‘YA’YAN haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, a jiya sun zaɓi Alhaji Hamisu Jibrin Goma a matsayin sabon shugaban su.
Ya kayar da Hajiya Fatima Ahmed Ibrahim (Lamaj), tsohuwar shugabar ƙungiyar wadda ta sauka kwanan nan bayan wa’adin farko na shekara huɗu.
An sha tirka-tirka kafin gudanar da zaɓen domin an shafe kusan wata biyu ana cacar baki game da zaɓen bayan ƙarewar wa’adin mulkin Lamaj.
Sakamakon ƙurar da ta tashi a tsakanin membobin ƙungiyar, kwamitin amintattu (BoT) na MOPPAN na ƙasa ya turo wakilin musamman, Alhaji Habibu Barde, tsohon shugaban MOPPAN na Abuja, don ya taimaka a yi abubuwan da su ka dace game da zaɓen.
A wurin taron da aka yi jiya don gudanar da zaɓen, an yi magana a kan sauran ƙungiyoyin masu shirya finafinai na jihar, wato ‘guilds’, waɗanda su ne da ma ke zaɓen shugabannin MOPPAN ɗin a matakin jiha, inda su kuma su ke zaɓen shugabannin MOPPAN a matakin ƙasa.
Waɗannan ƙungiyoyi su ne na daraktoci, furodusoshi, ‘yan wasa, marubuta, editoci, masu kyamara, mawaƙa da masu bada kayan sawa.
Wasu daga cikin shugabannin MOPPAN reshen jihar sun bada umarnin cewa waɗannan ƙungiyoyi su rushe shugabannin su su sake zaɓe tunda dukkan su sun wuce wa’adin mulkin su, somin akwai waɗanda su ka shafe shekara sama da takwas ba su sake yin zaɓe ba har zuwa yanzu.
A nan aka samu bambancin ra’ayi, inda wasu su ka nuna ba su yarda da wannan shiri ba, domin ƙungiyoyin da kan su ne ya kamata su shirya wa kan su zaɓe, ba MOPPAN.

A ƙarshe dai sai da maganar ta kai ga iyayen ƙungiya irin su Alhaji Abdullahi Maikano, Yakubu Lere da sauran su su ka kira taron gaggawa don a samu masalaha game da ɓarakar da aka samu.
Iyayen sun shawo kan matsalar ta hanyar bada wasu shawarwari, inda aka samu maslaha da matsaya, wanda shi ne har ya kawo wannan rana da aka gudanar da zaɓen.
Sai dai kuma a wannan karo tsuntsu biyu aka jefa da dutse ɗaya. Tun safiyar jiya aka sanar da ‘yan takara da membobi masu kaɗa ƙuri’a cewa za a gudanar da majalisi (congress) ne da kuma zaɓe.
Haka kuma aka yi, domin sai da aka fara gabatar da majalisin sannan aka yi zaɓen.
An bada sanarwar cewa za a fara majalisin ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe a wani ɗakin taro da ke Media Centre Services da ke Titin Independence, amma ba a fara ba sai wajen ƙarfe 12:57 na rana, inda uban taron, Habibu Barde, ya umarci darakta Saminu Mohammed Mahmud ya buɗe taron da addu’a.
Barde, tare da abokan aikin shi, wato shugaban kwamitin zaɓe Malam Ibrahim Tahir, sakataren kwamiti Rabi’u Koli da menba Hadiza Maina, sun jagoranci zaɓen daga farko har ƙarshe.
Bayan an buɗe taro da addu’a, Barde ya yi jawabi game da matsalolin da ke tattare da zaɓen MOPPAN na Kaduna. Ya ce, “Ni an turo ni ne don yin gaskiya, don haka ban san kowa ba, ni ba ɗan Kaduna ba ne.
“Kada wani ya yi tunanin ina goyon bayan wani, ni gaskiya kawai zan yi. Don haka ni dai ‘mandate’ ɗi na a yi zaɓe lafiya.”
Ya ƙara da cewa, “Tun ranar Alhamis na shigo Kaduna. Sai da na shigo garin na fahimci wani abu, domin an ce in ba ka san gari ba ka saurari daka, don haka ni na saurara.
“Saboda haka, shawara na su ‘guilds’ da su ke riƙo ba za su yi zaɓe ba, mu da mu ke a nan mu amince za mu yi zaɓen MOPPAN.”
A daidai nan, sai Adamu Bello Ability ya miƙe ya bada shawarar cewa dukkan shugabannin ‘guilds’ ɗin su fita waje, su zaɓi mutum biyar-biyar daga cikin su da za su yi zaɓen.
Shi ma Al-Amin Ciroma, a nasa jawabin, shawarar da ya bayar kenan, inda ya ce da ma shi ma abin da ke zuciyar sa kenan, amma “yayan sa” Ability ya hutar da shi ya faɗi abin da ya ke so ya faɗa.

