ƘARSHEN tika-tika, tik! Jaruman Kannywood, Abdul’azeez Muhammad Shareef, wanda aka fi sani da Abdul M. Shareef, da Maryam Muhammad Ƙaura, wadda aka fi sani da Maryam Malika, za su yi aure bayan doguwar soyayya da su ka sharɓa.
Za a ɗaura auren nasu ne a ranar Juma’a, 27 ga Yuni, 2025, a masallacin Alhaji Sani Zangon Daura da ke Unguwar Kaji, hanyar Kaduna zuwa Zariya, da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Maryam Malika ta taɓa auren ƙanen marigayi mawaƙi El-Mu’az Birniwa a cikin watan Yuni, 2012, wanda daga baya suka rabu bayan sun haifi ‘ya’ya.
Tun bayan fitowar Malika daga gidan miji, soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin ta da Abdul M. Shareef, wanda yaya ne ga mawaƙi Umar M. Shareef.
Soyayyar tasu ta yi ƙarfi matuƙa, inda har wasu na cewa Malika ba ta karɓar aikin fim har sai Abdul ya ba ta umarni.
A halin yanzu dai Malika za ta shiga gidan Abdul ne a matsayin matar sa ta biyu.
