INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa Hajiya Hauwa Hussaini rasuwa, wato mahaifiyar jarumi kuma mai ba da sutura a Kannywood, Umar Muhammad, wanda aka fi sani da Umar Big Show.
Hajiya Hauwa, mai kimanin shekara 53, ta rasu da misalin ƙarfe 11:00 na dare a jiya Laraba, 6 ga Satumba, 2023 a asibitin Nassarawa da ke Kano.
An faɗa wa mujallar Fim cewa bayan an sanar da Hajiya labarin wata rasuwa da aka yi ne sai gefen kan ta ya fara ciwo, daga nan aka garzaya da ita asibiti, inda ta rasu.
An yi mata sallah a gidan ta da ke Mariri da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Alhamis, 7 ga Satumba.
‘Yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Umar M. Shareef, Ado Gwanja, Hamisu Breaker, Yusuf Guyson, Horo Ɗan Mama, sa sauran su.
Umar Big Show shi ne na farko a cikin ‘ya’yan ta shida, maza uku, mata uku.
Allah ya jiƙan Hajiya Hauwa da rahama, amin.