HOTUNA sun ɓulla na yadda sabon Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya je gaban mahaifiyar sa ta sa albarka kan naɗa shi muƙami a gwamnati da aka yi.
A hotunan guda goma akwai inda ya duƙo kai, Hajiya ta shafa don sanya masa albarka a yayin da ya ke riƙe da jar hular sa mai ɗauke da rubutun laƙabin sa, wato “Abba Na Abba.” A wasu hotunan kuma ita da shi sun riƙe takardar naɗa shi wannan muƙami da gwamna ya yi.

Haka kuma a hotunan an ga jarumin da matar sa da ‘ya’yan su, cike da farin ciki su ma, sannan an gan shi tare da sauran ‘yan’uwa, kowa na taya shi murna da yi masa fatar alheri.
A ƙasan hotunan, El-Mustapha ya rubuta: “Abba ɗan Gwaggo… Sai godiya.”
Dubban mutane, ciki har da manyan ‘yan Kannywood, sun nuna son hotunan, kuma sama da 150 sun furta kalaman goyon baya tare da addu’a.


