TSOHON jarumin Kannywood, Aminu Ilu Dambazau, wanda aka fi sani da Aminu Asid, ya yi kira ga gwamnati da kada ta manta da ‘yan fim a cikin mutanen da za ta ba tallafi a shirin nan da ta ke ƙoƙarin aiwatarwa na agaza wa ‘yan ƙasa mabuƙata.
A hirar sa da mujallar Fim, jarumin ya ce: “Ina ba da shawara tunda mun zamanto masu biyayya ga gwamnati da shugabannin mu, to su yi ƙoƙari wajen samar wa ‘yan masana’antar nan wannan tallafin na rage raɗaɗin rayuwa da gwamnati za ta yi.
“Don ni ban ji ana magana a kan wannan ba.”
Haka kuma jarumin ya yi tsokaci da kira kan shirin sabunta rajistar ‘yan fim da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da ƙungiyar MOPPAN su ke ƙoƙarin yi nan gaba kaɗan da cewa su dubi halin matsin da ake ciki a Nijeriya.
Asid ya ce: “Don Allah idan za a yi wannan sabuwar rajistar a duba hali da yanayi na ƙuncin rayuwa da ake ciki wajen sauƙaƙa harajin da za a karɓa a hannun mu, duba da hali da yanayin rayuwar wannan zamani da mu ka tsinci kan mu…
“Baya ga haka kuma, mecece makomar mu idan an yi rajistar da yake yanzu masana’antar tamu ta na cikin wani yanayi? Ko akwai wani tsari da ita gwamnati ta ke yi wa wannan masana’antar tamu ko kawai ai an ba da muƙami ga wasu ‘yan’uwan mu?”
Asid ya yi la’akari da cewa rabon da a taimaki masana’antar Kannywood da rancen kuɗi tun lokacin da ba ‘yan masana’antar nan ba ne a kan shugabacin.
Ya ce, “Don haka ina kira da ba da shawara a taimake mu ko da da tallafi ko bashi don mu dawo da tattalin arzikin masana’antar tamu.
“Ina yi mana fatan alheri. Ubangiji Allah ya taimaki shugabannin mu da masana’antar mu.”