GA dukkan waɗanda su ka yi yayin kallon dirama a gidan talbijin ba za su manta da matar Alhaji Buguzum ba a cikin shirin ‘Ƙuliya’ wadda sunan ta na gaskiya shi ne Hajiya Rakiya Ƙwaro.
Tsohuwar ‘yar fim ce tun ana wasan kwaikwayo na talbijin har ta zo ana damawa da ita a masana’antar Kannywood, wanda a nan ma ta bayar da gudunmawa sosai a fagen shirin fim.
To sai dai a yanzu tsufa ya riski Hajiya Rakiya, shekaru sun ja, babu ƙarfin yin aikin.
Ko da yake a yanzu ba tsufan nata ne ya zama matsala a gare ta ba, sai yanayi da kuma halin da ta ke ciki, domin kuwa Hajiya Rakiya Ƙwaro a yanzu ta shafe tsawon lokaci ta na fama da rashin lafiya, kuma ta sha kwanciya a asibiti idan ta samu sauƙi a dawo da ita gida.
A ziyarar da mujallar Fim ta kai mata gidan ta da ke Unguwa Uku a Kano, mun ɗan yi gajeriyar tattaunawa da ita inda ta bayyana mana halin da ta ke ciki.
A cikin tattaunawar, Hajiya Rakiya Ƙwaro ta ce, “Na daɗe ina fama da ciwon ƙafa da kuma sauran cutuka sakamakon ciwon suga da kuma hawan jini da na ke da shi.
“Amma dai a wannan lokacin ya fi takura mini, don na sha kwanciya a asibiti. Ko a yanzu ma ban fi sati da dawowa gida daga asibitin ba, kuma na shafe kwana goma sha bakwai a can asibitin ina kwance.
“Sai da na fara samun sauƙi aka dawo da ni gida.”
Ta ci gaba da cewa: “Yanayi na rashin lafiya ka san babu daɗi, musamman idan ya haɗa da tsufa. Don ko a yanzu ma da mu ke magana da kai don na ɗan samu sauƙi ne, amma da maganar ba za ta yiwu ba.”
Da mu ka tambaye ta ko ta na samun kulawa daga ‘yan fim, sai ta ce, “Ina samu, kamar a wajen Naziru Sarkin Waƙa da Isa Bello Ja da Abdulkareem Muhammad. Don shi Isa Bello Ja ya na zuwa duba ni lokaci-lokaci.”
A ƙarshe, mun tambaye ta ko akwai wani tallafi da ta ke buƙata a wajen jama’a, sai ta ce: “To ai shi mara lafiya mabuƙaci ne a kowane lokaci, musamman ma dai ni a matsayi na na marar ƙarfi. Don haka ina buƙatar addu’a ga jama’a da kuma duk wata gudunmawar da mutum ya ke ganin zai iya yi mini.
“Fatan mu dai shi ne Allah ya ba mu lafiya da kuma cikawa da imani.”
To amin, Hajiya.