A YAU, shekarar 2019 ta zo ƙarshe. Gobe za mu shiga sabuwar shekarar 2020 da yardar Allah.
Shin yaya ‘yan fim su ka ga sana’ar su a cikin shekara mai shuɗewa? Ci-gaba aka samu ko ci-baya?
Mujallar Fim ta tuntuɓi mutum huɗu – ɗaya a ɓangaren gwamnati, ɗaya a ɓangaren masu shiryawa, biyu kuma a ɓangaren ‘yan wasa – kan yadda su ke ganin ya dace a yi domin a fitar da jaki daga duma a shekara mai kamawa ta 2020. Ga abin da su ke cewa:
1. ISMA’IL NA’ABBA (AFAKALLAHU)Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano:
“Alhamdu lillahi! Gaskiya an samu ci-gaba. Na farko dai a wannan shekarar ne Allah ya ba mu iko mu ka samar da ‘database’ na dukkanin masu ruwa da tsaki na harkar fim, kama daga masu bada umarni, masu shiryawa, ‘yan wasa, marubutan fim har zuwa masu tacewa.
“Bayan wannan, a wannan shekarar ne mu ka yaye ɗalibai da aka horas da su.
“Haka kuma a wannan shekarar ta 2019 mu ka samar da wani kwamiti wanda zai inganta kasuwancin finafinai, wanda zai inganta kasuwanci tsakanin ‘yan ‘downloading’ da masu shirya fim, wanda mu ka kirawo da ‘Kannywood Distribution Network’ a ƙarƙashin Sani Sule Katsina. Wannan shiri ya na da alaƙa kai-tsaye da masu gidajen kallo, masu ‘downloading’ da kuma sauran abubuwan da za su bunƙasa kasuwancin.
“Sannan a wannan shekarar ne mu ka gabatar da taron BON Awards, wanda aka yi tsakanin ‘yan Kudu da kuma ‘yan Arewa ta yadda za a bunƙasa sana’ar da yadda za a janyo ra’ayin mutane domin su saka hannun jari a masana’antar. Wannan shi ne a taƙaice.”
2. FATIMA IBRAHIM (LAMAJ)Shugabar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, MOPPAN, reshen Jihar Kaduna:
“Ba zan ce an samu ci-gaba ba, ba zan ce an ci baya ba. Domin kasuwar fim ma ta mutu ga baki ɗaya. Don ko ka zuba kuɗin ka ka yi fim ma ba ka da inda za ka je ka saida.
“Kuma mu a Kaduna ba mu da sinima, ballantana in ka yi fim za ka kai shi can ka nuna don ka samu kuɗi in ba a Kano ba. Kuma a Jihar Kanon ma za ka ga layi ya yi yawa, abin sai wane da wane, sai ka na da hanya sannan za ka samu ka nuna fim ɗin ka. Sannan ƙa’idojin ma su na da wahala wallahi. Kuma za ka ga yawancin kuɗin da ake samu ma na masu gidan kallon ne, domin mai fim zai ɗauki kashi 40, gidan kallo kashi 60; ka ga ko su ake nema wa kuɗin kenan. Kuma babu adalci a ciki kenan.
“Sannan kuma mu a nan Kaduna matsalar mu ƙungiyoyi sun yi yawa, sun kasu. Sun kasa haɗa kan su wuri guda ta yadda za a samu mafita mai kyau.
“Ana maganar MOPPAN. A ƙarƙashin MOPPAN kuma akwai ‘guilds’ guda bakwai. Ya kamata a ce mun haɗa kai don ciyar da masana’antar gaba.
“Yanzu harkar fim ta koma ‘online’, kuma wannan ma ci-gaba ne. Ni yanzu ‘distributor’ ce ta YouTube, akwai kamfanin da na ke yi wa ‘supplying’ finafinai ina samun kaso na a ciki.
“Amma in-sha Allahu cikin shekarar da za mu shiga za a samu sauye-sauye a Kannywood da zai kai ta mataki na gaba. Allah Ya taimake mu.”
