• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

MOPPAN da KAFIGAN sun yi gaisuwar rasuwar Galadiman Kano

* KAFIGAN ta yi wa El-Mustapha ta'aziyyar rasuwar kakan sa

by ALI KANO
April 2, 2025
in Nijeriya
0
MOPPAN da KAFIGAN sun yi gaisuwar rasuwar Galadiman Kano
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYOYIN Kannywood biyu, wato Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da Kannywood Film Industry Guilds and Associations (KAFIGAN), sun miƙa saƙon alhinin su ga iyalan Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, kan rasuwar sa.

Shi dai Galadima, Allah ya yi masa rasuwa ne jiya yana da shekara 92 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Dattijon , wanda ya fi kowa tsufa a cikin masu riƙe da muƙamin sarauta a masarautar Kano, ya bar ‘ya’ya da jikoki masu yawa. Ɗaya daga cikin ‘ya’yan sa shi ne Shugaban jam’iyyar APC ta Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.

A cikin takardar sanarwar da MOPPAN ta fitar ta hannun jami’in ta na yaɗa labarai, Malam Ibrahim Amarawa, ƙungiyar ta ce: “Al’ummar Kannywood sun samu labari maras daɗi na rasuwar marigayi Galadiman Kano Alh Abbas Sanusi. Rasuwar sa ba kurum babban rashi ne ga Masarautar Kano ko Jihar Kano kaɗai ba har ma ga Nijeriya baki ɗaya.

“Muna addu’ar Allah maɗaukakin sarki ya gafarta masa kuma ya ba iyalin sa da masoyan sa da dukkan jama’ar Jihar Kano haƙurin jure wannan babban rashin.”

A nata ɓangaren, ƙungiyar KAFIGAN ta fitar da sanarwa ta hannun Daraktan ta na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Malam Al-Amin Ciroma, a Abuja, inda ta ce: “Cikin zurfin baƙin ciki, ƙungiyar Kannywood Film Industry Guilds and Associations (KAFIGAN) tana miƙa saƙon gaisuwar ta kan rasuwar Alhaji Abbas Muhammadu Sanusi, wato Galadiman Kano kuma babban mai zaɓen sarki a Masarautar Kano.”

A takardar, an ruwaito ciyaman na kwamitin amintattu na ƙungiyar, Alhaji Isma’il Na’Abba (Afakallahu), yana bayyana mariganyin da cewa “babban ginshiƙi ne ga tsarin sarautar gargajiya, wanda gudunmawar da ya bayar ga ɗorewar ta da cigaban ta za a ci gaba da tuna su har ma a wajen Masarautar Kano.”

Afakallahu ya miƙa gaisuwar sa ga gwamnati da jama’ar Jihar Kano, da majalisar Sarki da dukkan iyalin mamacin, muna addu’ar Allah ya jiƙan sa ya saka masa da gidan Jannatul Firdaus.

A wani labarin kuma, KAFIGAN ta miƙa saƙon ta’aziyya ga Babban Darakta na Hukumar Tace Finafinai da Ɗabi’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, bisa rasuwar kakan sa, Malam Kawu Na Warure, wanda ya rasu a yau sakamakon rashin lafiya.

A wata takardar sanarwar da Ciroma ya bayar, an ambato Darakta-Janar na ƙungiyar, Hon. Adamu Bello, a madadin kwamitin amintattu da membobin ƙungiyar, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga El-Mustapha kuma ya yi addu’ar Allah ya jiƙan kakan nasa.

Abba El-Mustapha da kakan sa, Malam Kawu Na Warure

Loading

Previous Post

Kidinafas sun sako Janar Tsiga bayan kwana 56 da tsare shi

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta fara sabunta kayan aikin gidajen watsa labarai, cewar Minista

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta fara sabunta kayan aikin gidajen watsa labarai, cewar Minista

Gwamnatin Tarayya ta fara sabunta kayan aikin gidajen watsa labarai, cewar Minista

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!