• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Hassan Giggs: Ba ni da abar so kamar Muhibbat

by DAGA IRO MAMMAN
January 1, 2022
in Ranar Murna
0
Hoton cika shekara 42 wanda Muhibbat Abdulsalam ta wallafa. Ɗiyar ta Aisha Humaira ce ta ɗau hoton

Hoton cika shekara 42 wanda Muhibbat Abdulsalam ta wallafa. Ɗiyar ta Aisha Humaira ce ta ɗau hoton

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN darakta a Kannywood, Hassan Giggs, ya sabunta shauƙin soyayyar sa ga matar sa, Muhibbat Abdulsalam, inda ya nuna cewa bai da kamar ta.

Giggs ya faɗi haka ne a saƙon taya murna ga matar tasa wadda ta cika shekara 42 da haihuwa a yau, 1 ga Janairu. 

A saƙon, wanda ya wallafa a soshiyal midiya kuma mujallar Fim ta fassaro, shugaban na kamfanin shirya finafinai na Giggs International, Kano, ya faɗa wa tsohuwar fitacciyar jarumar ta Kannywood cewa: “Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki, masoyiya ta. 

Hoton taya murna wanda Hassan Giggs ya wallafa tare da saƙon sa

“Kin cika shekaru 42 da haihuwa, amma har yanzu ki na kama da matashiyar da shekarun ta ba su kai hakan ba.”

Daga nan daraktan ya miƙa godiyar sa ga Allah, ya na faɗin: “A gaskiya ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba ni macen aure abar so kamar wannan, mace mai zuciyar zinari.

“Wata sa’a sai in riƙa tunanin wannan soyayya mai daɗi wadda ke saka ni amincewa da cewa lallai a rayuwa akwai soyayyar gaskiya.

Hassan da Muhibbat lokacin da su ka cika shekara 13 da aure a Yuni 2021

“Duk da yake ba lallai ba ne in kasance wanda ya fi kowa, amma na samu abin da ya fi kowanne. Kuma wannan labarin wannan soyayyar da ta fi kowacce, na soma tunani a kan sa, kuma sai ta ke kwararowa babu wani surki a cikin ta. Sai kalmomin su dinga tahowa tare da farin ciki mai cika zuciya da mace mafi dacewa.

“Barka da zagayowar ranar haihuwar ki, masoyiya ta.

“Uwar kyawawan ‘ya’ya na mata guda 3: Aisha, Fatima da Khadija.”

Saƙon na Giggs ya burge mutane sosai; kusan duk wanda ya karanta shi sai ya yaba.

Da yawa sun yi wa ma’auratan addu’ar fatan alheri.

Su dai su Giggs da Muhibbat, a watan Yuni 2021 ne su ka cika shekara 13 cur da aure.

Idan kun tuna, ba yau ba ne Giggs ya fara bayyana shauƙin so game da matar sa, kuma ya taɓa wa mujallar Fim cewa tun da su ke, Muhibbat ba ta taɓa yin yaji ko da sau ɗaya ba.

Hassan Giggs da Muhibbat tare da ‘ya’yan su a cikin Yuni 2021

Haka kuma ya taɓa faɗa wa wakilin mu cewa ba zai taɓa yi mata kishiya ba, kuma auren su na mutu-ka-raba ne.

Loading

Tags: aurebirthdayGiggs InternationalHassan Giggshausa filmsMuhibbat Abdulsalamzagayowar ranar haihuwa
Previous Post

Nafisa Abdullahi ta janye daga fitowa a ‘Labari Na’

Next Post

INEC ta yi wa ƙungiyoyi 51 rajista don sa ido a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
INEC ta yi wa ƙungiyoyi 51 rajista don sa ido a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja

INEC ta yi wa ƙungiyoyi 51 rajista don sa ido a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!