kare mutunci da tarbiyyar mutanen Jihar Kano.

Ya yi nuni da cewa ba waɗannan finafinan ake da buƙata ba a yanzu domin kuwa akwai labarai da dama waɗanda ya kamata masu shirya finafinai su maida hankali a kan su.

Afakallah ya ce, “Wannan doka an yi ta ne domin kare duk wani abu na mutunci da kuma tarbiyyar mutanen Jihar Kano, kuma da man can akwai wannan doka.

“Akasarin finafinan da ake shiryawa ana shirya su ne domin su faɗakar, su wa’azantar, to kuma idan aka kalli tsarin finafinan, wasu sun bauɗe daga hanya, an fara koya wa mutane maimakon su faɗakar sai su koyo munanan ɗabi’u. Wannan ya sa dole a tashi a ɗauki mataki.”

Shugaban ya faɗa da kakkausar murya cewa hukumar sa ta taka wa shirya irin waɗannan finafinan burki. 

Ya ce, “Mun taka burki da duk wani fim da za a shirya shi da za a nuna makamai a ciki saboda irin halin da mu ke ciki a yanzu domin daƙile yaƙi da ta’ammali da makamai a cikin al’umma.

“Hukumar Tace Finafinai ta hana dukkanin wani fim da za a yi wanda zai nuna hada-hada da kuma ta’ammali da ƙwayoyi ko sayar da su ko shan su. 

“Sannan bayan wannan da abubuwan da ake yi na garkuwa da ɗan’adam, yadda ake yi da kuma yadda abubuwan su ke kasancewa.”

Bugu da ƙari, Afakallah ya ce, “Shi kan sa nuna ƙwacen waya da ake yi a cikin fim da sauran su, shi ma mun taka masa burki.”

Ya ce duk waɗannan abubuwan ba su ya kamata yanzu masu sana’ar shirya fim su maida hankali a kan su ba, domin akwai abubuwa da yawa na labarai da za a ɗauka waɗanda za su taimaki al’umma, misali maganar ilimi da maganar hana barace-barace da ake yi da gararambar yara a kan titi, zaman kashe wando da tumasanci.

“Duk waɗannan abubuwan ya kamata a maida hankali wajen shawo kan su,” inji shi.

Shugaban ya ce, “Yanzu hukumar mu ta tace finafinai daga wannan karon duk wanda zai yi wani fim da zai nuna shaye-shaye ko safarar su ko kuma kidinafin ko fito da makamai ana harkar daba ko ana wani abu, wannan abin mun taka masa burki.”

Ya yi gargaɗin cewar duk wanda aka kama da yin irin wannan fim ɗin zai fuskanci fushin hukuma domin kuwa za su ɗauki matakin doka a kan sa.

A cewar sa, “Matuƙar mutum ya yi wannan fim ya kawo mana, hukumar mu ba za mu tace ba. Idan kuma ba mu tace ba, ba za ka saki ba. Ka ga ka kashe kuɗin ka a banza kenan. 

“Don haka idan za mu tace za mu ce ka cire wannan abin, idan kuma ba ka cire ba to ka yi laifi. In ka sake shi ba mu tace ba laifi ne, kuma a nan doka za ta yi aiki.

“Ko ka kawo a ciki an yi ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ko makamai ko garkuwa da ɗan’adam sai mu ce ka cire wannan abin. Shi ya sa tun kafin a yi mu ka tura wannan saƙon. Domin me? Domin a taka wa abin birki, kada ma mutum ya je ya fara ko ya je ya yi. 

“Saboda yanzu kamar abin ya karkata, mutane irin shi su ke yi, finafinan maimakon su hana abin sai su ke nuna kamar karantarwa su ke yadda za a yi abin. Don haka ba yadda za a yi hukuma ta zuba idanu a kan waɗannan abubuwan.”

A ƙarshen tattaunawar sa da mujallar Fim, Afakallah ya yi kira ga furodusoshi da daraktoci da su guji shirya irin waɗannan finafinan, ya na mai nanata cewa, “Kiran mu da masu shirya finafinai shi ne da su je su ɗauki fannin tattalin arziki, su yi finafinan da za su taimaka wajen gina rayuwar ɗan’adam da finafinan da za su taimaki lafiya da dukkanin al’amura.

“A bar waɗannan finafinan da mu ke da ƙalubale musamman a yankin nan namu na Arewa, na harkar garkuwa da ɗan’adam, na harkar shaye-shaye, na harkar wato dukkanin abubuwa na ta’ammali da makamai da ƙwace-ƙwacen wayoyi, duk waɗannan ba finafinan da su ke da muhimmancin ne a yanzu ba.

“Mu fito da abin da zai gina ɗan’adan da rayuwar sa da tattalin arzikin ƙasa. Wannan shi ne abin da ya kamata a yi.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa fito da wannan dokar da Afakallah ya yi ya na zuwa ne ƙasa da makwanni uku da hukumar yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, wato NDLEA, ta shirya taron bita tare da haɗin gwiwa da ‘yan masana’antar Kannywood inda aka gayyaci Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Haka kuma idan ba ku manta ba, ita ma Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta fito da doka kwanan nan inda ta hana shirya duk wani fim a kan harkar ta’addanci, wanda ya haɗa da kidinafin da hare-haren da ake kai wa ƙauyuka ana karkashe mutane sassan ƙasar nan.

Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: Censorship in Nigeriadrug abusegwamnatihausa filmsHukumar Tace Finafinai ta Jihar KanoKannywoodKanoKano State Censorship BoardkidinafinKidnappingshaye-shayeta'addanci
Previous Post

Babban alherin da na samu a Kannywood shi ne aure na da Maryam Sangandale – mawaƙi Abdul Kafinol

Next Post

Ali Nuhu: Ni da mahaifiya ta

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Ali Nuhu: 'Mahaifiya ta, Hajiya Fatima Kardiram Digirema, ta rasu a shekarar da na fara fim'

Ali Nuhu: Ni da mahaifiya ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!