• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Finafinai 510 sun shiga gasar KILAF ta 2024

by MUKHTAR YAKUBU
September 24, 2024
in Labarai
0
Finafinai 510 sun shiga gasar KILAF ta 2024

Fostar gasar KILAF ta bana. A dama, Malam Muhammad Galadima

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FINAFINAI 510 ne suka samu shiga Gasar Baje-kolin Finafinai ta KILAF Awards ta bana.

Wannan ita ce gasa karo na bakwai da za a gudanar tun farkon fara taron a shekarar 2018.

Daraktan shirya taron KILAF Awards, Malam Muhammad Galadima, shi ne ya ba da sanarwar hakan a tattaunawar sa da mujallar Fim kan shirye-shiryen bikin na bana.

Galadima ya ce, “A bana sai dai mu ƙara godiya ga Allah a game da wannan gasar saboda ka ga wannan shi ne karo na bakwai da za a yi.

“Kuma a shekarar da ta gabata mun samu finafinai guda 50 daga ƙasashe 21 da suka shiga gasar, amma a bana wani abin mamaki a wannan shekarar kafin mu kai ga rufe karɓar finafinan a ƙarshen watan Agustan da ya gabata, mun samu finafinai da suka shiga gasar har guda 510 daga ƙasashe 54.

“Don haka wannan abin alfahari ne ga wannan gasar da kullum abin yake ƙara haɓaka.

“Kuma wani abu da zai ƙara ba ka mamaki a bana shi ne hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero ya bayar da dama ga duk wani ɗalibi da ya shirya fim da ya dace ya ajiye kuɗi dubu ɗari biyar za a bayar ga duk ɗalibin da ya shirya fim da ya dace a gasar a duk inda yake a duniya.

“To, ga wannan wani abu ne da ba a saba yi ba.

“Don haka a yanzu tsare-tsaren wannan biki ya yi nisa, za a bayar da dama masu ɗaukar nauyi su shigo sosai da sosai.

“Kuma a wannan shekarar kusan za a gabatar da kashi saba’in ba abubuwan da za a gudanar a cikin Jami’ar Bayero.

“Kamar kowace shekara akwai yawon buɗe ido ga baƙi da za su zo. Sai cin abinci da sarakuna kamar yadda aka saba yi a otal ɗin Tahir, da sauran abubuwa, yayin da kuma a wannan shekarar muna sa ran za a yi bikin ba da kyaututtuka a babban ɗakin taro na Gidan Gwamnatin Kano domin a samu damar shigowa a tsakanin gwamnati da mutane.

“To kuma abin da zai ba ka sha’awa game da wannan taron shi ne yana taimaka wa tattalin arzikin Jihar Kano, saboda idan baƙi suka shigo, dole sai sun sayi abubuwan da ake sayarwa a Kano da hawa mota, wanda hakan zai taimaka wa cigaban tattalin arzikin Jihar Kano da kuma samun kuɗin shigar ta.

“Don haka ya kamata a ce wannan abin wani abu ne ba wai Kannywood kawai ba, kamata ya yi a ce duk wani wanda yake kishin Hausa da Hausawa ya bayar da gudunmawa a duk inda yake a duniya, saboda magana ake ta assasa harsunan Afirika.

“To duk wanda ya yi fim a Afrika, ko da wanne yare ya yi shi, in dai na Afrika ne, ko da a wata ƙasa yake a cikin Turai, in dai fim ɗin da yaren Afrika ya yi, to KILAF ta na yi masa maraba.

“Don haka a yanzu mun tura finafinan ga alƙalan gasar, suna can suna aiki ba dare ba rana don ganin an samu sakamako mai kyau.

“A shekarar da ta gabata fim ɗin Zimbabwe shi ne ya kwashe kyaututtuka masu tsoka, to a bana mun zuba ido mu ga fim ɗin wace ƙasa ne zai samu nasara.

“Muna fatan za mu yi taron lafiya mu tashi lafiya cikin nasara.”

Loading

Tags: gasar finafinai ta AfirkaKILAF AwardsMuhammad Galadima
Previous Post

Gwamnatin Kano ta kulle gidajen kallo biyu saboda ƙin bin ƙa’idojin ta

Next Post

Yarjejeniyar Samoa: Gwamnatin Tarayya ta yaba da hukuncin NMCC kan rahoton bogi da jaridar Trust ta buga

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Yarjejeniyar Samoa: Gwamnatin Tarayya ta yaba da hukuncin NMCC kan rahoton bogi da jaridar Trust ta buga

Yarjejeniyar Samoa: Gwamnatin Tarayya ta yaba da hukuncin NMCC kan rahoton bogi da jaridar Trust ta buga

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!