An kawo ƙarshen taron bikin Kalankuwar Afirika wato KILAF AWARD 2024 da taron bayyana sunayen jarumai da finafinan da suka yi nasara a gasar a daren ranar asabar 30 ga Nuwamba, 2024.
An gudanar da taron ne a babban ɗakin taro na Gidan Gwamnatin Jihar Kano, wanda manyan baƙi daga ciki da wajen ƙasar nan suka halarci taron.

Babban baƙo a wajen, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusif ne, wanda ya samu wakilcin Kwamishiniyar Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko. Sai kuma Ministar Al’adu Hannatu Musawa da Hajiya Kaltume Gana ta wakilta.
An shafe tsawon dare dai ana gudanar da taron har zuwa ƙarfe ɗaya na dare. Kuma daga ƙarshe aka bayyana sunayen jarumai da finafinan da suka yi nasara a gasar.
Waɗanda suka yi nasara dai a cikin finafinai guda 511 da suka shiga gasar daga ƙasashe daban-daban na Afirika su ne:
- Mafi kyawun fim a Gabashin Afirka – ‘The Caller’
- Mafi kyawun fim a Afirka ta Kudu – ‘Face Deep’
- Mafi kyawun fim a Yammacin Afirka – ‘Gidan Dambe’
- Mafi kyawun fim a Afirka ta Tsakiya – ‘Shuka Shuka’
- Mafi kyawun fim a yankin Asiya – ‘Korkyt’
- Gajeren fim a Afirka ta Kudu – ‘Baratani’
- Mafi kyawun gajerun finafinai a Arewacin Afirka – ‘The Third Party’
- Mafi kyawun gajeren fim a Gabashin Afirka – D.A.D.
- Mafi kyawun gajeren fim a Yammacin Afirka – ‘Jini da Igiya’
- Mafi kyawun ‘Documentary Film’ – ‘The Sea Goddess’
- Mafi kyawun fim ɗin ɗalibai – Ƙasar da ba ta da hutawa
- Mafi kyawun samar da sauti – ‘The Caller’’
- Mafi kyawun ‘production design’ – ‘Kaka’
- Mafi kyawun ‘Cinematography’ – ‘Ba A Ji Ba’
- Mafi kyawun tsara labari – ‘The Caller’
- Mafi kyawun kwalliya – ‘Kaka’
- Mafi kyawun tacewa – ‘The Caller’
- Zaɓaɓɓen fim a Nahiyar Afirka baki ɗaya – ‘The Caller’
Jaruman da suka yi nasara a gasar su ne:
- Gwarzon jarumi Yakubu Mohammed, wanda ya taka rol ɗin Malam Habu a fim ɗin ‘Kaka’
- Gwarzuwar jaruma Nice Githinji, wacce ta taka rol ɗin Koki Mandla a cikin fim ɗin ‘The Caller’
- Mataimakin gwarzon jarumi – Madu Bako da fim ɗin ‘Gidan Dambe’
- Mataimakiyar gwarzuwar jaruma – Joanita Wandera Bewolira a matsayin Maada a fim ɗin ‘Makula’
- Gwarzon darakta – Likarion Wainaina Mburu da fim ɗin ‘The Caller’