MINISTAR Ayyukan Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa kwanan nan za a ƙara ɗaukar matasa masu cin gajiyar shirin tallafi na ‘N-Power’ su 400,000.
Ta yi wannan albishir ne a Kano, lokacin da ta ke jawabi wurin rufe kwas ɗin horas da matasa fasahar ‘N-Knowledge’, waɗanda aka kammala horar da su a ƙarƙashin Rukunin C.
Ministar ta ce ƙarin matasa 400,000 ɗin da za a ɗauka duk su na cikin matasa miliyan ɗaya da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a samar wa tudun dafawa a ƙarƙashin shirin na ‘N-Power’.
Ta ce, “Shirin Kashi na C1 ya ƙunshi matasa 510,000, sai Kashi na C2 da za a ɗauka kwanan nan, su kuma 400,000 ne.”
Hajiya Sadiya ta ce, “Tsarin ‘N-Knowledge’ shiri ne da aka ƙirƙiro shi domin horar da matasa 20,000 fasahar ayyukan kwamfuta masu tafiya da zamani, tare da ba su takardun shaidar ƙwarewa a fannonin da su ka samu horo a kai, ta yadda za su iya samun ayyukan dabarun fasahar zamani a cikin ƙasar nan da sauran ƙasashen duniya.
“Kuma za su samu ƙwarewa sosai wajen dabaru da fasahar ƙirƙirar ababen samar da cigaba da kuma dabarun sana’o’in hannu a zamanance a cikin ƙasa ko sauran ƙasashen duniya.”
Daraktan Harkokin Kuɗaɗe na shirin, Muhammad Sambo, shi ne ya wakilci ministar a bikin yaye matasan su 3,000 da aka yi ranar Laraba a Kano, waɗanda aka zaɓo daga cikin dukkan jihohin Arewa-maso-yamma.
Ya ce a yanzu an horas da matasa 13,000 a faɗin ƙasar nan, kuma ana nan za a zaƙulo cikon ragowar 7,000 daga ko’ina cikin ƙasar nan.