• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kasafin kuɗin 2025 taswira ce ta ƙarfafa tattalin arziki da cigaban ƙasa – Minista Idris

by Editors
March 4, 2025
in Nijeriya
0
Kasafin kuɗin 2025 taswira ce ta ƙarfafa tattalin arziki da cigaban ƙasa – Minista Idris

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai Alhaji Mohammed Idris yana gabatar da jawabin sa a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai Alhaji Mohammed Idris yana gabatar da jawabin sa a taron

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗi na 2025 a matsayin wata muhimmiyar taswira ta ƙarfafa tattalin arziki, daidaito na zamantakewa, da cigaban ƙasa.

Da yake jawabi a Taron Manema Labarai na Ministoci karo na uku na shekarar 2025 a Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da ke Abuja a ranar Talata, Idris ya ce wannan kasafin ya mai da hankali ne kan saka hannun jari a muhimman sassa da ke da tasiri kai-tsaye kan jin daɗin ‘yan Nijeriya da cigaban tattalin arzikin su.

Ya ce: “Kasafin kuɗi na 2025 ba kawai takardar kuɗi ba ce; taswira ce ta inganta tattalin arziki, daidaito na zamantakewa, da cigaba mai ɗorewa.

“Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.”

Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatarwa za su fara haifar da ainihin sauyi ga al’umma.

Ya kuma jaddada cewa tun tuni aka fara ganin sauƙin farashin kayan abinci, wanda ke samar da sauƙin rayuwa ga ‘yan ƙasa.

Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata domin tabbatar da ingantaccen tasirin sa a rayuwar ‘yan Nijeriya.

Idris (a tsakiya) tare da Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Ƙaramin Ministan ma’aikatar, Sanata John Owan Enoh, a taron

Ya ce, “Ina tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi aiki tuƙuru don ganin an aiwatar da kasafin kuɗi cikin tsari domin ya haifar da gagarumin tasiri a rayuwar al’umma. Saboda haka, ina kira ga ‘yan Nijeriya da su mara wa wannan ƙoƙari baya domin gina ƙasa mai cigaba da haɗin kai.”

Haka nan, Idris ya jinjina wa ‘yan jarida kan rawar da suke takawa wajen bayar da rahotanni na gaskiya da suka shafi cigaban ƙasa.

Ya buƙace su da su ci gaba da gudanar da aikin jarida bisa ƙa’idojin da suka dace domin ƙarfafa dimokiraɗiyya da inganta sanin makamar gwamnati a tsakanin al’umma.

“A wannan zamani da ƙarya ke yawaita wajen ruɗar da jama’a, jajircewar ku kan gaskiya da adalci ta fi zama dole fiye da kowane lokaci. Dole ne mu haɗa kai domin tabbatar da cewa labaran da ke tsara yadda ake tattauna batutuwan jama’a sun kasance bisa haƙiƙanin gaskiya, ba tare da son zuciya ko ƙazafi ba,” in ji shi.

Taron ya samu halartar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Ƙaramin Ministan ma’aikatar, Sanata John Owan Enoh, da wasu jigajigan gwamnati.

Wani sashe na mahalartan taron

Loading

Tags: Alhaji Mohammed IdrisDr. Jumoke OduwoleSanata John Owan Enohtaron manema labarai
Previous Post

Zargin ɓata sunan Kannywood: kotu ta tura ɗan TikTok Ahmed Pasali zuwa kurkuku

Next Post

Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na Chana – Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na Chana – Ministan Yaɗa Labarai

Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na Chana – Ministan Yaɗa Labarai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!