AN kafa Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano ne sakamakon ƙoƙari da hoɓɓasan da su masu sana’ar shirya finafinai su ka yi na tsaftace sana’ar su da kan su a lokacin gwamnatin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a zangon sa na farko. An kafa hukumar ne domin ɗaga darajar sana’ar da tsaftace al’amuran finafinai domin su yi daidai da al’adun mu, zamantakewar mu da addinin mu.
Bayan wani lokaci, hukumar ta faɗaɗa komar ta wurin faɗaɗa ayyukan ta zuwa wasu al’amuran kamar kula da bibiyar rajistar gidajen kallo, masu tallar magunguna, ɗab’i da mamaye harkokin tafiyar da ƙungiyoyin masu shirya finafinai kamar rajista ta ‘ya’yan ƙungiyoyi da ma wasu abubuwan. Hakan ba ya cikin hurumin kundin tafiyar da hukumar na shekarar 2001/2002 kuma babu wani gyara da gwamnati ta yi a hukumance har ya zuwa yanzu.
Ba a nan Gizo ke saƙar ba. Duk da irin tsangwama da tursasawa da hukumar ke yi wa jarumai, furodusoshi, daraktoci da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fim, ‘yan Kannywood na ƙoƙarin yin biyayya ga duk al’amuran hukumar saboda a zauna lafiya duk da sanin cewa akwai wurare da dama da ake hawan ƙawara wurin tafiyar da hukumar.
Bayan wani nazari na bincike da mu ka yi, mun gano wasu abubuwan da ke faruwa waɗanda su na da buƙatar kawo ɗauki da gyarawa domin cimma nasarar hukumar da kyautatuwar masu sana’ar fim, kamar haka:
1- Akwai tsarin rajista da sabunta ta da hukumar ta bijiro da shi, wanda a kan yi a duk shekara, kuma hukumar ta na ɗaukar tsattsauran mataki tun daga watan farko na Janairu ba tare da ta yi duba da durƙushewar tattalin arziki da masana’antar ke fuskanta ba, ƙalubalen rashin aikin yi. Babu ɗaga ƙafa a watanni uku na farkon shekara, kuma babu tuntuɓa ko bin wata hanya da za a sanar da masu sana’ar cewa lokaci ya yi da ya kamata a zo a sabunta rajista kamar yadda sauran hukumomin tattara haraji su ke yi, sai kawai idan mai shirya fim ya zo neman takardar izinin ɗaukar fim (permit) – wanda shi kan sa wannan ɗin ba bisa ƙa’ida ya ke ba – sai a tursasa shi a kan sai ya biya kuɗin sabunta rajista na kowane ɗan wasa da ya zaɓa zai saka a cikin fim ɗin sa.
Wannan ba daidai ba ne. Ba ma haƙƙin furodusa ba ne biyan kuɗin sabunta rajistar ɗan wasa. Ga kuma bada lasisin da hukumar ta ke yi ga duk wani wanda ya zo neman wani abu ba tare da wata takarda daga hannun ƙungiyoyin finafinai ba domin sahalewa.
Duk da duk irin tsangwama da tursasawar da hukumar ke yi wa jarumai, furodusoshi, daraktoci da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fim, ‘yan Kannywood na ƙoƙarin yin biyayya ga duk al’amuran hukumar saboda a zauna lafiya duk da sanin cewa akwai wurare da dama da ake hawan ƙawara wurin tafiyar da hukumar
2- Hukumar na karɓar kuɗin sabunta rajista sau biyu ko sau uku a shekara. Wannan biyan haraji sau biyu ne, wato ‘double taxation’, a kan ‘yan wasa da masu aikin bayan fage a wurin masu shirya finafinai saboda duk mai shirya fim idan ya zo sai a gaya masa cewa wai ‘yan wasan sa ba su sabunta rajistar su ba, a karɓi kuɗin sa, kuma idan wani furodusa ya zo da wasu sunayen ‘yan wasan da wancan furodusan na farko ya zo da su sai shi ma a gaya masa cewa ba su yi sabuntawa ba. Wato kenan an karɓa a can an kuma karɓa a nan! Babu wani kundi da ya ke nuna wannan ɗan wasa ya sabunta rajista ko akasin haka. Hankalin hukumar ya tattara ne wurin tattara kuɗi a kan hanyar da ta dace ko rashin dacewa.
