WATAƘILA idan na ce kasuwar finafinan Hausa ta mutu ban yi kuskure ba, amma kuma za ta iya kasancewa ni ne ban fahimci halin da kasuwar ta ke ciki ba. Amma dai kasuwar finafinan Hausa ta na cikin buƙatar agaji da shugabanci nagari da kuma haɗin kai a tsakanin waɗanda su ke cikin masana’antar ta Kannywood.
Shirye-shirye masu dogon zango (series films) su ne su ka kasance abin da masana’antar ta riƙe a matsayin wanda zai riƙe harkar saboda masu kallo sun karkata ga kallon shiri mai dogon zango.
> Karɓuwa Da Abin Da Ya Biyo Baya
Tun farkon fara shirin ‘Labari Na’ ya karɓu a wajen al’umma, musamman masu son kallon finafinan Hausa, saboda yadda ake yaɗa labarin fim ɗin a shafukan sada zumunta da kuma yadda shi kan sa marubucin ya tsara labarin.
Tun daga lokacin da aka fara tallar fim ɗin na fara jiran ranar da za a fara haskawa. Hakan ya sa tun daga ranar da aka fara shirin har yau babu abin da ya wuce ni a cikin shirin, kuma na yi sharhi a kan shirin tun farko-farko, kafin in daina saboda dalili na ƙashin kai na.
Masu bibiyar shirin sun daɗe da samun labarin cewa Nafisa Abdullahi za ta daina fitowa a cikin shirin, tun kafin ta fitar da sanarwar da ta fitar a ranar Asabar, 1 ga Junairu, 2022.
Fitar Nafisa ta haifar da gagarumin giɓi a cikin shirin, duba da yadda aka gina labarin a kan ta kuma babu yadda shirin zai ci gaba ba tare da haska ta ba. Kusan kashi 70 cikin ɗari na waɗanda su ke cikin shirin ‘Labari Na’ su na da alaƙa da labarin Nafisa, wanda hakan ya sa ta zama jagora a fim ɗin.
Haka shi ma Nuhu Abdullahi, wanda ya na da tasiri sosai a cikin shirin, saboda daraktan shirin sai da ya fara fitar da shi daga cikin labarin, bayan ya bar gida saboda rashin sanin asalin sa, amma aka sake dawo da shi cikin rayuwar Sumayya saboda labarin Sumayya ba zai cika ba sai da Mahmoud, amma daga baya darakta ya fitar da shi ta hanyar kashe shi.

> Darajar Jarumai
Amma mu yi duba kan Nafisa da Nuhu Abdullahi kafin fara shirin ‘Labari Na’.
A tsarin Kannywood, jaruman masana’antar su na da daraja guda uku kamar yadda ni na ke gani. Akwai wanda jarumi ne kuma dole sai da shi, wato idan ka na son fim ɗin ka ya samu kasuwa ka na buƙatar shi. Akwai waɗanda ba yabo ba fallasa, wato ‘yan tsakiya, sai kuma waɗanda ‘yan ciko ne.
Sannan kafin shirin ‘Labari Na’ duk wanda ya ke bibiyar finafinan Hausa ya san Nafisa ta fita daga cikin jaruman da su ke kan ganiyar su, wato ina nufin an samu matasa masu tasowa. Shirin ‘Labari Na’ ne ya dawo da ita kan ganiyar ta kuma ta dawo da sharafin ta.
Bayan fara ‘Labari Na’ Nafisa ta samu talla da kamfanin Pepsi, idan ban yi kuskure ba, sannan ta buɗe kamfani kamar yadda ta bayyana, bugu da ƙari hotunan ta su ka dawo shafukan sada zumunta da jaridu.
Nuhu Abdullahi ya na cikin ‘yan babu yabo babu fallasa, wato jarumi ne wanda idan babu shi a cikin fim zai karɓu kuma ‘Labari Na’ ya dawo da martabar sa a Kannywood.
> Me ya sa su ka fita?
Kamar yadda Nafisa ta bayyana dalilan ta na yanke hukuncin fita daga cikin shirin, har yanzu ba mu ji dalilin da ya sa Nuhu ya fita ba, daga bakin sa ko kuma daga wajen daraktan fim ɗin.
