BIYO bayan maka ɗan TikTok Ahmed Pasali da aka yi a kotu, a yau Litinin matashin ya bayyana a gaban Babbar Kotun Yanki (Upper Area Court) da ke Kasuwar Nama a Jos, Jihar Filato, domin fuskantar alƙali.
Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ce ta yi ƙarar sa bisa tuhumar ƙazafi da ɓata sunan Kannywood da ya yi a wani saƙon bidiyo da ya wallafa a soshiyal midiya.
An karanta wa Pasali tuhume-tuhumen da ake yi masa waɗanda suka haɗa da ƙazafi da ɓata sunan ‘ya’yan masana’antar Kannywood, shi kuma Pasali ya musanta zargin.
Nan take lauyan sa ya roƙi kotu da ta ba da belin sa.
Bayan sauraren kowane ɓangare, sai Mai Shari’a Thomas Nakowa ya zayyano sharuɗɗan ba da belin nasa da suka haɗa da ajiye kuɗi N250,000, da kawo wanda zai tsaya masa wanda yake da gida a cikin Jos, kuma zai kawo wa kotu takardun gidan, sannan dole ɗaya daga cikin membobin MOPPAN ya sa hannu.
Rashin cika ƙa’idojin ya sa aka wuce da Wasalin gidan gyaran hali, har sai ya cika waɗannan ƙa’idoji.
Alƙali ya ɗage zaman sauraren ƙarar zuwa 5 ga Afrilu.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Shugaban MOPPAN na Ƙasa, Malam Umaru Maikuɗi Cashman, ya sha alwashin ƙungiyar za ta saka ƙafar wando ɗaya da duk wani wanda a ɓata sunan ɗan Kannywood ko yin ƙazafi ga ‘ya’yan ta.
![]()