An bada dama ga mahalarta su faɗi ra’ayin su kan zaɓen mutum biyar-biyar a cikin ‘guilds’ da kuma waɗanda ba su yarda ba.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su game da yadda za a gudanar da zaɓen, inda aka samu mutanen da su ka yarda su 97, mutum 9 kuma su ka ce ba su yarda ba.
An ɗauki maganar waɗanda su ka yi rinjaye, aka umarci kowa da ya fita daga cikin ɗakin taron. Daga can aka je aka yi sallar Azahar.
Kafin a koma taro, kowace ‘guild’ ta fitar da mutum biyar da za su kaɗa ƙuri’a.
Bayan an dawo, sai aka shiga fagen zaɓe. Habibu Barde ya karanto sunayen da aka ba shi daga kowace ‘guild’ don tabbatar da su a gaban jama’a.
Daga nan sai Malam Ibrahim Tahir, shugaban kwamitin zaɓen, ya bada dama ga ‘yan takara masu neman manyan muƙamai su gabatar da manufofin su na mintuna biyu-biyu. Sannan ya kira sunan dukkan ‘yan takarar da muƙaman da su ke nema, kuma ya karanto dukkan sharuɗɗan zaɓe da masu kaɗa ƙuri’a za su bi.
An fara kaɗa ƙuri’a da misalin ƙarfe 3:27 da wakilan ƙungiyar marubuta. Daga ita sai ta ‘yan wasa, sai ta furodusoshi, sai ta daraktoci, sai ta masu kyamara, sai ta mawaƙa, sai ta masu bada kayan sawa, sai kuma ƙungiyar editoci.
Da aka kammala zaɓen, Barde ya yi magana a kan zaɓen ‘guilds’, wanda da ma ba su amince MOPPAN ta yi masu zaɓe ba, ya ce ko an amince a yi zaɓen su yanzu?
Nan take aka nuna ba a yarda ba. Sai ya ce, “To tunda haka ne an ba shugabannin riƙon ƙwaryar ‘guilds’ ɗin da su je su yi zaɓe da kan su nan da wata ɗaya, kuma su dawo su sanar da majalisa cewa sun gudanar da zaɓuɓɓukan su.
“Don haka MOPPAN za su ba su dukkan kayan zaɓen da su ka tanadar masu.”
Daga nan sai aka buƙaci wakilan ‘yan takara da su je wurin da za a ƙirga ƙuri’un. An ƙirga baki ɗaya, an samu lalatattu guda biyu. Daga nan aka bayyana waɗanda su ka yi nasara a zaɓen, kamar haka:
Nasiru Ɗanmaliki – ƙuri’u – 49, Ruƙayya Usman – ƙuri’u 45,
Shebe Liman – 42
Maina Yusuf – 45
Umar Maijalingo – 45
Fatima George – 43
Dukkan waɗannan ba su da abokan hamayya. Ga inda zaɓe ya ke nan:
Abubakar Hunter – ƙuri’u 32
Yusuf Gidaje – 19
Zakara: Hunter
Dikko Yakubu – 37
Dakta A.S. Bello – 15
Zakara: Dikko
Sulaiman Sha’ani – 35
Murtala Aniya – 15
Zakara: Sha’ani
Hamisu Jibrin Goma – 39
Fatima Lamaj – 13
Zakara: Goma
Bayan an gama lissafawa, Lamaj ta nuna dattaku, inda ta karɓi faɗuwa, sannan kuma ta samu Goma ta taya shi murna.
Haka shi ma Aniya ya taya Sha’ani murna, har su ka ɗauki hoto tare.
An umarci lauya Jamilu Sulaiman ya rantsar da sababbin shugabannin nan take. Ya fara da sabon shugaba, Alhaji Hamisu Jibrin Goma. Daga bisani ya haɗe sauran baki yaɗa ya rantsar da su.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 7:00 na dare.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci taron su ne: Fatima Lamaj, Saminu Mohammed Mahmud, Musa Muhammad Abdullahi, Adamu Bello Ability, Rabi’u Rikadawa,Yahuza Ilu, Abubakar Muhammad, Yusuf Abubakar (JTF), Habibu Barde, Abdullahi Tasiri, Abdullahi Musa, Al-Amin Ciroma, Murtala Aniya, Jamilu Adamu Kocila, Isma’il Koli, Sabi’u Gidaje, Yusuf Gidaje, Haruna Gidaje, Nafi’u Gidaje, Garba Shehu PS, Uwaisu Abubakar, Buhari Zariya, Aminu Mirror, Umar Maijalingo, Nura MC, Abubakar Hunter, Ibrahim Tahir, Rabi’u Koli, Jamil Nafseen, Sagir Baban Kausar, Maina Yusuf, Zaharaddin Mando, A.A. Rasheed Kabala, Ibrahim Saminaka, Sulaiman Sha’ani, Danladiyo Mai Atamfa, Ibrahim Captain, Bilal Naseer, Abdul SD, Najib Marubuci, Ibrahim Saminaka, A’isha Umar Mahuta, A’isha NTA, A’isha Abubakar ZIAU, A’isha B. Umar, Hadiza Maina, Jamila Lasco da Ummi Hutu.

