CUTAR koronabairus (COVID-19) ta sa an ɗage ci gaba da ɗaukar fim ɗin ‘The Right Choice’ a garin Abuja, inji babban furodusan shirin, Malam Kabiru Musa Jammaje.
Ya ƙara da cewa tun a cikin watan Janairu 2020 ne aka fara aikin fim ɗin, inda aka shafe tsawon mako biyu ana yi, wato daga ranar 26 ga watan zuwa 10 ga Fabrairu.
Wasu matsaloli sun sa ba a samu damar kammala aikin ba a lokacin da aka tsara, don haka aka mayar da ƙarashen aikin zuwa 10 ga wannan watan na Afrilu.
Yanzu kuma ɓullar cutar ‘coronabairus’ ta sa aikin ba zai yiwu ba.
A hirar sa da mujallar Fim, Jammaje ya ce: “Duba da yadda ake ciki a yanzu ya sa dole mu ka ajiye maganar ƙarasa fim ɗin duk da cewar kusan kashi tamanin cikin ɗari na aikin mun gama shi.
“Don haka kashi ashirin cikin ɗari ne yanzu ya rage mana, amma za mu jira mu ga yadda yanayi zai bayar nan gaba, sannan mu ƙara tsaida wata sabuwar ranar.”
Dangane da yadda aikin ya gudana kuwa, furodusan ya ce, “An yi aiki cikin nasara, don haka mu ke da ƙarfin gwiwar ƙarashen ma za mu samu nasara fiye da wadda mu ka samu a baya, don haka akwai nasara a cikin aikin.”
‘The Right Choice’ gagarumin fim ne da ake ganin shi ne na farko da wani ɗan Kannywood ya shirya da ya lashe kuɗi mafi yawa tarihin masana’antar.
Ana ƙiyasin cewa zai lashe zunzurutun kuɗi har naira miliyan 35 kafin a kammala shi.
Fim ɗin ya ƙunshi manyan jaruman Kannywood da na Nollywood.
‘Yan Kannywood sun haɗa da Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Asabe Madaki da Sani Mu’azu, yayin da ‘yan Nollywood su ka haɗa da Segun Arinze, Nancy E. Isime, Enyinna Nwagwe, da sauran su.
A ƙarshe, Jammaje ya bayyana alhinin sa dangane da halin da duniya ta samu kan ta a ciki sakamakon wannan annoba ta ‘COVID-19’, ya na fatan Allah ya kawo mana ƙarshen ta.