HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai yi aikin gyara da kuma tsaftace masana’antar Kannywood.
A wajen rantsar da kwamitin da ya yi a ofishin sa ranar Juma’a, 29 ga Yuni, 2024 shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa manufar kafa kwamitin ita ce domin shiga lungu da saƙo na masana’antar domin tabbatar da kowa ya mallaki rijistar da ke nuna shaidar mutum cikakken ɗan masana’anta ne tare da tabbatar da masu shiryawa tare da ɗaukar nauyin finafinai sun bi dokar karɓar shaidar ɗaukar finafinai daga hannun hukumar (wato shooting permit).
Da yake bayyana waɗanda aka naɗa a matsayin wakilan kwamitin, El-Mustapha ya ce hukumar ta yi la’akari da ɓangarorin masana’antar daban-daban inda ta zaɓo mutane waɗanda su ne aka ɗora wa alhakin gudanar da wannan aikin. Su ne:
- Tijjani Abdullahi Asase (Actors Guild) – Ciyaman
- Ali Muhammad (KSCB) – Memba
- Aina’u Ade (Actors Guild) – Memba
- Aminu Muhammad Sabo (Actors Guild) – Memba
- Jazuli Labaran Gwale (KSCB) – Memba
- Abubakar Usaini Alaramma (Arewa Film Markers) – Memba
- Isma’il Khalil Ja’en (MOPPAN) – Sakatare

A lokacin da ya ke jawabin karɓar aikin da aka ba su a madadin ‘yan kwamitin, Tijjani Asase ya gode wa shugaban hukumar bisa la’akari da cancantar su ta zaɓo su domin yin aikin.
Daga nan ya roƙi ga hukumar da ta ba su cikakken haɗin kai da goyon baya ta yadda za su gudanar da aikin su cikin nasara.
Haka kuma ya sha alwashin gudanar da aikin su cikin ƙwarewa ba tare da tsoro ko nuna bambancin siyasa ba.
