* Ya ƙaryata masu iƙirarin samun riba a gidan sinima
SHUGABAN ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim ta ƙasa (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), reshen Jihar Kano, Alhaji Salisu Muhammad (Officer), ya alaƙanta mutuwar kasuwar finafinan Hausa da rashin goyon bayan da ya ce Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba ta ba ‘yan fim.
Officer ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da mujallar Fim a ofishin sa a Kano kan halin durƙushewa da Kannywood ta tsinci kan ta a ciki.
A cewar sa, hukumar tace finafinan ta na ɗaya daga cikin abiɓubuwan da ke yi wa ƙungiyar MOPPAN tarnaƙi wajen sha’anin gudanar da ayyukan ta.
Ya ce, “MOPPAN a yau ta ga dama idan ta zauna aka yi rubuce-rubuce kasuwancin kaset zai dawo, amma mu na da wani tarnaƙi guda ɗaya da mu ke fuskanta tsakanin ƙungiya da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, kuma wannan ita ce babbar matsalar da za mu samu tarnaƙi a kan dukkan abin da ƙungiya ta ɗauko, saboda akwai haƙƙi da ya wajaba wanda na shugabancin ƙungiya ne, akwai kuma haƙƙi da ya wajaba cewa na Hukumar Tace Finafinai ne. Idan kuwa ana samun wani abu na wannan ya shiga aikin wannan, to bai zama lallai a samu abin da ya kamata a ce an samu ba a masana’antar, sai dai a yi haƙuri har zuwa lokacin da za mu fuskanci juna mu da gwamnati, domin da zarar ka yi motsi za a ce ka raina abin da gwamnati ta ke yi ko kuma in ka yi wani yunƙuri ka nuna mata cewa wannan fa hurumi ne na ƙungiya ba hurumi ne ba na gwamnati ba, ba kuma hurumi ne na hukuma ba, to daga nan kuma ka faɗa wani tarko da ake so ka faɗa.”
Haka kuma ya yi nuni da cewa tun bayan ɗarewar sa kujerar shugaban riƙo na ƙungiyar, masana’antar Kannywood ta kasance wani kufai a fannin kasuwancin kaset, kuma ya danganta hakan da rashin gudanar da ayyuka na ƙwarai waɗanda al’umma ke da buƙata.
Officer ya ce: “Kamar yadda kowa ya sani, harkar saida fim ko kuma cinikayya ta finafinai sai dai addu’a, saboda hali ne wanda aka tsinci kai yanzu; jama’a za su ɓadda kuɗi su yi fim amma a rasa yadda za a yi da shi. Ba mutum ya kai kaset ba, zamani ya cinye kasuwar kaset. Ba a kai shi sinima ba, sinima kusan wacce ake shiga domin a yi kallo a Jihar Kano ƙwaya ɗaya ce. Ba kuma ka sa shi a YouTube ba, shi kan sa sai ka yi masa hidima ka ɗauki tsawon lokaci kafin ka fara cin gajiyar sa.
“Mun zo mun samu wannan harka duka a taɓarɓare, musamman a faɗin Jihar Kano.
“Duk wanda ya ce harkar fim ta na samun cigaba, to gaskiyar magana ya yi ƙarya, sai dai kawai a ci gaba da haƙuri.
“Sannan ana yaɗa ƙarya a kan ƙididdigar da ba gaskiya ba ce na cewa fim ya na sayuwa ko ana nuna shi a sinima. Mutum dubu nawa ake cewa sun shiga sinima wanda a ƙarshe za ka ga cewa duka akwai ƙarin bayanai wanda ba gaskiya ake faɗi ba a cikin irin wannan ƙididdigar da ake fitarwa.”
Officer ya ƙara da cewa, “Mun zo mun samu wannan yanayi wanda kuma ni a gani na dole ne sai mun yi wani abu, wato waiwaye adon tafiya, sai mun fara kallon menene maƙasudin mutuwar wannn kasuwanci na saida kaset, mu kalle su ɗaya bayan ɗaya tun daga fitar da sidi. Domin idan aka duba cewa maƙwabtan mu Inyamurai ko kuma ‘yan ‘Nigerian Film’, su na hadahadar kasuwancin fim ɗin kaset har zuwa wannan zamani. Abin abin a duba ne.”
Sai dai a daidai lokacin da ya ke wannan jawabai masana’antar na ganin cewa ta kama hanyar farfaɗowa daga wannan kwanciyar da ta yi, kamar yadda wasu daga cikin jarumai da masu shirya finafinai ke bugun ƙirji da bayyana YouTube a matsayin wata hanya da za ta iya dawo da martabar Kannywood.
To amma Officer ya bayyana YouTube a matsayin wata hanya da Bahaushe ke ce wa guntun gatarin ka, sannan kuma ya bayyana rashin ƙirƙira da sabunta basira da wasu mashirya finafinai su ka ɗauko a wannan tsari na YouTube na iya zamar musu wani shinge tsakanin su da masu kallo.
Ya ce, “YouTube wani abu ne wanda sai an yi haƙuri da shi.
“Kuma gaskiyar magana, har yanzu mu na da wata matsala guda ɗaya da ta dabaibaye mu mu masu shirya finafinai na kannywood. Har yanzu mun kasa yin wani aiki na a zo a gani.
