ALLAH ya yi wa mahaifiyar fitaccen mawaƙi, gwanin rawa kuma jarumi a Kannywood, Yusha’u Ahmad, wanda aka fi sani da Ishe Baba, rasuwa.
Hajiya Hafsa, mai kimanin shekara sittin da wani abu, ta rasu jiya Juma’a, 30 ga Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 4:00 na asuba a gidan ta da ke Nassarawa, kusa da Duala Police Station, a Jos, Jihar Filato, bayan ta yi fama da doguwar jinya ta tsawon shekara uku da wata bakwai.
An yi mata sallah a gidan ta.

‘Yan fim da su ka je masa ta’aziyya sun haɗa da ‘ya’yan ƙungiyar MOPPAN na Jihar Filato, Fahardi Ɗan Mama, Y.S. Malam, da sauran abokan sana’ar sa.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Ishe Baba shi ne na bakwai a cikin ‘ya’yan ta.
Allah ya jiƙan Hajiya Hafsa da rahama, amin.