• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jami’a a ƙasar Togo ta ba furodusan Kannywood Abdul Amart digirin girmamawa

by DAGA MUKHTAR YAKUBU DA ABBA MUHAMMAD
November 13, 2022
in Labarai
0
Bikin ba da digirin dakta ga Abdul Amart a Jami'ar IHIRIS, a Lomé

Bikin ba da digirin dakta ga Abdul Amart a Jami'ar IHIRIS, a Lomé

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA jami’a mai zaman kan ta a ƙasar Togo ta bai wa furodusa a masana’antar finafinai ta Kannywood Abdulrahman Mohammed (Abdul Amart Maikwashewa) digirin girmamawa na dakta.

Jami’ar, mai suna IHIRIS University, ta ba shi digirin ne a wani taro da ta gudanar a muhallin ta a jiya Asabar, 12 ga Nuwamba, 2022.

Sanarwar karramawar, wadda mujallar Fim ta gani, ta ce jami’ar ta karrama Abdul ne sakamakon bibiyar ayyukan sa da ta yi na tsawon shekara 10 inda ta gano cewa shi mutum ne mai son cigaban jama’a, wanda hakan ya sa jama’a da dama su ke ƙaruwa ta hanyar gudunmawar da ya ke ba su, don haka a matsayin sa na mai ciyar da al’umma gaba ta hanyoyin sama musu abin yi da kuma yadda za su dogara da kan su.

Ta ce sgi ne dalilin ba shi digirin domin ya ƙara himma wajen abin da ya sa a gaba.

Tuni dai Abdul Amart ya dawo gida da yammacin wannan rana ta Lahadi.

Abdul Amart, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ‘YBN Network Group’, ya yi addu’ar Allah ya sa wannan digiri da aka ba shi ya amfane shi da kuma duniya baki ɗaya.

Ya yi wannan addu’ar ne a yau Lahadi lokacin da ya ɗora hotunan ba shi digirin a Instagram, ya kuma yi rubutu da Turanci ya ce, “On the 12th of Nov, 2022, I was honored by the IHERIS University Togo, with a doctor of philosophy in Diplomacy and Public Management. It is indeed a great honor and as such I will like to thank the management of IHERIS university for this great honor. May Allah almighty make it useful for me and the entire Universe.”

Mujallar Fim ta fassara rubutun da cewa: “Ran 12 ga Nuwamba, 2022, an karrama ni a IHIRIS University, Togo, da digirin girmamawa a ‘Philosophy In Diplomacy and Public Management’. Lallai wannan babbar girmamawa ce, saboda haka zan so in gode wa hukumar gudanarwa ta IHERIS University a kan wannan babbar karramawa. Allah ya sa ta amfane ni da duniya baki ɗaya.”

A yanzu Abdul Amart ya bi sahun su Ali Nuhu, Aminu Ladan Abubakar (ALA) wajen samun digirin girmamawa na dakta.

Ɗimbin ‘yan fim da sauran jama’a sun taya Abdul Amart murna kan wannan abin farin ciki da ya samu.

Ƙungiyar ‘Kannywood Foundation’, wato Gidauniyar Kannywood, ta taya shi murna.

Takardar shaidar digirin dakta da Jami’ar IHIRIS Togo ta ba babban furodusa Abdul Amart a birnin Lomé

Kakakin ƙungiyar, Alhaji Mohammed Kabiru Maikaba, ya ba da sanarwa cewa: “A madadin shugabancin majalisar ƙoli ta dattawan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, wato ‘Kannywood Foundation’, na matuƙar farin cikin taya ɗan’uwan mu, Dr. Abdul Muhammed Amart (Maikwashewa) murnar samun wannan ɗaukaka ta samun babbar lambar yabo ta digirin digirgir, wato Doctorate Degree’.

“Hakika dukkan mu a wannan majalisa mun cika da farin cikin samun wannan labari. Sabili da haka, kafatanin shugabanci da ‘ya’yan wannan majalisa na farin cikin taya ka murnar samun wannan zinariyar lamba. 

“Babu shakka wannan jami’a ta cancanci yabo don kuwa ta yi wannan abin alheri a gurin da ya dace, don kuwa ta ajiye ƙwarya a gurbin ta. Kuma duk ɗan wannan masana’anta mai albarka ya sani kuma ya ji irin taimako da tallafi da kuma irin gudunmawar da ka ke ba wa ‘ya’yan wannan masana’anta, ‘yan’uwa da dangi da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya. 

“Babu shakka mutum mai irin zuciyar ka, mutum mai manufar kawo wa al’umma cigaba, ba zai taɓe ba, don haka ba zai ci tuwon sa gaya ba. 

“Irin wa’annan manufofi Allah Ubangiji ya duba ya ce wa mala’iku su yabe ka, shi ya sa ka fara ganin sakamakon tun a duniya. 

“Dakta! Baki ɗayan mu ‘yan wannan majalisa mu nai maka addu’a Allah ya ci gaba da riƙo da hannun ka. Allah yai maka albarka, ya yi wa zuri’a albarka, ya jiƙan magabata. Allah ya sa wannan cigaba da ka ke samu ya sa danshin sa ya kai ga duk ɗan wannan masana’anta. Allah ya sa wannan yauƙi ya yauƙaƙa ya zuwa duk wani loko da saƙo na wannan masana’anta. Amin. Kafatanin ‘yan wannan majalisa nai maka fatan alheri. Alhamdu lillah.”

Loading

Tags: Abdul Amart MaikwashewaAli NuhuAminu Aladigirgirdigirin girmamawaIHIRIS UniversityKabiru MaikabaKannywood FoundationYBN Network Group
Previous Post

Rikicin PDP: Na amince da tayin sulhun da su Wike su ka yi, inji Atiku

Next Post

INEC da hukumomin tsaro sun yi taron gaggawa don hana ci gaba da cinna wa ofisoshin hukumar wuta

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Hagu zuwa dama: Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya); Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, da Sufeto-Janar na 'Yansanda, Alhaji Usman Alƙali, a taron gaggawar

INEC da hukumomin tsaro sun yi taron gaggawa don hana ci gaba da cinna wa ofisoshin hukumar wuta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!