JAMI’AN hukumar tsaro ta asirce, wato DSS, sun bindige wani mutum tare da kama wani guda ɗaya daga cikin kidinafas ɗin da ake kyautata zaton su ne suka sace mahaifiyar fitaccen mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) suka yi garkuwa da ita.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda ɓarayin suka sace Hajiya Hauwa’u Adamu a gidan su da ke garin Kahutu a Ƙaramar Hukumar Ɗanja cikin Jihar Katsina, suka gudu da ita a daren Juma’a, 28 ga Yuni, 2024.
Ɓarayin sun buƙaci a biya diyyar naira miliyan ɗari tara (N900,000,000).
Sai da Hajiya ta shafe tsawon kwana ashirin kafin su sako ta.
Jaridar Daily Trust a yau ta ruwaito wata majiya mai ƙarfi da ta ce an ƙwato zunzurutun kuɗi har naira miliyan ashirin da shida da rabi a hannun ɓarayin a lokacin ceto gyatumar ta Rarara.
Majiyar ta ce wata rundunar binciken musamman ta ‘yan sanda daga Kano ce ta kai wa gungun ɓarayin su biyar samame a dajin Maƙarfi da ke Jihar Kaduna a daidai lokacin da suke raba kuɗin ganima.
Jaridar ta ce ‘yan sandan sun kai harin ne bayan an ba su bayanan sirri game da gungun ɓarayin.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Yanzu haka akwai wani mai suna Hamisu Tukur da ke tsare a hannun hukuma, tare da raunukan harbi a jikin sa, sannan an kashe wani mai suna Bature.”