• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta yi wa ƙungiyoyi 51 rajista don sa ido a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja

by DAGA WAKILIN MU
January 1, 2022
in Nijeriya
0
INEC ta yi wa ƙungiyoyi 51 rajista don sa ido a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wa wasu ƙungiyoyi su 51 rajista domin su sa ido kan zaɓen da za ta shirya a ƙananan hukumomin da ke Gundumar Birnin Tarayya (FCT) a ranar 12 ga Fabrairu, 2022.

A wata sanarwa da hukumar ta bayar a ranar Laraba a Abuja, ta bayyana cewa jerin sunayen ƙungiyoyi da ta amince da su ɗin sun haɗa da ƙungiyoyi 50 ‘yan ƙasa da kuma guda ɗaya daga ƙasar waje. 

A cewar sanarwar, ƙungiyoyin ‘yan  ƙasa da aka yi wa rajista sun haɗa da ‘Advocacy for Quality Leadership and Health Awareness Foundation’, ‘Africa for Millenium Change Initiative’, da ‘Centre for Democracy and Development’.

Akwai kuma ƙungiyar lauyoyi ta ‘Nigeria Bar Association’ da ‘Nigeria Civil Society Situation Room (Policy and Legal Advocacy Centre)’, yayin da ƙungiyar ‘yan ƙasar waje da aka yi wa rajista ita ce ‘International Foundation for Electoral Systems’.

Hukumar ta shawarci ƙungiyoyin da aka yi wa rajistar da su cike duk wasu takardu da ake buƙata ta hanyar yanar gizo a wannan gidan yanar: (http://observergroups.inecnigeria.org/) daga ranar 29 ga Disamba, 2021 zuwa ranar 13 ga Janairu, 2022.

Haka kuma hukumar ta nanata buƙatar da ke akwai ta ‘yan sa idon su kiyaye dukkan sharuɗɗan kare kai daga kamuwa da cutar korona (COVID–19) waɗanda INEC ta fito da su kan harkar zaɓe da kuma yi wa ‘yan sa ido rajista.

Wannan, inji INEC, ya haɗa da rattaba hannu kan wani fom na sahale wa hukumar da kuma bayar da kayan aiki na kare kai da ake kira ‘Personal Protective Equipment’ (PPE) ga dukkan masu aikin sa ido.

Ta yi gargaɗin cewa “duk wanda ya kasa bin sharuɗɗan za a soke rajistar sa ba tare da ɓata lokaci ba.”

INEC ta ce rarraba kayan aiki ga masu aikin sa ido ‘yan ƙasa (da su ka haɗa da katin shaida ga kowane mai sa ido) za a yi shi ne a ofishin ta da ke Abuja daga ranar 3 ga Fabrairu zuwa ranar 11 ga Fabrairu, 2022.

Loading

Tags: electionFCT Area CouncilsHukumar Zabe ta KasaIndependent National Electotal CommissionINEC
Previous Post

Cewar Hassan Giggs: Ba ni da abar so kamar Muhibbat

Next Post

Mansur Makeup zai angwance a ranar 8 ga Janairu

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
Mansur da Amina

Mansur Makeup zai angwance a ranar 8 ga Janairu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!