KOTUN Majistare mai lamba 21 da ke No-Man’s-Land, Kano, ta yanke wa jarumin Kannywood kuma ɗan TikTok Abubakar Usman Kilina hukuncin ɗaurin shekara ɗaya ko biyan tarar N100,000 tare da biyan Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano tarar N30,000 saboda ɓata mata lokaci da ya yi.
Hukuncin ya biyo bayan samun sa da laifin rashin ɗa’a da shigar ‘yan daudu da furta kalamai marasa tarbiyya a bidiyon sa da yake gabatarwa a TikTok.
Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ce ta yi ƙarar sa a kan zargin karya dokar ta da ya yi.
Alƙalin kotun, Hajiya Hadiza Muhammad Hassan, ta ja hankalin Abubakar da ya daina yin abubuwan da suka saɓa wa doka, da sharaɗin idan har ya sake aikatawa to za ta ɗaure shi shekara ɗaya babu tara.
Tun a ranar 2 ga Yuni ne dai Hukumar Tace Finafinai ta gurfanar da shi a kotun inda aka karanta masa laifin sa a lokacin kuma ya musanta. Don haka ne kotu ta tura shi kurkuku har zuwa yau Alhamis domin ta yanke hukuncin.
A lokacin da yake bayani ga ‘yan jarida ta bakin jami’in yaɗa labarai na hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya jaddada aniyar sa ta kawo ƙarshen ayyukan rashin ɗa’a da ke yawaita a soshiyal midiya a Jihar Kano.
Ya bayyana aniyar sa ta ci gaba da kare martabar addini da kuma kyawawan al’adun jama’ar jihar.