“Shi YouTube a wajen mutanen mu sun ɗauke shi kamar wani bakin zare aka fara samarwa, amma yanzu kowa ya buɗe YouTube, sannan kowa ya na ɗora abin da ya ga dama har ma da abubuwan da bai dace ba, wanda yanzu ta kai ga cewa masu kallon mu sun fara ƙosawa a kan abubuwan da mu ke ɗorawa a kan tashar, abu ya fara zama kamar wasan yara.
“Duk da haka amma za ka ga yanzu ƙalilan ne a cikin mu da su ke yin aiki mai nagarta kuma su maida hankali a kan abin da su ke yi. Wannan ƙalubale ne a kan mu.
“YouTube kuma can da man sai ka raine shi kuma ya na ɗaukar tsawon lokaci kafin ka fara cin moriyar sa.
“Ya kamata mu yi wa kan mu adalci mu samu ƙungiya domin mu yi tsarin da zai ɗore, a kuma dafa wa ƙungiyar nan a ɗora ta kan gwadaben da za a dinga ayyuka masu ƙayatarwa da kuma burge mutane.”
A game da irin ƙudirin da MOPPAN reshen Jihar Kano ke son kawowa domin a dawo da martabar wannan masana’anta, Officer ya ce, “Yanzu haka mun samu damar zantawa da wasu bankuna domin su zo su sa mana hannayen jari wajen farfaɗo da sinimomin da mu ke da su a wannan jiha. Duk da cewa a arewacin ƙasar nan ba inda ya kai Kano sinima amma yanzu guda ɗaya ce tak mu ke kai kayan mu domin a kalla, wanda a da ba haka abin ya ke ba.
“Kan wannan dalili na lalacewar wasu daga cikin sinima ya sanya mu ka tashi tsaye domin haɗa kai tare da wasu bankuna da mu ke sa ran za su ba mu haɗin kai don cimma dawo da harkar mu ta finafinai.”
A ƙarshe, shugaban ya faɗi wasu daga cikin matsalolin da su ka dabaibaye Kannywood, inda ya kira su da hanyoyin da su ka hana masana’antar yin rawar gaban hantsi, wanda hakan ba ƙaramin tarnaƙi ya ke kawo wa masu son zuba jari a cikin masana’antar ba.
Wasu daga cikin ƙalubalen da ya zayyano sun haɗa da matsalar maimaita abu a cikin fim wanda ya ce “wani abu ne muhimmi wanda ya jawo wasu daga cikin masu kallon mu gajiya da abin da mu ke yi domin su.”
“Idan yau mutum ya yi fim wani sai ya ɗauki irin sa ya canza shi sai ya zama idan mace ce a wurin a wancan fim ɗin shi kuma sai ya sa namiji a wannan fim ɗin da aka kwaikwaya.
“Sannan babu ƙirƙira ko fiƙira a kan abubuwan da mu ke ƙoƙari mu ke ba wa mutane. Wannan shi ne babban abin da ya fara ɗauke zuciyar masu kallo daga abubuwan mu.
“Akwai harkar shugabanci. Waɗanda mu ke shugabanta ba su san menene haƙƙin mu a kan su ba, ba sa bibiya ba sa iya bada wani haƙƙin ko haraji da ya kamata su ba wa ƙungiya wanda abin nan ya wajaba a kan su.
“Ba kuma sa ba wa ƙungiya martaba ga shugabannin ta. In har ka ga mabiyi ya waiwayi cewa yau akwai shugabanci ko akwai ƙungiya, sai wani abu ya faru da shi wanda dole sai ƙungiya ta shiga sannan za ka ga ya waiwayi ƙungiya domin ta cire shi daga wannan haɗari da ya faɗa.
“Rashin haɗin kai na taka muhimmiyar rawa wajen durƙusar da wannan masana’anta ta yadda an kasa zama domin a yi tunani kan abubuwan da aka dawo da su tun daga baya domin a duba su a sabunta su domin gogayya da zamani. Yau idan ka ɗauki jarumi a wannan masana’antar, an dinga maimaita shi kenan har sai ɗan kallo ya ƙosa da ganin sa.
“Sannan inda ake shirya fim ɗin ma wuri guda ne sai dai kawai a canza labule ko zaman kujeru.
“Bugu da ƙari shi ne ɓangaren kasuwanci wanda mu na da buƙatar masu zuba hannun jari, amma saboda su masu zuba hannun jarin ba su samu gamsuwa a kan abin da za su zuba hannun jarin nasu a kai ba sun kasa zubawa, su na jin tsoro.
“Baya ga cewa wannan masana’anta ce mai ɗauke da ɗimbin arziki, amma an yi wasa da ita a hankali a hankali fiƙirar da Allah ya ba mu ta na gushewa mu na yin ƙasa, har ta kai ga abubuwa sun taɓarɓare har ya zamana ba ma iya gina wani abu da za a yi alfahari da shi.
“Bugu da ƙari, mu na fuskantar ƙulubale na rashin jari. Ba mu da jari, don duk wanda ka gani ya yi fim sai dai ko ya sayar da gonar sa ya sa kuɗin ya yi fim, wanda daga ƙarshe sai dai ka kunna a gidan ka ku na kallo kai da da iyalin ka.
“Duk da cewa wani lokacin sai dai mu ba wa gwamnati, amma ba ta taimaka mana wajen ganin an inganta wannan masana’anta.”