MAWAƘI a Kannywood, Abdullahi Abubakar (Auta Waziri) da sahibar sa Halima Mustapha (Marmah) sun fitar da kyawawan hotunan kafin aure (pre-wedding pictures), kamar yadda sauran ‘yan fim da mawaƙa ke yi.
Mujallar Fim ta ba ku labarin za a ɗaura auren su a ranar Juma’a mai zuwa.
Da yake an ɗauki hotunan ne a kamfanin ɗaukar hoto na mawaƙin mai suna ‘Diamond Star’, an fitar da hotunan yadda ya kamata.
Abokan sana’ar mawaƙin suna ta raba hotunan a soshiyal midiya tare da yi masu fatan alkhairi.
Ga hotunan mun kawo maku domin ku kashe kwarkwatar ido.