SAKAMAKON matsalar tsaro da ake fama da ita a Nijeriya, musamman a yankin Arewa, wata ƙungiya mai suna ‘Concerned Citizens for Development Initiative’ ta ɗauki nauyin shirya wani gajeren shirin fim mai suna ‘Ishara’.
A fim ɗin, an nuna muhimmancin miƙa lamari ga Allah a duk lokacin da al’umma su ke fuskantar wani bala’i ko masifa.
Haka kuma an ga yadda tsananin rashin tsaro tare da masifar hare-haren ‘yan bindiga su ka tilasta al’ummar wani Ƙauye yin gudun hijira zuwa wani guri na daban. Sai dai a kan hanyar su sai su ka haɗu da wani malami mai suna Malam Suwiɗi (Hussaini Sule Ƙoƙi), wanda ya tambayi ɗaya daga cikin matan dalilin su na ƙaurace wa garin su.
Bayan jin dalili daga bakin Kumbo (Hajara Usman) tare da Maigari (Mansur Kwaram), an nuno al’ummar wannan gari sun taru a ƙofar gidan Maigari, inda Malam Suwiɗi ya yi masu nasiha tare da jan hankalin su a kan duk inda mutum ya ke to babu shakka masifa za ta iya samun sa.
Haka kuma ya ja hankalin su da su gyara tsakanin su da Allah tare da mayar da al’amuran su ga Ubangiji domin samun dacewa tare da warwarewar dukkan al’amuran da su ka tsananta.
Bayan sa-in-sa daga mutanen wannan ƙauye tsakanin su da Malam Suwiɗi, a ƙarshe sun amince tare da karɓar nasihar sa, inda aka nuno su a cikin masallaci su na yin sallah tare da yin addu’a a kan matsalar tsaro da ta addabi al’umma.
Allah maji roƙon bawa, kwana ɗaya da yin wannan addu’a aka samu rashin fahimta tsakanin gungun ‘yan fashin dajin, inda hakan ya kai su ga hallaka junan su.

Darasin Shirin Fim Ɗin
Babban darasin da ke cikin wannan fim shi ne tunasarwa ita ta ke dawo wa da mutane hankalin su jikin su, idan masifa ta taso musu su nemi taimakon Allah.
Haka kuma wannan shirin ya na ƙara jan hankalin al’umma da su fauwala wa Ubangiji dukkan wani al’amari tare kuma da yin tuba na gaskiya.
Karɓar gaskiya a lokacin tsananin ko ƙuncin wata masifa, domin idan hankali ya ɓata to tabbas hankali ne ke dawo da shi.
Haka kuma shirin ya na ƙara koyar da haɗin kai tare da amfanin sa a tsakanin al’umma.
Sai kuma muhimmanci da tasirin addu’a a lokacin tsanani da sauƙi, domin shi Allah maji roƙon bawan sa ne.
Al’umma Na Da Rawar Takawa:
Dole mutane a koma ga Allah domin tuba da neman kawo ƙarshen wannan dambarwa da ta ƙi ci ta ƙi cinye wa. A guji tsine wa shugabanni; maimakon haka, a riƙa taya su da addu’a.
Al’umma ta guji raina abubuwan da ke faruwa domin toshe kafafen ɓarna da ka iya kunno kai;
Su waye su ka taka rawa a cikin shirin?
Fitattun jaruman masana’antar Kannywood irin su Hussaini Sule Ƙoƙi da Hajara Usman da Sulaiman Yahaya Bosho da Sharu Mustapha Naburaska. Sauran su ne Jamila Umar Nagudu da Hadiza Mohammed Sani (Kabara) da Aminu Ari Baba da Mansoor Kwaram da Yusuf Baban Chinedu da Tsalha Ɗanɗano da kuma Ɗan’azumi Baba Chediyar ‘Yangurasa (Kamaye).
Haƙiƙa wannan gajeren fim na ‘Ishara’ ya yi matuƙar isar da saƙo tare da bayar da darussa masu yawa, kuma tabbas saƙon zai ƙara taimakawa wajen canza wa al’umma tunani a kan matsalar tsaro da ake fama da ita a sassan arewacin Nijeriya.