Dole ne in girmama dalilan su, amma fa kada su manta cewa sun shiga wani layi da al’umma su ke kallon su a matsayin masu ɗebe masu kewa kuma sun ɗauko wani aiki wanda masu kallo su ke bibiyar su har ake ɓata lokaci ana kallon su, sannan a yi sharhi a kan shirin ‘Labari Na’ duka saboda su.
Sun kai wani mataki a cikin shirin ‘Labari Na’ wanda dole mai kallo ya na buƙatar su domin ganin yadda labarin zai zo ƙarshe.
Wannan abu da ya faru a cikin shirin ‘Labari Na’ barazana ce ga Kannywood saboda nan gaba za a iya samun wasu jaruman su aikata abin da ya faru. An nuna wa jarumai masu tasowa hanyar yin bore a lokacin da su ka ga cewa dole sai an yi da su a harkar
Tabbas, abin da su ka yi ba zai yi wa mai kallo daɗi ba idan har sun yarda cewa domin al’umma su ke yi, to ya kamata su da daraktan fim ɗin su yi haƙuri su kammala aikin da su ka ɗauko domin kada su rasa daraja da girmamawa tare da goyon baya daga wajen masu kallo. Sannan su ma wataƙila su na da burin yin fim nasu na ƙashin kan su (da man Nafisa ta na yin nata), wannan matakin da su ka ɗauka zai iya shafar kasuwar su ta gaba (ba na fatan haka).
> Matsayin Aminu Saira
A shekarun baya ba na tsayawa in kalli kowane irin fim idan har ba Aminu Saira ne ya yi shi ba saboda yadda ya iya bayar da umarni da kuma kawo labari mai sosa zuciya.
Hakan ya sa na sake amincewa da shi a wannan lokacin tun da na ga shi ne daraktan fim ɗin na ‘Labari Na’, saboda na gama yarda da aikin sa.
Kuma a cikin shirin idan mai kallo bai manta ba, ai ya canja mahaifin Presido. Da farko Ibrahim Mandawari ne mahaifin Presido, amma daga baya aka canja shi saboda wani dalili da Saira bai bayyana ba. Yadda na yarda da iya aikin Saira, na yi zaton zai yi wani abu domin ganin fitar Mahmoud daga cikin shirin ba ta taɓa darajar labarin ba, amma sai dai kawai ya yanke hukunci ya cire shi saboda rashin daidaita kwangila (idan ita su ke ƙullawa).
Akwai finafinai da dama da aka yi kuma aka canja jarumai ba tare da an samu irin wannan matsalar ba kuma babu abin da ya canja saboda shi mai kallo labari ya ke bibiya ba jarumai ba (amma su ma jaruman su na taka babbar gudunmawa wajen ƙarɓuwar fim).
Tabbas, Saira ya samu matsala kuma ya na da damar ɗaukar duk wani mataki da ya ke ganin ya fi masa kyau, amma ya na buƙatar ci gaba da tafiya da masu bibiyar sa saboda yadda aka yarda da aikin sa.
> Barazana Ga Kannywood
Wannan abu da ya faru a cikin shirin ‘Labari Na’ barazana ce ga Kannywood saboda nan gaba za a iya samun wasu jaruman su aikata abin da ya faru. An nuna wa jarumai masu tasowa hanyar yin bore a lokacin da su ka ga cewa dole sai an yi da su a harkar.
Finafinai masu dogon zango su ne su ka rage wa Kannywood kuma tun kafin su yi nisa sun fara ɗaukar hanyar lalata harkar.

Yanzu ‘yan Kannywood sun zama ‘yan siyasa, sun koma tallar ‘yan takara, daga wajen wannan ɗan siyasar sai wajen wannan. Harkar fim ɗin ta fara tsayawa, sannan sun fara dawowa ta hanyar ‘series film’. Amma wannan matakin da su ka fara ɗauka tabbas babu inda za su je.
Mutane da yawa ba su kula cewa shi kan sa ‘Labari Na’ ya samu canjin marubuci ba. Yanzu ba Ibrahim Birniwa ba ne ya ke rubutawa. Hakan ya na nufin babu Nafisa, babu Nuhu Abdullahi sannan babu wanda ya fara rubuta labarin tun farko. Ka ga dole a samu matsala!
* Abba Gwale ɗan jarida ne mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum a Kano. I-mel abbalggwale18@gmail.com