3. RABI’U MOHAMMED RIKADAWA (DILA)Fitaccen jarumi:
“A baya an saba a yi fim a kai kasuwa ne, amma yanzu an koma sai dai a yi fim a nemi sinima a kai a nuna. Amma ka san yadda kowa ya ke fahimtar nashi ci-gaban. Kuma wani abu wanda ba a saba yin sa ba. Ci-bayan da aka samu wannan shekarar shi ne ba a samu yawan finafinai ba. Kuma kullum ana neman hanya ne da za a ɓulle.
“In ba ka manta ba, a lokacin da za a bar VHS za a koma CD da DVD, a kusan lokacin abin Maryam Hiyana ɗin nan, a lokacin ba a iya yin komai.
“Sai lokacin da su Aminu Saira su ka shigo Kaduna su ka yi wannan fim ɗin ‘Garin Mu Da Zafi’, sannan da aka buga aka gane kasuwar. Haka maganar siniman nan za a yi ta kokuwar yadda za a yi ya karɓu, wanda kuma bai sani ba za a tafi a bar shi.
“Amma kuma in ka yi abu mai kyau, akwai gidajen talbijin da za ka kai a saya, saboda haka wannan ci-gaba ne ba ƙarami ba. Amma sai mutum ya tsaya ya yi tsam da hankalin sa sannan zai iya fahimtar sa.
“In da ka saba ka yi fim ka miƙa kasuwa, yanzu ba haka abin ya ke ba. Misali, kamar mai ɗanwake ce, ta saba ta yi a cikin gida, sai aka ce ta kama shago, sai ta yi wasu abubuwa waɗanda za ta ga kamar abin da wahala. Amma in aka bi a hankali, kowa zai amfana.”
4. RAHAMA SADAUFitacciyar jaruma:
“Gaskiya babu maganar ci-gaba a masana’antar fim a wannan lokacin da mu ke ciki. Saboda idan ka duba gaba ɗaya idan furodusa ya yi fim a wuri ɗaya ya ke iya saida fim ɗin sa – siniman Kano.
“Mu na da jihohi 19 a Arewa, kuma duk su na kallon fim. A wani lissafi da aka yi, an fi kallon finafinan Hausa a kan na Kudu. Amma wannan kasuwar ta lalace, sinimar kawai ake iya kallon fim.
“Shin fim ɗin da ka yi ɗan Kano kawai ka yi ma wa? Ina sauran jihohin da su ma su na da buƙatar kallo?
“Idan ba ku manta ba, na yi ‘Rariya Tour’; in ka ga mutanen da su ka zo su ka kalla… mun je Yola, mun je Gombe duk mun nuna, amma saboda rashin gidajen kallon ba a kai masu finafinai.

“Yanzu sai dai ka yi fim kawai ɗan Kano ya kalla. Don haka ka gaya mani ta inda ci-gaba ya ke. Wanda a da kai ka san idan ka yi fim ka buga sidi da fim ɗaya sai ka yi kuɗi.
“Ban da yanzu, saboda kowa ja baya ya ke yi, babu wanda zai zuba kuɗin sa ya yi fim, kuɗin su ƙi fitowa.
“Kullum in mu ka zauna mu na magana, na kan ce dole sai mun haƙura mun tafi ‘digital’, kamar yadda duniya ta tafi.
“Idan ba za a yi ‘providing’ sinimu da yawa ba, a yi ko da guda biyar ne a garuruwan da aka san cewa sun fi kallon finafinan Hausa.
“Idan kuma ba za a yi wannan ba, sai dai mu tafi ‘digital’. Saboda duk furodusan da na haɗu da shi, sai na tambaye shi, ‘Ka na da dibidi a gidan ka?’ Bai da shi! Kowa a waya ya ke kallo. Sai a nemi hanyar da za a tafi ‘digital’ ɗin da ɗan kallo zai sa a wayar shi ya kalla. Wannan shi ne kaɗai mafita.
“In kuma ba za a iya wannan ba, gwamnati ta yi haƙuri, ta daure – saboda mu na biyan haraji, babu kamfanin da zai yi fim bai biya haraji ba; duk da ban dai sani ba, amma ni ina biya – a daure a gina mana sinimu ko da guda biyar ne a gani, a ce yau wancan ya saida dubu biyar a Kano, ana yi maka maganar miliyoyi ne.
“Wannan shi ne mafita, in ba shi ba sai dai a haƙura.”