AUREN fitaccen daraktan Kannywood Hassan Giggs da fitacciyar jaruma Muhibbat Abdulsalam ya na ɗaya daga cikin aurarrakin ‘yan fim ɗin Hausa da ake kafa misali da su ta fuskar daɗewa da kuma zaman lafiya da ƙaruwar arziki a tsakanin ma’auratan. Aure ne mai cike da soyayya da ƙaunar juna. Har ta kai ga Giggs ya na iƙirarin cewa ba zai iya yin adalci a tsakanin matan sa ba muddin ya ƙara aure.
An dai ɗaura auren su ne a ranar 28 ga Yuni, 2008 a Kaduna, wanda ya kama shekara 13 cur a yau ɗin nan.
Domin murnar wannan rana, tun da sanyin safiyar yau Giggs ya turo wa mujallar Fim hotunan murnar cika shekara 13 da shi da iyalin sa su ka ɗauka. Don haka ne mujallat ta waiwaye shi domin ta ji ta bakin sa dangane da sirrin daɗewar auren su da sauran batutuwa. Ga tattaunawar:
FIM: Ya za ka kwatanta tsawon waɗannan shekaru 13 da ku ka yi a matsayin ma’aurata kai da Muhibbat?
HASSAN GIGGS: Alhamdu lillah! Ba ni da wani abin da zan ce illa godiya ga Allah, saboda ya ba ni mata ‘yar gidan mutunci, karamci da kuma tarbiyya.
Domin kuwa ba na mantawa tun a farkon haɗuwar mu a shekara ta 2005 amma ba mu yi aure ba sai 2008, domin kuwa a lokacin da ake shirye-shiryen bikin, ba na mantawa, na je na samu wasu ɗakunan taro inda za a yi shagali a ciki domin ka san mu mu na da jama’a, to da mahaifin ta ya ji labari sai ya kira ni ya ce, “Hassan, na ji an ce ka kama ɗakin taro, ko?” Na ce, “Haka ne.” Sai ya ce, “Nawa ka biya?” Sai na ce, “Dubu ɗari biyu da goma sha biyar.” Nan fa ya ce na je na karɓo. Haka kuma aka yi; na je na ƙarɓo na kawo masa. A nan take ya kira wani abokin sa ya ce akwai wani ‘hall’ ɗin makaranta a gyara shi ɗan sa zai yi biki a ciki, nawa ake biya? Sai aka ce masa dubu ashirin da biyar. Nan ya ɗauka ya biya.
Sannan ya tambaye ni, “Nawa ne kuɗin da za ka biya na sadaki?” Na ce masa, “Dubu hamsin.” Nan ya ce ba za a yi haka ba, dubu goma zan bayar, sauran na haɗa su da waɗancan kuɗin na ajiye domin kuwa akwai wani hali da ma’aurata su ke shiga a satin farko, waɗannan kuɗin za su yi maka amfani.
Duk da yake ba a ce wa ma’aurata ba sa samun matsala, amma muhimmin abu shi ne ku san yadda za ku yi domin ku ga kun magance matsalar ku ba tare da wani ya ji ko ya sani ba.
Har wa yau, ba na mantawa da wani lokaci da mahaifiya ta ta zo gidan mu ta ke ce min, “Kai, ku na burge ni! Hassan ba ka taɓa kawo ƙarar matar ka ba.” Na ce, “Mama, ya za a yi na kawo ƙarar mata ta?” Mu ka yi dai wasa da dariya.
Ni abin da ni na yarda da shi a nawa tunanin shi ne a duk lokacin da ka fara bada ƙofa wani ya san irin halin da ka ke ciki da iyalin ka ko ka ba shi labari, to fa lallai auren ku ya fara samun matsala. Sannan kuma idan babu yarda a aure, to akwai matsala.
Mata ta a tsawon shekara13 ta yarda da ni na yarda da ita, ba ma zargin juna. Wannan ya na ɗaya daga cikin nasarar da mu ka samu.

FIM: Ka taɓa bayyana wa mujallar Fim cewa ba za ka iya yi wa matar ka kishiya ba. Shin har yanzu maganar ta na nan ko kuma ta sauya zani?
GIGGS: Maganar tsakani da Allah ni ina tunanin cewa idan zan ƙaro wata, idan har ban so ta yadda na ke son mata ta ta farko ba, ban yi adalci ba. Shi ya sa na ke cewa ni ba zan iya ƙara aure ba, idan na ƙara aure ba na tunanin zan so ta fiye da yadda na ke son mata ta Maman Humaira kenan.
Sannan ba na tunanin zan iya ƙara aure gaskiya saboda mu na zaman lafiya da ita.
FIM: Wane abu ne ka ke jin ba ka iya mantawa da shi a zaman ku?
GIGGS: Ba na manta a duk lokacin da zan yi tafiya ko na dawo ko ba na nan idan ta yi amfani da kuɗin hannun ta, wato ta ranta min, in na dawo za ta ce, “To Baban Humaira ga shi mun yi amfani da kuɗi kaza, idan Allah ya hore maka za ka biya ni.” Yawanci ba ta jira na na yi wani abu ko ina nan ko ba na nan, sai dai na zo gida na ga ta yi abu da kan ta, sai dai daga baya in ce, “Ga shi dai an samu, Allah ya yi albarka, na gode.” Waɗannan abubuwan ba na mantawa da su.
FIM: A shekarun nan 13, ‘ya’yan ku nawa da Muhibbat?
GIGGS: ‘Ya’yan mu uku. Mu na da A’isha Humaira, mu na da Fatima, Azima kenan, sannan kuma mu na da Nana Khadija.
FIM: Wane fata ka ke da shi a rayuwar ku ta nan gaba?
GIGGS: Fatan mu ni da ita mu kai shekaru aru-aru har babu haƙora! (dariya) Kamar yadda ta ke magana, wai in zauna har babu haƙora a baki na ita ma ba haƙora a bakin ta! (dariya)
Kuma ina sa ran in Allah ya yarda ni da ita mu ƙara haɗuwa a Aljanna in-sha Allahu.

Comments 1