• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Alhaji Bashir Tofa: Ba Rabo da gwani ba….

by DAGA FATUHU MUSTAPHA
January 3, 2022
in Tsokaci
0
Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa

Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

“Ku mu taru mu zaɓi NRC don kadda mu kai ga taɓewa….”

NA fara gamuwa da Alhaji Bashir Usman Tofa tun zamanin NRC da SDP. Amma sani na mutum da mutum sai ‘yan shekarun nan, sai dai cikin ƙanƙanin lokaci mu ka saba, ta zama kamar sanayyar shekara da shekaru. 

A sanin da na yi masa, mutum ne mai dattako da yakana, kishi da mutunta mutane. Ba ya shayin faɗar gaskiya ko a kan waye. Ga biyayya ga na gaba, domin ni shaida ne a kan wannnan. Ya taɓa gaya min dalilin da ya hana shi fito da littafin tarihin sa, ya ce min saboda wasu manya da ya ke ganin girman su sun hana shi. Da na ce masa ai duk sun rasu, sai ya ce min in har bayan rasuwar su zan saɓa musu, to ban ga dalilin da zai sa in ƙi yi a gaban idon su ba. Ya ƙara da cewa ba tarbiyyar mu ba ce, ƙin biyayya ga maganar na gaba.

A nan na ɗauki wani sabon darasi na rayuwa. Wani abin sha’awa game da shi shi ne duk da nacin da na yi ta yi masa a kan littafin, bai taɓa nuna ɓacin rai a kan na dame shi ba, ko a waya ko gaba da gaba. Abin da dai ya ke gaya min, ba zai haura umarnin da manyan sa su ka ba shi ba. 

Alhaji Bashir mutum ne karimi, domin ko a yau ɗaya daga cikin abokan sa na kusa, Malam Bilya Bala, ya ba mu labarin daya daga cikin irin karimcin sa, inda ya ce mana ƙarshen ganin sa da shi watannin baya sun haɗu domin su haɗa kuɗi su taimaka wa wani abokin su. Sai Alhaji Bashir ya ce shi duk abin da aka tara, zai bayar da linkin biyu. Haka kuwa aka yi. 

Rayuwar Alhaji Bashir Tofa darasi ce ga matasa, su fahimci cewa ba tarin shekaru ba ne nasarar rayuwa, ilmin da biyayya ga na gaba da kuma son jama’a ita ce nasarar rayuwa

A lokacin da ya ɗauki situdiyo ɗin gidan sa gaba ɗaya ya bayar ga wasu mawaƙa, na tambaye shi cewa, ba ya ganin na za su yi amfani da shi yadda ya dace? Sai ya ce min, “Mu dai mun yi abin da ya dace a matsayin mu na iyaye, saura kuma ya rage nasu, su bai wa maraɗa kunya.”

Mutum ne mai zurfin tunani da fiƙirar magana. Zama na da shi na fahimci rayuwa, na yi karatun rayuwa ƙwarai a wurin sa. Mun tattauna a kan ilmin taurari, yadda ake rubutun zube, alaƙar sa da IBB, abin da ya haɗa su da Abacha, yadda rikicin nasu ya zamar masa alheri, har ya rubuta tarihin Musulunci, da makomar Arewa bayan mulkin Buhari, da yadda ya zama shugaban jam’iyyar NPN ya na yaro matashi, kai har da alaƙar sa da babban abokin sa, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi. 

A nan na lura da cewa bambancin aƙida ko fahimta bai sa ka ɓata da abokin ka. Domin a lokacin da su ka dawo daga karatu, a gidan sa Rimi ya zauna, amma sai ga Rimi ya na PRP shi kuma ya na NPN, kuma hakan bai taɓa shafar abokantakar su ba, duk kuwa da dagar da aka shaya a tsakanin jam’iyyun guda biyu. Ya kuma sha min nasihohi da su ka haska min hanya. 

Alhaji Bashir mutum ne mai barkwanci da haba-haba. Zai wuya ka same shi, ku yi hira ba ka fito cikin farin ciki ba. Duk saurin da ka ke in ku ka fara hira da shi, sai ka manta abin da ke gaban ka. 

Ya taɓa ba ni wani labari na yadda su ka sanya JS Tarka a jirgi daga Legas zuwa Kano; labari ne mai ban-dariya. Da yadda su ka fafata da Hassan Sarkin Dogarai a gaban Sarkin Kano Ado, har su ka sa sarki dariya a fada. Da wasu labarai masu ban-dariya da na ji a wurin sa, musamman haɗuwar su da wani attajiri mutumin Kano a Brussels.

Wani abu da ba na mantawa, kuma ya ke bani dariya a game da shi, shi ne yadda ya dage allankatafar ni abokin sa ne, ba ɗa ba. Abin ya faru ne, da na yi masa waya na nemi izinin zan zo in gaishe shi, sai ya gaya wa masu gadin gidan sa cewa wani abokin sa zai zo. Wannan ya sanya da na zo, masu gadin su ka ce su dai ya ce masu abokin sa zai zo, bai ce ni ba, amma in kira shi a waya. Da na kira shi, sai ya ce min ai ya gaya masu zan zo. Na ce masa, “Su dai sun ce abokin ka zai zo.”

Sai ga shi ya fito ya na masu faɗa ba ya ce masu abokin sa zai zo ba? Nan aka bar ni da baki a wangale, ina kallon ikon Allah. Tun daga lokacin mu ke wannan mahawara da shi, shi ya dage a kan ni abokin sa ne, na ke zuwa mu yi hira, ni kuma na dage ɗan sa ne na ke zuwa in ƙaru da ilmin da Allah ya ba shi. 

Magana ta ta ƙarshe da shi, kusan ‘yan satuttukan baya ne, da na kira in gaida shi, ya ke ce min, “Ba ka kawo yaran ka ba da ka ce su na so su zo su gaida ni.” Saboda na gaya masa mun wuce ta ƙofar gidan da su, su na tambayar gidan waye, na ce, “Zan kawo ku gaida shi, wani kakan ku ne.” 

Rayuwar Alhaji Bashir Tofa darasi ce ga matasa, su fahimci cewa ba tarin shekaru ba ne nasarar rayuwa, ilmin da biyayya ga na gaba da kuma son jama’a ita ce nasarar rayuwa. 

Mutum ne mai kishin addinin sa. Bai taɓa yarda da zalunci ba, dalilin da ya sa ya sha daga da shugabannin Nijeriya da dama.  

A gaskiya Kano, Nijeriya da mutanen Arewa mun yi rashin mutum mai kishin mu da son cigaban mu. Zai wuya a mayar da kamar sa. 

Allah ya jiƙan sa da gafara, ya yafe kurakuran sa, ya sa Aljanna makoma. 

Kaico! Ba rabo da gwani ba…!

Loading

Tags: Abubakar RimiArewaBashir Othman TofaBilya BalaFatuhu MustaphaHassan Sarkin DogaraiJS TarkaKanoNPNNRCrasuwaSDP
Previous Post

Yanzu ba ruwan mu da Hukumar Tace Finafinai, inji masu gidajen kallo na Kano

Next Post

‘Labari Na’: Tsakanin Aminu Saira, Nafisa, Nuhu Abdullahi da Kannywood

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Jarumai da ma'aikata a wajen ɗaukar shirin 'Labari Na'

'Labari Na': Tsakanin Aminu Saira, Nafisa, Nuhu Abdullahi da Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!