A YAU Lahadi, 13 ga Disamba, 2020 jarumin Kannywood Kabiru Ibrahim (Adebo) ya aurar da ɗiyar sa mai suna Hafsat.
An ɗaura auren Hafsat Ibrahim (Adebo) da sahibin ta, Ishaq Shehu Muhammad, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Malam Naziru da ke Tukuntawa, Kano, a kan sadaki N100,000.
Wannan aure na gida ne, domin angon ɗan yayar mahaifin amarya ne, kuma a hannun Adebon ya tashi, don shi ne ya riƙa shi.

Usman Mu’azu da Naziru Ɗanhajiya a wurin ɗaurin auren
Ɗaurin auren ya samu halartar ‘yan fim da dama, waɗanda su ka haɗa da Ali Nuhu, Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara), Hafizu Bello, Adam M. Adam, Naziru Ɗanhajiya, Usman Mu’azu, Jadda Garko, Auwal Ɗanja, Ibrahim Sharukhan da sauran su.
Allah ya sa alheri, amin.
