HUKUMAR Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta na neman jaruma Umma Shehu domin ta je ta kare kan ta kan ƙazafin da ta yi wa hukumar a wani saƙon bidiyo da ta wallafa.
Babban kwamandan hukumar, Alhaji Harun Sani (Ibn Sina), shi ne ya faɗa wa BBC Hausa hakan.
A shekaranjiya dai Ummah, wadda ke da zama a Kaduna, ta wallafa bidiyon a Instagram inda ta kare Sayyada Sadiya Haruna kan kama ta da ‘yan Hisban su ka yi a kan tuhumar yaɗa baɗala ta hanyar soshiyal midiya.
A bidiyon, wanda ta ɗauka a lokacin da ta ke cikin tuƙa mota, Ummah ta yi iƙirari cikin ɓacin rai cewa su ma ‘yan Hisbah ɗin ai wasun su ma mazinata ne, amma ba a kula da su ba sai waɗanda aka raina.
Ta ce kama Sadiya Haruna shiga lamarin tsakanin bawa da mahaliccin sa ne kuma cin zarafi ne.
To amma saboda caa da aka yi mata da suka a soshiyal midiya, sai jarumar ta yi sauri ta goge bidiyon daga shafin ta.
Daga nan ta ci gaba da tura hotunan da ta ɗauka a shafin nata, ta yi fuska kawai kamar babu abin da ya faru.