• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jaridar Daily Trust ta saba buga ‘rahotannin ƙarya’, inji Gwamnatin Tarayya

by WAKILIN MU
July 6, 2024
in Nijeriya
0
Jaridar Daily Trust ta saba buga ‘rahotannin ƙarya’, inji Gwamnatin Tarayya

Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta bayyana cewa jaridar Daily Trust ta saba yaɗa abin da ta kira da “rahotannin ƙarya”.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya yi maganar a taron da ya yi da manema labarai a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja a ranar Asabar.

Ya yi jawabi ne sakamakon hayaniyar da ta tashi bayan jaridar ta buga labari cewa gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu a ƙasar Samoa kan wata yarjejeniya da za ta ba ‘yan luwaɗi da masu maɗigo cikakken ‘yanci a ƙasar nan.

Labarin ya harzuka jama’a tare da haifar da suka kan gwamnatin Tinubu.

A taron, Minista Idris ya ce gwamnati mai ci yanzu tana mutunta ‘yancin faɗin albarkacin baki da suka mai ma’ana to amma ta damu da “rahotannin ƙarya” da ke fitowa daga Daily Trust.

Ya ce: “Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnati ce mai kyautata alaƙa da kafafen yaɗa labarai. Hakan ya yi daidai da aƙidar Shugaban Ƙasa a matsayin sa na wanda ya daɗe yana gwagwarmayar tabbatar da dimokiraɗiyya da ‘yancin ɗan’adam.”

Idris ya yi nuni da cewa gwamnati ta ba kafafen yaɗa labarai damar su yi suka da kuma kare ‘yancin faɗin albarkacin baki ga jama’a.

Ya ce, “Amma abin baƙin ciki ne yadda wasu mutane suke wasa da wannan kyakkyawan yanayin wanda gwamnati ta tanadar. Mun yi matuƙar mamakin yawan aikin jarida da kuma kalamai na ganganci da wasu gidajen watsa labarai da mutane suke yi waɗanda suna da illa ga tsaron ƙasa.

“A cikin ‘yan watannin nan da suka gabata Daily Trust ta riƙa buga munanan labarai masu tada hankalin jama’a waɗanda ba wani abu ba ne illa ƙoƙari da gangan na yin ɓatanci ga gwamnati.

“A lokuta da dama mun yi ƙoƙarin ƙin yarda da cewa haka ɗin ne to amma yadda ake ci gaba da buga irin waɗannan labaran babu ƙaƙƙautawa tilas mu yarda da cewa haka ɗin ne.”

Ministan ya lissafa wasu rahotannin na Daily Trust waɗanda ya ce duk na ƙanzon kurege ne.

Ya ce: “Lokacin da aka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, Daily Trust ta riƙa buga labaran ƙarya cewa wai Gwamnatin Tarayya ta na cusa ƙasar nan cikin yaƙi, ta na murɗa labarin a kaikaice don tada hankalin jama’ar wani yanki domin ta haifar da rashin jituwa.

“Ita wannan jaridar ta buga wani babban kanu na labarin ƙanzon kurege cewa wai gwamnati ta na ƙoƙarin kafa sansanonin sojin ƙasashen waje a cikin ƙasar nan. Ita Daily Trust da waɗanda su ka haifar mata da labarin ba su kawo guntuwar shaida ko ɗaya ba don kafa hujja.

“Sannan mako biyu kacal da suka gabata, Daily Trust ta ƙirƙiri wani labari tare da yaɗa shi wai Gwamnatin Tarayya ta sauya sunan Titin Murtala Muhammed da ke Abuja zuwa Titin Wole Soyinka.

“A dukkan waɗannan lokuta jaridar ta dogara da ƙarya da ji-ta-ji-ta ne. Kuma ba su nuna nadama ko kunya ba su ba da haƙuri kan labaran.

“Amma ba mu taɓa tunanin cewa Daily Trust da masu buga ta za su zubar da ƙimar su har su yi gangancin yin ƙoƙarin jefa ƙasar nan cikin bala’i ba ta hanyar buga zargin ƙarya cewar gwamnati ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta ɗaure wa ‘yan luwaɗi da masu maɗigo gindi ba.

“A ganin mu, wannan abin kunya da rashin imani ne domin kuwa babu wannan zancen a cikin takardun da aka sanya wa hannu.

“Abin mamaki, jaridar ba ta ba da wata shaida ba ko ta kawo yarjejeniyar da ta ce an rattaba wa hannu domin kafa hujja.

“Abin baƙin ciki ne a ce labarin maras tushe kuma mai tayar da hankali shi ne wasu limamai suka yi amfani da shi a huɗubar su bayan an yaudare su da labarin, wanda hakan ya ƙara tunzura jama’a.”

Idris ya ce duk da waɗannan al’amurran, gwamnati za ta bi doka kuma ba za ta ɗauki tsauraran matakai ba.

Ya ce: “Gwamnatocin da suka shuɗe sun rufe gidajen kafafen yaɗa labarai kan abubuwan da ba su kai wannan muni ba, amma mu za mu bi abin a hankali kuma bisa doka.”

Idris ya bayyana cewa gwamnati za ta kai maganar ga Ƙungiyar Mamallaka Gidajen Jaridu ta Nijeriya (NPAN) tare da shigar da ƙara.

Ya ce: “Gwamnatin Tarayya tana goyon bayan kafafen yaɗa labarai masu ɗa’a da faɗin albarkacin baki amma ba za ta amince da labaran ƙarya da ke cutar da zaman lafiya da tsaron ƙasa ba.”

Idris ya halarci taron manema labaran ne tare da Ministan Kasafin Kuɗi Da Tsare-tsaren Ƙasa wanda ya yi ƙarin haske kan yarjejeniyar ta Samoa.

Loading

Tags: Daily Trustlabaran ƙaryaMohammed IdrisYarjejeniyar Samoa
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yi ta’aziyyar rasuwar Zainab matar Mataimakin Gwamnan Neja

Next Post

Mawaƙiya Zainab A. Baba ta yi aure

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
Mawaƙiya Zainab A. Baba ta yi aure

Mawaƙiya Zainab A. Baba ta yi aure

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!