HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar ta bayyana jin daɗin ta bisa yadda ɗakunan tarurruka da gidajen wasanni suke bin dokokin ta, musamman a yayin bukukuwan Babbar Sallah da ta gabata.
Kwamitin da ke da alhakin sa ido kan ayyukan waɗannan wuraren taro a lokacin Sallah ne ya tabbatar da cewa dukkan wuraren da suka sami damar kai ziyara sun cika ƙa’idojin da hukumar ta shimfiɗa a yayin bukukuwan Sallar.
Bayanin hakan ya fito ne daga shugaban kwamitin, Alhaji Lawan Hamisu Ɗanhassan, wanda shi ne daraktan da ke lura da sashen finafinai da cigaban sa a hukumar.
Alhaji Lawal ya ce: “Hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an ci gaba da bin doka da oda, tare da ɗaukar matakin da ya dace kan duk wanda ya karya doka ba tare da nuna sani ko sabo ba.”

Ya kuma buƙaci masu ɗakunan taro da gidajen wasanni a jihar da su ci gaba da bada haɗin kai domin tabbatar da kiyaye al’ada tare da tarbiyyar addinin Musulunci.
Ɗanhassan ya bayyana godiyar sa ga shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, bisa yarda da kafa kwamitin tare da ɗora masa alhakin sa ido tare da tabbatar da ɗa’a a tsakanin masu zuwa gidajen wasannin da ɗakunan taron da ke jihar.
Ya kuma yaba wa gwamnatin Jihar Kano bisa goyon bayan ta ga ayyukan hukumar tare da amsa buƙatun hukumar a kan lokaci.