JIBI Laraba jaruma kuma furodusa a Kannywood, Hajiya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya) za ta ƙaddamar da wani katafaren kamfanin turaruka da kwalliya a Kano mai suna ‘DY Ultra 85’.
A sanarwar da ta fitar kan taron da za a yi, Dawayya ta miƙa saƙon gayyata ga dukkan masoyan ta da abokan sana’ar ta zuwa wurin bikin.

Za a yi bikin ƙaddamar da kamfanin da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a lamba 16A, Titin Guda Abdullahi, Farm Centre, kusa da Asibitin Annury.
Babu ‘African time’, kamar yadda aka sanar a jikin katin gayyatar.