JAGORAR Matan jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna, Hajiya Maryam Suleiman, ta bayyana cewa ta dawo daga rakiyar tsohon gwamna Malam Nasir El-Rufai, ta ce barin jam’iyyar da ya yi babban kuskure ne.
Maryam, wadda ta hannun damar El-Rufa’i ce a da, an dakatar da ita daga APC kwanan baya saboda sukar Gwamna Uba Sani da ta yi. Ta ce yanzu ta yi nadama, kuma tana ba shi haƙuri.
A cewar ta, abin da ta aikata yarinta ce, amma Uba Sani mutum ne mai jinƙai kuma ya yafe mata.
Ta ce ba ta fahimci abubuwan da suka jawo ta soki Uba ba, “amma bayan na gane kuskure na, sai na ba shi haƙuri,” inji ta.
Ta ce: ‘’Na faɗa masa cewa abin da na yi yarinta ce kuma a gaskiya ban fahimci abubuwan ba ne. Kowa ya san cewa ni mai sadaukarwa ce ga jam’iyya. Na gane kurakurai na kuma na gyara.”
Laƙabin Hajiya Maryam a da shi ne ‘Maryam Mai Rusau’ saboda alaƙar ta da El-Rufa’i, to amma yanzu tana kiran kan ta ne da ‘Maryam Mai Ginau’ domin nuna sabuwar alaƙar ta da gwamnatin Uba Sani.
Jagorar Matan ta ce gwamnatin El-Rufa’i ta tafka kurakurai da yawa, musamman wajen rushe kasuwanni da kuma korar malaman makarantun firamare.
Ta ce: “A gaskiya, mutane sun yi kukan waɗannan shirye-shiryen kuma an cuci jama’ar da abin ya shafa. Wasu ma sun rasa ran su. Hanyar cin abincin wasu ta toshe.
‘’Idan an kwatanta da Gwamna Uba Sani kuwa, za a ga shi mai tausayi ne. Mutum ne mai son ya taimaki mutane ko da bai san su ba. Akwai ɗimbin bambanci tsakanin sa da tsohon gwamna.”
Hajiya Maryam ta ƙara da cewa ta san Uba Sani tsawon lokaci tun kafin ya zama Sanata. Ta ce: ‘’Na riga Malam Nasir El-Rufa’i sanin shi. Mutum ne mai kirki wanda a ko yaushe yana neman yadda zai kyautata rayuwar talakawa.’’
Jagorar Matan ta ce babu wani tasiri da SDP za ta yi domin yanzu take koyon ta-ta-ta a fagen siyasa kuma ba a gama sanin ta ba.
“Ba zan taɓa komawa waccan jam’iyyar ba saboda ni cikakkiyar ‘yar APC ce,” inji ta.