HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta buƙaci ta gabatar da kasafin naira biliyan 305 ga Majalisar Tarayya domin yin zaɓen 2023 da kuɗaɗen.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya gabatar da kasafin ga Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattawa, a ranar Litinin.
Kwamitin ya gayyaci INEC da cewa ta sanya kasafin kuɗaɗen da za ta kashe wajen zaɓen 2023 a cikin kasafin kuɗaɗen ta na 2022 domin Majalisar Dattawa da ta Wakilai su yi nazarin kuɗaɗen kuma su amince.
A ranar Talata ne ake sa ran majalisun biyu za su rattaba amincewar su da adadin kuɗaɗen da za a kashe a lokacin zaɓen.
Haka nan kuma Farfesa Yakubu ya yi wa Kwamitin Kasafin Kuɗi bayani dalla-dalla cewa naira biliyan 305 ɗin daban su ke da naira biliyan 40 na kuɗaɗen kasafin shekara na ayyukan yau da kullum a hukumar.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa waɗannan naira biliyan 305 da hukumar ke nema, daban su ke da naira biliyan ɗin da INEC ɗin za ta kashe wajen ayyukan ofishin ta na cikin kasafin 2022.
Yakubu ya ce an rigaya an damƙa wa INEC naira biliyan 100 domin fara shirye-shirye, waɗanda ya ce adadin sun yi kaɗan a fara shirye-shiryen zaɓen 2023 da su.
“Mun damƙa masu kasafin naira biliyan 305 domin aikin zaɓen 2023 da su,” inji shi.
Bayanan kasafin dai ya ƙunshi shafuka 22.
Waɗancan naira biliyan 40 kuwa, kuɗaɗen ayyukan yau-da-kullum ne na ofishin INEC, ciki har da gudanar da zaɓukan da a kan gudanar ba lokacin ɗaya da babban zaɓe na ƙasa ba.
Ya ce, “Ya kamata wannan kwamiti ya sani cewa nan gaba akwai zaɓukan cike-gurabu har guda takwas, guda uku zaɓen ɗan Majalisar Tarayya ne, sauran biyar kuma na majalisar dokoki ta jihohi ne.”
Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe, Sanata Barau Jibrin, ya ce za a saka kuɗaɗen gudanar da zaɓen 2023 a cikin kasafin 2022.