A tattaunawar sa da mujallar Fim a kan zaɓen, sabon shugaban, Alhaji Hamisu Jibril Goma, wanda mazaunin Birnin Zariya ne, ya bayyana irin farin cikin da ya tsinci kan sa a ciki dangane da nasarar da ya samu, ya ce, “Alhamdu lillahi. Wannan nasara babu abin da za mu ce sai mu yi wa Allah godiya, domin duk abin da Allah ke yi wa bawa ya yi mana wannan.
“Ba mu taɓa tsammanin za mu samu irin wannan nasara ba, ga shi sai Allah ya ba mu. Saboda haka mu na yi wa Allah godiya da kuma jama’a godiya da su ka ga mun cancanta da mu zauna a kan wannan kujera, domin sun hango abin da za mu iya taimaka masu. Kuma ina roƙon Allah ya ba mu ikon taimakawa.
“Kuma alhamdu lillah, abu na farko da za mu fara aiki a kai, akwai matsaloli da mu ka taras, don haka matsalolin nan ba za mu iya magance su mu kaɗai ba. Za mu kira ‘stakeholders’, za mu kira malaman addini za mu yi zama da su su ba mu shawara ta yaya za mu yi maganin wannan matsalar.
“Mu kaɗai ba za mu iya ba don matsalolin sun yi yawa, sai mun haɗa hannu ƙarfi da ƙarfe, mun fito da Jihar Kaduna ta koma yadda ta ke uwa mabada mama a wannan harka.
“Waɗanda su ka zaɓe ni ina yi masu godiya. Ina kuma kira a gare su don sun zaɓe ni kada kuma su ƙyale ni; idan akwai wasu kurakurai ko shawarwari ya kamata su ci gaba da ba mu, domin shekara biyu kamar gobe ne.
“Ina kuma roƙon Allah ya dafa mana, ya kuma ba mu nasara.”
Haka shi ma wakilin kwamitin amintattu na MOPPAN ta ƙasa, Alhaji Habibu Barde, ya tofa albarkacin bakin sa. Ya fara da cewa, “Suna Alhaji Habibu Barde. Ni ne tsohon shugaban MOPPAN na Abuja da na sauka kwanan nan, don zan tsaya takarar mataimakin shugaban MOPPAN na ƙasa.
“Ana cikin haka ne sai BoT ta MOPPAN ta ƙasa ta kira ni ta neme ni da na zo Kaduna na yi ƙoƙari na haɗa kan ‘yan MOPPAN da ‘guilds’ ɗin su da ‘stakeholders’ da ‘elders’, na yi ƙoƙari duk yadda zan yi in ga an yi zaɓen MOPPAN, an yi maganar gyara wa ‘guilds’ zama waɗanda su ka yi ‘overstay’.
“To gaskiya abin dai ‘is not easy’, domin kafin a ba ni akwai waɗanda aka ba su su ‘yan Kadunan ba su daidaita da su ba. Cikin ikon Allah ni da aka ba ni, na zo na haɗa kan su a yi haƙuri da duk surutan da ake ta yi. Mun zo mun haɗa wannan zaɓe, na nemi haɗin kan su.

“Kuma da ma akwai waɗanda mu ke zaman mutunci da su, aka samu aka yi abin nan cikin mutunci. Ka ga yanzu an sauya mulki, sun zaɓa wa kan su sababbin shugabanni, har an rantsar da su.
“Don haka babu abin da zan ce sai dai mu gode wa Allah da wannan nasara da ya ba mu.”
Jerin waɗanda su ka samu nasara da muƙaman su dai shi ne:
1. Hamisu Jibril Goma – Shugaba
2. Sulaiman Sha’ani – Mataimakin Shugaba
3. Dikko Yakubu – Sakatare
4. Fatima George – Mataimakiyar Sakatare
5. Umar Maijalingo – Sakataren Kuɗi
6. Shebe Liman – Mai Bincike
7. Maina Yusuf – Ma’aji
8. Ruƙayya Usman – Walwalar Jama’a
9. Abubakar Hunter – Sakataren Tsare-tsare
10. Nasiru Ɗanmaliki – Jami’in Yaɗa Labarai









