BABBAN Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya jaddda aniyar sa ta kawo tsafta da gyara a ɓangaren masu tallar maganin gargajiya, duba da yadda wasun su ke yaɗa kalaman batsa da hotunan da ba su dace ba da nufin tallata magungunan su don su ja hankalin masu saye.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya ambato sakataren, inda ya ce, “Shugabancin sa ba zai zuba wa wannan halayya ido ta ci gaba da faruwa a cikin al’umma ba saboda hakan ya saɓa da tarbiyar Jihar Kano tare da koyarwar addinin Musulunci.”
Babban sakataren ya yi wannan jawabi ne a gaban harabar hukumar sa jim kaɗan bayan kammala aikin kamen masu maganin gargajiyar da aka samu da laifin saɓa dokar hukumar a wani aikin haɗin gwiwa da ta gudanar tsakanin ta da ‘yan sanda.

El-Mustapha ya ci gaba da cewa, “Doka ce ta ba wa hukumar damar gudanar da wannan aiki. A don haka hukumar za ta yi wa dokar biyayya sau da ƙafa domin cimma nasarar da tasa a gaba.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa mako biyu da su ka gabata hukumar ta soke lasisin gudanar da aiki ga dukkan abokan hulɗar ta, inda tace har sai ta tantance su tare da ba su damar ci gaba da aiki, ciki kuwa har da ƙungiyar masu tallar maganin gargajiyar.