Misali, akwai furodusan da ya biya kuɗin rajistar wasu jarumai da zai saka a sabon fim ɗin sa a watan Fabrairu na wannan shekarar ta 2022. A lokacin, sai da ya ja hankalin hukumar da cewa ya kamata a ɗaga masa ƙafa, ba don komai ko don rugujewar tattalin arziki da masana’antar ke fuskanta aƙalla watanni uku na farkon shekara, amma jami’an hukumar su ka tubure sai da ya biya. Hakan aka yi ya ƙara turo wasu daga cikin jaruman da ya biya wa kuɗin sabuntawar a kan su je su ƙara biya a watan Maris 2022 domin tabbatar da zargin. Hukumar ta ƙara karɓar kuɗin, luma ta bada rasiɗi.
Wannan lamari ya jima ya na faruwa, amma su furodusoshi aikin su kawai su ke yi ba tare da sanin hakan ba. Hakika wannan lamari na da buƙatar a zurfafa bincike domin a yi wa tufka hanci.
3- Maganar takardar izinin fita ɗaukar fim (shooting permit), idan mu ka koma mu ka duba cikin kundin tafiyar da hukumar na shekara 2001/2002, babu wata saɗara da ta yi magana a kan hakan, kuma babu wani ɓangare na kasuwanci a Jihar Kano ko Nijeriya da ake tursasa mutane karɓar lasisi ko izinin zuwa kasuwa a kowace rana, duk da maƙudan kuɗaɗen da hukumar ke karɓa na rajistar kamfanoni, ‘yan wasa da masu aikin bayan fage da hukumar ke karɓa a duk shekara, sai a masana’antar Kannywood hakan ke faruwa. Babu tausayi a cikin al’amuran hukumar sai gallaza wa masu sana’ar, wanda hakan ba daidai ba ne. Akwai buƙatar a yi duba na tsanaki.
4 – A kullum Hukumar Tace Finafinai ta na raba kan masu sana’ar fim wurin shigo da siyasa cikin ayyukan ta da ware ‘yan bora da ‘yan mowa.
Misali, hukumar ta shirya wani aikin horas da masu sana’ar da haɗin gwiwar gwamnatin mai albarka baban mu Dakta Abdullahi Umar Ganduje a Jihar Kano, inda aka horas da mutane masu yawan gaske. Abin kaico, sai aka ware wasu da ake ganin wai su na adawa da hukumar ne saboda su na jan hankalin ta wurin tafiya a kan turba wurin rashin ba su damar shiga tsarin ko hana su satifiket da tallafin kayan aiki na shaidar kammala koyarwar, sannan ake zargin abin da gwamnati ta sahale na kayan aiki an musanya shi da mai ƙasƙanci daraja. Wannan abin kunya ne a fuskar hukumar da ke yamaɗiɗin kawo gyara da cigaba.
5 – Yaudara da ƙarairayi ba kama hannun yaro. An yaudari masu sana’ar shirya fim da cewa za a ba su tallafi mai tsoka domin cigaban sana’ar. Hukumar ta yi amfani da wannan dama wurin tatsar ‘yan Kannywood wasu kuɗaɗen masu nauyi, yaudarar samar da wata kasuwar fim, wanda har yanzu kiɗa kawai mu ke ji a Magwan, babu wani ƙudiri da hukumar ta yi alƙawarin samar wa ‘yan masana’antar da ya tabbata sai kambamin zulaƙe kamar a labarin Gizo da Ƙoƙi.
6 – Akwai buƙatar samar da ƙwararru wurin duba fim kafin fitar sa, wato ‘preview’, domin waɗanda aka naɗa su na wannan aikin ba ƙwararru ba ne ko kuma ba su da wani ma’auni na ƙwarewa wurin tace fim. Akwai buƙatar ƙaro sanin menene fim ko kuma yaya ake yin fim ko kuma wane abu ya dace ko saɓanin hakan. Ya na da fa’ida a haɗa su da waɗanda su ke yin fim a zahiri domin su ƙara sanin makamar aikin fim. Jajircewa da fahimtar fim abu ne wanda ba shi da shinge, amma hukumar ta yi burus da yadda ake wulaƙanta fim, a fiffige shi kamar kazar mayu. Hakan ya na mayar da mu baya a duniyar finafinai. Lallai akwai buƙatar gyara a wannan lamari.
A ƙarshe, ina kira ga mai girma shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da ‘yan majalisar ƙoli a hukumar, da shugabannin ƙungiyoyin masu sana’ar fim da masu ruwa da tsaki da a yi gaggawar nemo hanyar gyara da cigaba mai ɗorewa a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.
* TY Shaba fitaccen jarumi ne, mawaƙi kuma furodusa a Kannywood