JARUMAR Kannywood Ikilima Yusuf ta buɗe kanti nata na kan ta mai suna Ekeey Collection a ranar Laraba da ta gabata a Kano.
Katafaren kanti ne wanda ke lamba 3, Titin Sheikh Dakta Nasiru Kabara, daura da Gidan Ɗan’asabe da ke Titin Gidan Zu.
A wajen taron an shaƙata da kaɗe-kaɗe da raye-raye, daga baya kuma aka yanka kek tare da yanka igiyar ƙaddamar da kantin.
Kayan da za a riƙa sayarwa a wajen sun haɗa da atamfofi, yadiddika, shaddoji, takalma da jakankuna.

Da ta ke jawabi yayin buɗewar, Hajiya Ikilima Yusuf ta yi godiya ga Allah da ya sa ta ga wannan rana. Ta ce buɗe wajen harkar kasuwancin nata ya na ɗaya daga cikin burukan ta a rayuwar.
Bayan haka nan ta yi godiya ga dukkan waɗanda su ka ba ta gudunmawa wajen shirya bikin da kuma ƙawaye da ‘yan’uwa da abokan arziki da su ka samu halartar wajen.
Ta ce: “Ina fatan za ku taya ni da addu’ar Allah ya sa an buɗe a sa’a, da fatan Allah ya kai kowa gidan sa lafiya.”
Ɗimbin mahalartan bikin dai sun taya Ikilima murna tare da bayyana jin daɗin su dangane da wannan yunƙuri da ta yi na tsayawa da ƙafafun ta.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a yanzu buɗe wurin kasuwanci abu ne da ya zama ruwan dare a cikin Kannywood, musamman ma dai mata. Su na yin rige-rigen buɗe wajen kasuwanci, wanda hakan alama ce ta ƙoƙarin su na neman madafa ba tare da sun dogara kacokam a kan harkar fim ba.


