BABBAN Sakataren Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ba da umarnin dakatar da gidajen kallo guda biyu a Jihar Kano nan take.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar kuma ya bayyana wa manema labarai.
Abdullahi ya ce, “Gidajen kallon da aka dakatar sun haɗa da Murtala Small Abba Hausa da Babbangida Entertainment da ke unguwar Sabon Gari a Kano.”
Ya bayyana cewa an samu duka gidajen kallon da rashin bin ƙa’idojin hukumar, inda ya jaddada ƙudirin ta na hukunta duk masu karya doka kamar yadda suka yi.
Idan ba ku manta ba, a ‘yan watannin da su ka gabata hukumar ta dakatar da wasu gidajen wasan kwaikwayo a jihar saboda rashin bin ƙa’idoji da dokokin da aka gindaya masu na tafiyar da harkokin su da kuma gurfanar da su a gaban ƙuliya bisa abin da su ka aikata na rashin aiki da su.