HUKUMAR Hisbah ya Jihar Kano ta yi sulhu da masu gidajen kallo da wuraren shaƙatawa da kuma masu ɗakunan taro a faɗin jihar.
A yau Talata ne dai hukumar ta gana da shugabannin ƙungiyoyin su domin tattaunawa kan yadda za a samu daidaito a tsakani wajen gudanar da ayyukan su.
Babban Kwamandan Hisbah na jihar, Malam Haruna ibn Sina, ya ce, “Mu na fatan masu gidajen kallo da wuraren shaƙatawa su sanya Musulunci a cikin ayyukan su.”
Ya ƙara da cewa ba gaskiya ba ne labarin da ake yaɗawa cewar hukumar za ta rufe gidajen kallo ko wuraren shaƙatawa domin ba ta da hurumin yin haka.
Ibn Sina ya ce za su yi haɗin gwiwa da shugabannin ƙungiyoyin ta yadda za su riƙa yin aiki tare domin tabbatar da ba a keta dokokin Musulunci ba.
Manyan abubuwan da Hisbah ta ja hankalin ƙungiyoyin sun jaɗa da sanya idanu kan ƙananan yara waɗanda shekarun su ba su kai na girma ba da ke zuwa wuraren nasu, hana masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi shiga wuraren, da kuma batun zuwan ‘yanmata wuraren shaƙatawa barkatai.
Da ya ke mayar da jawabi a madadin ƙungiyoyin, Malam Murtala Tijjani ya yaba wa hukumar kan yadda ta nuna damuwa a gare su har ta gayyace su domin tattaunawa da su.
Idan mai karatu bai manta ba, mujallar Fim a baya-bayan nan ta kawo labarin cewa Hukumar Hisbah ta yi iƙirarin hana yin duk wani nau’in shagalin biki da dare, musamman ma fati wanda ta ce ya na hana ‘yan biki yin sallar magariba da isha.